☁️☁️☁☁☁☁☁☁☁️☀
🐔 _*(HUDAH Y'AR KARYA....💁🏼)*_
🐤🐤🐤🐤🐤🐤🐤
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🐛
_Written By *ASY KHALEEL...✍🏻*_
Wattpad@asykhaleel
Facebook Group
Asy khaleel Novel's grp
IG @asykhaleel
5️⃣8️⃣
Abdullahi A. Ameen, cikakken sunan sa kenan, mahaifinsa Alhj ameen Babban sojan sama ne (Air vice marshal)
Alhj Ameen dan asalin jihar barno state ne aiki ya kawo shi garin Kaduna, gidansa babban gidane anan unguwan sarki Kaduna, matarsa daya Hjy Hauwa, sai yaransu guda ukku, Jamila Abdallah sai autarsu Husna.
Alhj Ameen mutum ne mai tsatstsauran ra'ayi duk abunda yasa agabansa tofa shine mekyau babu mai iya ja dashi a gidansa hatta matarsa shakkarsa take,
Tinda suka fara haihuwa ya qudirci ya'ya'n sa saisun zama ani abu a kasar Nigeria, hakan yasa Jamila tana kare primary school ya harba ta Malaysia karatu, a iya tunanin sa gani yake duk babu wasu makarantun da suke kulawa da karatun yara cikin gida Nigeria, (nidai Asykhaleel nace kudi dai in sunyi yawa dole anema hanyar da za a walakanta su tinda ba Allah bane arai duniya ita akasa a gaba Allah kasa mu gyara)
Haka Jamila ta cigaba da rayuwa a can wurge wata kasar da babu dangin iya bare na baba, kunga maganar mai kwa6awa bata taso ba, damma dai shiriya tana a hannun Allah. Jamila abinda yakaita shi tasa agabanta.
Haka Abdallah shima daga primary akai waje dashi don kuwa burin Babansa akansa yafi na kowa, Mominsu tayi kuka ba adadi, sedai ko kallo bata isa A. Ameen ba, hasali ma kallon sakarya kawai yake mata.
An samu rashin sa'a awajan Abdallah domin tinda ya tsinci kansa hurge a inda babu mai cewa yi bare kuma ka bari, ga kuma kudi wanda Dad ke yawan tunkuda masa waidan yayi abunda ake so , a can ya hadu da yara majiya dadi irinsa, sukaita shimfida rayuwa kalar wanda tai musu dadi, tin babu yanda suke sunsan dadin mata, yarinya komin yanda take ji da kanta, da kuma kyawun surarta sai sunsan yanda suka ja ra'ayinta, burinsu daya su dandani zumarta. (Ya Allah ka shirya mana zuri'a)
Ahaka Husna ta taso itama aka cillata America a lkcn Momin su ta tada qayar baya akan bata yarda ba, sedai a barmata Autar ta a gabanta, marshal Ameen ya ce ita dinme?
har akwai macen data isa ta canja masa ra'ayi, afafau itama ta nuna bai isaba, fadi take
"Wannan rashin emani dami yai kama duk ka raba min ya'ya akan wani burinka, sannan ko baka duba wannan ba, ai ka duba yanayin Husnah yarinyar da agabanmu sai ciwo yayi kamar zekasheta, amma badai ta fadi ba, se in nine na matsa mata muje asibiti, to acan wazeyi mata wannan?
To gaskiya banyarda ba, sosai ta dage akan sedai ya saketa, haka kuwa akayi take ya nuna mata yafita karfi akansu, ya bata saki daya, don ya baqanta mata washe gari jingin su Husna ya daga zuwa kasar Amurka.
Daga baya iyaye suka shiga lamarin sukayi gyara har aka maida auren nasu, wani abun mamaki kowa ya bude baki ita akeba rashin gaskia dole ta fauwalawa Allah komai, sedai tanabin yaranta da adduar shiriya dan ita ta hangi abinda ta hanga. Haka dai rayuwansu ya kasance, Jamila bata dawo gida da sunan zama ba sai data zama cikakkiyar barrister, lkcn tana da 32years da haihuwa.
A can Delhi Abdallah yayi nisa sosai cikin karatun likita, yayinda Husna take 200level a university, kwatsam wata rana suna cikin class ta fara murqususu ciwan ciki ya kamata sosai, haka aka nufi asibitin makaranta da ita nan da nan likitoci .suka rufa akanta, take suka gano appendix ne kuma harya fashe mata aciki.
Cikin matsanancin tashin hankali shuwagabannin makarantan suka sanar da Alhj Ameen halin da ake ciki, domin Babban likitan ya baiyana cewa za a iya mata aiki emergency sedai ya zama done iyayenta su saka hannu dan aikin yanada mugun hadari, ba kowa akema irinsa asami rayuwansa ba, gabaki daya kayan cikinta za a fitar sa'annan awanke su akuma mayar a dinke.
