☁️☁️☁️☁️☁️☁️☁️☁️☁️☀️🐔*_(HUDAH Y'AR KARYA...💁🏻♀️)_*
🐤🐤🐤🐤🐤🐤🐤
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🐛_Written By *ASY KHALEEL...✍🏻_*
*_Wattpad@asykhaleel_*
*_IG@asykhaleel_*6️⃣0️⃣
Feedoh tayi matukar farin ciki dajin an saka ranar auren aminiyarta, dayake duk abin dake wakana Hudah tana sanar da ita, hakama Mamy dan har yanzu suna mutumcin sosai da Momi babu abin daya canja,
Itama Feedoh anyi baikonta da fa'eed yaran qanwar Dad dintane iyayensu suka hada, anyi sa'a kuma suna san juna, wata shidda aka tsaida lkc, in anyi bikin Hudah da wata biyu za'ayi nata,
Tinda aka saka rana, Abdallah ya fara 6ollowa Hudah da wasu tsurfa, a duk lokacin da suke tare kokarin sa ya ta6a jikinta, inhar suna hira a motarsa hannun shi yana sakale da nata yana wasa da yan yatsunta ahaka ake hirar, tayi mitar yabari yaki denawa harta gaji,
Abin nasa yayi kamari ne lkcn da akaci wata daya da saka rana, bikinsu ya rage saura wata uku,
Yanzu yakai ga har kissing dinta yake, yauma kamar yanda suka saba, fira suke a cikin mota hannunsa daya saman kafadarta dayan hannun yana wasa da karan hancinta, cikin mafi raunin murya yake bayyana mata matsalar shi,
Batayi zato ba saijin hannunsa tayi cikin ragarta yafara wasa da kirjinta.Saurin janye jikinta tayi takai hannu zata bude murfin motar da nufin ta gudu, dasauri ya riko hannun ta yana fadin.
"Sorry my sweetheart hug me please". Afusace ta furta,
"Bazan iyaba gaskia.. Kafin takarasa ya daura mata sassanyar kiss a le6e. Tin tana iya kokarinta wajan hanashi har sai daya kashe mata jiki da salonsa dole ta sakar masa ragamar jininta yaita yamutsa ta sanransa. Daga ita harshi sunyi nisa don kiris ya rage ta fara mayar masa da martani, taji ya saki yar kara wanda har saida ta tsorata. Awahalce ya fara fadin."My Hudah kiji tausayina ki temakeni karna mutu.. Tureshi tayi jikinta ya fara kyarma "wani irin temako kakeso in maka Abdallah?
Mekake nufi ne, in baka kaina kakeso awalakance?
Anya Abdallah kanemin san gaskia?.Ido ya zuba mata dan ya kasa magana, babban bukatarsa a lokacin yaji ya shiga Hudah,
Dakyar ya samu damar bude baki yana fadin.."Kiji tausayina wannan ba wani abun damuwa bane ni mijin kine, nafa biya sadaqin ki shedarwa kawai ya rage, wlh ina cikin matsanancin hali ki temaka min na iya yau kadai bazan jure ba please..
_To gareku masu bibiya, Anya kunaso mu gama book din nan da wuri? Dan banga alama kuna sakin zafafan comments da vote ba, domin vote da comments dinku shi zeban kwarin gwiyar Kullun na maku dan farin ciki😊
YOU ARE READING
*HUDAH 'YAR KARYA....*
Romance*HUDA YAR KARYA* _Labarine akan wata yarinya mai suna huda wadda ta dauki karyan dunia ta daurawa kanta alhalin ita ba yar kowa ba_. _Matashiyar yarinya ce mai tsabagen San karya da San gayu da shiga ta alfarma dansan abun dunia, Wanda kallo daya za...