☁️☁️☁☁☁☁☁☁☁️☀
🐔 _*(HUDAH Y'AR KARYA....💁🏼)*_
🐤🐤🐤🐤🐤🐤🐤
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🐛_Written By *ASY KHALEEL...✍🏻*_
Wattpad@asykhaleel
Facebook Group
Asy khaleel Novel's grp
IG @asykhaleel
1️⃣1️⃣-2️⃣0️⃣
Tin bayan rasuwan M Yunus gaba daya al'amura suka sake cudewa su Mamy da yaranta, ada gani take duk ya barta da dawainiya wannan dalilin yasa bashi da damar yasata ko ya hana ta, magana kadan zeyi ta haushi da fada tamkar itace mijin badan komai ba,
Sai dan ganin d'an sana'ar da take suna haduwa su rufawa juna asiri, sai bayan ta rasa shi a sannan ne ta fahimci lallai ba karamin kokari Baba yake ba, ta gane cewa lallai rike gida sai namiji, amma dan rashin gdy irin namu na mata wani lokacin har namiji yafita yasan yanda yayi yakawo mana, a memakon musa hannu biyu mu kar6a muyi godiya ga Allah, sai mu raina watama sababi zata kama ita don bata sami yanda take so ba,Anan nake jan hankalin yan uwana mata da murinqa godiya da abinda Allah ya horewa mazajan mu, Allah ma yana cewa,
لإن شكرتم لآ زيدنكم
Ma'ana idan kuka gode sai Allah ya dad'a muku, Allah ka wadata mana zukatan mu ameen.
Haka dai rayuwan Mamy da 'ya'yanta yacigaba da wakana basu da wani matemaki sai Allah, dangin M.Yunus da sukazo ta'aziya daga kauyen Zamfara, sunso su dauke mata nauyin wasu ya'yan, Mamy ta nuna Sam bazata bada yaranta akai mata kauye a zube su a gona ba maganar karatun su kuma ko oho, sunyi iya kokari akan tabasu koda mutum biyune, Mamy takafe akan Sam bazai yuwu ba, dan haka suka barta da yaranta, tin lokacin ba wanda yasake waiwayar su daga 6angaran dangin miji,
Awahalce Mamy tayi kwanaki arba'in dinnan na takaba, kasancewar batada daman yin sana'a sai wanda yaga Allah ya temaka masu, aifa tana fitowa ta fara kasuwanci ba kama hannun yaro, kama daga kansu omo, sabulu, kayan miya, kayan lashe lashe na yara kala kala duk saidawa take, yaro da babba a unguwan kowa yasan gidanta, har suna aka radama gidan waishi gidan (qwalama) tayi hakan ne domin su tsira da mutumcin su don Mamy mace ne wanda Sam bata jurewa quncin rayuwa, da wannan kasuwancin sukeci suyi sauran buqatu hatta karatun ya'yanta babu abinda ya canja, abangaran Hudallahi fa??
Yanzu takai kimanin shekaru ukku a wajan koyon dinki, sosai take da fahimta har mamakin ta mentor dinsu take wanda suke kira aunty Munirah, Hudah tafi yawancin wa'inda suka rigata zuwa wajan fasaha don,
Babu kalar dinkin zamani wanda yake gagarar ta dinkawa, sedai dan gyara kadan da ake mata awajan yanka, hakan yasa tashiga ran munirah sosai don tana temaka mata ba kadan ba, shiyasa itama take dan yi mata ihisani in sunyi aiki tana sammata dan na kashewa, dakyar da gumin goshi Mamy tasamu Hudah ta zana junior waec, tin daga nan Hudah ta yakicar da makaranta mamy tayi juyin duniya akan ta daure takare secondary ta amshi certificate dinta, sam Hudah ta sharawa idonta toka tai watsi da maganar Mamy don ita ranta yafison dinkin nan burinta tadan kara gane wasu abubuwan aiyi mata freedom itama ta faracin gashin kanta, Mamy tana gani dole tasa ido don Hudah kafiyane da ita, sanin cewa koda ta matsa mata akan setayi tofa kudinta zata 6ata abanza, tasan halin Hudah tinda tace batayi tofa baza tayi abinda akeso ba dole kasa mata na mujiya👀*_Wannan kenan._*
*WACECE HUDALLAH*??
Saiku kasance tareda *KING ASY KHALEEL* danjin cikakken tarihin..
*HUDAH YAR KARYAH* 💁🏼
ESTÁS LEYENDO
*HUDAH 'YAR KARYA....*
Romance*HUDA YAR KARYA* _Labarine akan wata yarinya mai suna huda wadda ta dauki karyan dunia ta daurawa kanta alhalin ita ba yar kowa ba_. _Matashiyar yarinya ce mai tsabagen San karya da San gayu da shiga ta alfarma dansan abun dunia, Wanda kallo daya za...