Karkuso kuga tashin hankali wajan marshal Ameen, sosai ya dimauce dole ya umurcesu da suyi gaggawan saka hannu aceto masa ran diyarsa.
Lkcn da abin yafasu yana Lagos ne, ba 6ata lkc ya umurci matarsa datazo ta iskeshi a yau dinnan, sedai besanar da ita meke faruwa ba, tuni ya gama shirin tafiyar su America jinginsu zai tashi da asubahi.
Hajiya Hauwa bata kawo komai ba, tayi zaton kamar yanda yasaba ne idan baya kusa da ita yakan gaza hakuri har yayi mata irin wannan emergency calling din.
Acan America doctors sunyi duk abinda ya dace akan Husna yanzu sai sauraron ikon rabba,
Lkcn da suka isa america, tsayawa misulta tashin hankali wajan iyayen Husna musamman mahaifiyarta, wanan bata lkc ne,
Tashin hankalinsu ya karuwane lkcn da likitoci da dama ke yawan zarya akanta suna aune aune gashi kusan kwananta ukku dayin aikin babu alamun rai atare da ita, daga karshe suka dena 6oye 6oye suka sanar da Ameen, sedai yayi Hakuri yar'sa Allah yai mata sa'i A Ameen yayi kuka ba iyaka, amma gudun tashin hankalin Matarsa yasa yaki bayyana mata rasuwan yar tasu, lallashinta yayi da cewa sunyi turasu zuwa kasar India acan zasuga doctor, insha Allah za a dace, ya kuma tabbata mata Husna tana nan daranta,
Wani murmushin dayafi kuka ciwo Momi tayi, kallonsa kawai take tin safiyar ranan ta fashimci babu Husna tadai barsu sugama boye boyen su fito su fada,
Acan gida kowa yayi mamakin
Momy data iya daurewa dan har suka dawo gida babu ko digon hawaye a fuskarta sedai addua da take aikin yi mata a bayyane, agabanta aka shirya Husna ta kafesu da ido anyi juyin dunaya akan ta fita tace itafa ta dangana su gyarata kawai akaita makwancinta
Lkcn da aka dauketa za a fice nanne ta mike tana fadin,
"Shikenan Husna ta kin tafi kin barni ba zaki dawo ba? Wani irin kuka ya kubuce mata sai kuma sukaji dif ta sulale zata dadi akai saurin tarbota..
Kwanan Momi ukku kafin ta farfado da sunan Husna ta tashi, sai kuma ta koma fadin
"Kaika cuceni karabani da yata. Dad dake gefanta da gudu yazo ya rungumeta yana kuka wiwi kamar karamin yaro, yayinda zuciyarsa ke cike da nadaman tura Husna America bada sanran mahaifiyar ta ba,
Wannan dalilin yasa Dad ya dawo da Abdallah gida acewarsa inma karatunne yayi a gabansu, ko mutuwarce gara tazo masa yana cikin danginsa musulmai, bayan arba'in din Husna, Dad yasa ranar auren Jamila, sa6anin da dayake ta hanya hanya, dan ya rainawa mijin data kawo tace shiyai mata, yana danin becanci abasa ita ba, sbd beci ya Tara ba, taya zai bashi yarsa daya sha wuya wajan karatunta, wata daya jal yasaka ranar auren, yanzu haka watanta bakwai kenan da aure harma tana dauke da cikinta na wata hudu.
Dafarko mutuwar kanwansa Husna ya furgitashi duk wani shashanci ya dena, sedai dake ita zina abuce mai wuyar bari kuma wanda ya saba da mace mawuyacin hali yake shiga idan ya rasa ta, da ace iyayensa sunyi tunanin yi masa aure kila da baze komawa mummunar bagiransa ba, sai kuma basuyi hakan ba,
Bayan wasu yan watanni Abdallah yaci gaba da cin duniyarsa da tsinke Momi na lura da hakan ta fara bude masa wuta akan gara yayi aure da wannan shashancin, nan itama dad ya rufammata da fada ya kuma jaddada masu itada danta aurensa ba yanzu ba, harsai ya kammala karatu ya fara aiki, lkcn ne ya cancanci aje iyali..
Wannan shine takaitaccen tarihin Abdallah bari mu koma gidan aunty Jamila.
*KING ASY KHALEEL....* ✨
ESTÁS LEYENDO
*HUDAH 'YAR KARYA....*
Romance*HUDA YAR KARYA* _Labarine akan wata yarinya mai suna huda wadda ta dauki karyan dunia ta daurawa kanta alhalin ita ba yar kowa ba_. _Matashiyar yarinya ce mai tsabagen San karya da San gayu da shiga ta alfarma dansan abun dunia, Wanda kallo daya za...
