☁️☁️☁☁☁☁☁☁☁️☀
🐔 _*(HUDAH Y'AR KARYA....💁🏼)*_
🐤🐤🐤🐤🐤🐤🐤
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🐛_Written By *ASY KHALEEL...✍🏻*_
Wattpad@asykhaleel
Facebook Group
Asy khaleel Novel's grp
IG @asykhaleel5️⃣6️⃣
Wasa wasa soyayya mai karfi ta kullu a tsakanin Hudallah da Abdallah, sedai haryau bata yarda sunyi ido hudu da Sawad ba, duk da cewa a yanzu takan rasa wa tafi so cikin su, kuma wa yafi cancanta daya mallaketa?
Awannan lokacin zamu iya cewa hakurin Mamy ya gama karewa, sosai ta addabeta data tsaida tsayayye acikin masoyanta, wannan dalilin yasa Hudah ta shirya taje har gida ta iske kawarta Asy donta bata shawara, ita dai har yanzo takan rasa watafi kauna, kuma wa yafi kaunarta cikin mutane biyu?.
Bayan ta bayyanawa Asy dalilin zuwanta, Asy ta sauke ajiyar zuciya babu alamun wasa ta dubeta ta ce.
"Azahiri ko wannen su ba karamin so yake miki ba, ke yanzu wa kika fi so kuma kike ganin yafi dacewa dake? Harara Hudah ta watsa mata gami da cewa,
"Banson iskinci, ya zaki maido min tambayar danai miki bayan na sanar dake nakasa gane hakan ne, plz ki bani shawarar data dace dani dan Allah"
Murmushi Asy tayi tare da gyara zamanta sannan tafara da cewa.
Nidai a iya hasashena sai nake ganin kinfi dacewa da Sawa...
Kafin ta karasa fadin Sawad, a tsorace Hudah ta daga kai ta kalleta, Asy ta kada kai dama tasan haka zata kasance, tuni ta dade da gane Hudah tayi nisa acikin soyayyar Abdallah ko kadan bama za a kwatanta son datakewa Abdul da Sawad ba, itace dai takasa gane hakan, Asy ta daura da cewa,
"My Hudancy kenan ta Abdallah, abinda nakeso ki gane Sawad yanada hankali kuma ya dara Abdalllah shekaru ina tunanin zakifi jin dadin zama dashi fiye da Abdallah, kinsan wanda ya fika ya fika ne koda na awa daya ne,
Sannan in kika lura, Sawad yafi Abdallah kishinki hakan na nufin ya fishi sonki amma sanin dai-dai sai Allah, kuma ko ba komai kun Dade da Sawad kinga bai dace ki masa haka, nasan kina duba yanayin sakin hannunsa, ba kamar Abdallah ba, har yanzu baki gane wasu abubuwa da dama gameda..
Maza iri iri ne akwai wanda zai dinga 6arin kudi wajan neman aure, babban burinsa yaga ya kaiki gidansa ko nawa ya kashe wajan aurenki bazai damu ba, sedai me?
Dazarar kin shiga gidansa shikenan, nanne zaki ga sabon hali wani ma. sisin shi bazai yarda ki karu dashi ba, ke wani hatta abincin da zaki dafa saiya auna miki irinsu ga jarabar siya duk inda yaje ya dawo ya rufan miki ba kuma yanda kika iya dashi, shiyasa sai kiga yarinya shar shar gwanin bansha'awa a gidansu da zaran anyi aure sai nan da nan ta fita hayyacinta arinka cewa dama can kwadayi yaja miki.
Wani kuma haka Allah yayisa mai hannun ungo ne duk abinda yake miki agidanku idan kikaje gidansa sedai ya ninninka, ba yanda ba a samu.
So wasu dayawa samari basa sakinma yarinya kudi ne badan komai ba, sedan su gwada irin soyayyar da take masu shin soyayyar ta kudi ce ko ta tsakani da Allah, kaman yanda na lura wannan jarabawan Sawad ya ke miki, sanin kanki ne ba kudin daze kashe miki ne bashi dashi ba, in kika lura shidai ya kawo zallan kudin ne yabaki beyarda da hakan ba, amma kome kikace kina so jiki na 6ari zai kawo miki, so cikin maza akwai masu irin haka koda anyi aure wasu basu yarda su bama matansu kudi ba wai dan karta saba, sunfiso tace tana son abu kaza saisu kawo mata. So Babban kuskure ne ga samarin yanzu, suki kyautatawa budurwa wai suna gwada soyayyar da take masu. Mafi dacewa inhar kaga yarinya kana so kuma kanada abinda zaka kyautata mata to ka kyautata mata ko a wajan Allah yin hakan ba laifi bane ba kuma almubazzaranci ba, don babu abinda ba a nema da kudi anan duniyar, wani bangawan aljanna ana nemanta da kudi tahanyar sadaqa da kyautatawa, hakama aure dole ka zamo mai yawan alheri ga yarinyar da kake so, kayi la'akari da nema kake baka riga ka samu ba, in katsaya wasa kana gani wani zaizo ya ture gwamnatinka kamar yanda Abdallah yayi ma abokina juyin mulki. Asy ta saki siririyar dariya, ganin mugum kallon da Huda ta watsa mata,
"Ai gaskia nafada, duk mai hankali yasan kinyi nisa cikin soyayyar Abdallah, kuma banga laifinki ba, agaskia gayan yasan kan luv ga bajinta da kudi, don ko muma mun yagi rabonmu, sedai haryanzu ya kamata kigane Sawad shi ya fito ya nuna karara aurenki zeyi kuma shiyake matsawa da mgnr aure, shifa Abdul?
Karki manta student ne har yanzu karatu yake kina ganin iyayensa zasu goya masa baya yayi aure?"yes tin last month yake min maganar zai turo iyayen shi ni nace ya bani lkc"
Asy tadanyi shiru nadan lkc daga karshe ta bata shawarar ta bashi dama kawai ya turo, sosai ta gane shine kadai a ranta dan haka bazata cika zakewa akan Sawad ba,
Haka dai suka kare shawarwari sedai har lkcn Hudah ta kasa tsaida daya iyanzu ta gama sakankancewa Abdallah shine aranta dan har wani fadiwan gaba takeji idan Asy tace ta zabi Sawad...
*KING ASY KHALEEL...* ✨
YOU ARE READING
*HUDAH 'YAR KARYA....*
Romance*HUDA YAR KARYA* _Labarine akan wata yarinya mai suna huda wadda ta dauki karyan dunia ta daurawa kanta alhalin ita ba yar kowa ba_. _Matashiyar yarinya ce mai tsabagen San karya da San gayu da shiga ta alfarma dansan abun dunia, Wanda kallo daya za...