HUDAH Y'AR KARYA...68

774 74 18
                                        

☁️☁️☁️☁️☁️☁️☁️☁️☁️☀️🐔
_*(HUDAH Y'AR KARYA..💁🏻‍♀️)_*

     🐤🐤🐤🐤🐤🐤🐤
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🐛

_Written By *ASY KHALEEL..✍🏻_*
     _*Wattpad@asykhaleel _*
        *_IG@asykhaleel_*

                  6️⃣8️⃣


Abinka da 'ya da mahaifi kwanan Asy daya a tsare Dad dinta yaje aka bashi belinta bayan ya saka hannu akan sharadin zai tsaya har a biya su kudinsu.

   Yau kimanin kwana hudu kenan da tafiya da Hudah, har lkcn tanacan a rufe, soboda rashin gata kasancewan ita bata da wani wanda za aga kimansa, duk da cewa kullum sai Mamy taje masu da kuka tana rokon su akan su bata belin Hudah sai a diba mata lkcn da zasu kawo kudin,
Korar kare sukaiwa Mamy sukace Sam ba maganar beli saisun biya rabin kudi kafin a futo da ita,

  Mamy ta rasa yanda zata saka kanta gashi basu da wani matemaki sai Allah,

Daman Abdallah ne to yanzu baya kasar gashi ba a ko samunsa awaya,

Dole tasa tafara saida kayan data siyama Hudah na aure duk da tasan ko kwatan kudin ba zasu yi ba, wani abun takaici duk abunda ta d'aga ko rabin kudinsa ba a taya mata amma haka take bugar dasu saboda tsananin tashin hankali.

  Akwana biyu in kaje gidan Mamy kuka kawai zaka kama yi ita kanta ta fita hayyacinta duk ta kadar da duk wani abun mai amfani na gidan, hatta gadajan dake dakunan su ta kwa6e su ta siyar sannan ta samu ta hada dubu dari biyu da hamsin, ta adana su da nufin gobe tin safe zata kai a bata 'yarta,
Allah sarki *UWA UWA CE*

Abangaran Abdallah yana India amma ya baza masu kawo masa rahotanni duk abunda ake ciki suna sanar dashi, sosai ya tausaya ma Hudah, aransa yace,

"Dole dana dira in tsaya a fito da ita dan bata canci haka ba a gareni"

Sedai wani 6angaran har wani murmushi yake kufce masa in ya tuna wannan dalilin yayi masa sanadi, yanzu kam ya samu kafar gudu  cikin sauki.

Ranan data cika kwana shida aranan  ya dira gida Nigeria ko gida bai isa ba saida ya san yanda yayi ya samo dubu dari biyu da hamsin,  ya aika Naseer ya kaima Mamy,

Nan suka gama tsara komai na yanda zasu 6olloma lamarin.

    Da daddare Mamy harta rufe gida Naseer ya sallama tayo lilli6i ta fito tana tambayar waye?

"Nine  Naseer abokin Abdallah"
 
   Mamy najin haka ta bude ta bashi damar ya shigo daga ciki.

  Bayan sun gaisa ya jajanta mata akan abun daya faru da Hudah daga karshe ya kawo kudin nan yace gashi inji Abdallah yace dan Allah asan yanda akayi aka fito da ita gobe kar a barta ta kara kwana, sedai fa Mamy wlh an samu matsala sosai,  ya kara kasa da murya alamar damuwa,

Mamy kam haka kirjinta yake bugawa farfar tama kasa furta komai, Huzaifah dake zaune a gefe shine yai karfin halin cewa maiya faru kuma?

Naseer ya sake sadda kai yana girgiza kai alamar abun mai girma ne, sannan ya fara da cewa.

"Saukan Abdallah kasar nan kenan ya tadda labari mara dadi awajan iyayensa, atakaice dai yana dira ko barinsa ya huta basuyi ba, suka haushi da bala'i wai dama ba yarinyar kirki ya nemo zai aura ba, to wlh sun suke maganar aure kuma ko ta kofar gidan nan yasake bi Allah ya isa basu yafe masa ba, yarinya tin tana agida ta iya jawo fitina inaga tashigo gidansa a kawo masu mugun iri, kai maganganu marasa dadi sukaita ya6a masa, ba shiri sai gashi yazo min da kukansa karkuso kuga yanda ya shiga tashin hankali. Yanzu dai yace na kawo miki kudin nan asamu a fito da ita,  zai cigaba da lallashin su in Allah yasa sun hakura sai a sasanta daganan a gyara maganar biki, in kuma sunki amincewa tofa sedai ayi hakuri domin baban nan nashi ko kadan beda mutunci, shi dai yace in fada miki duk abunda yaima Hudah wlh ya yafe kuma har gobe yana kaunarta sedai in Allah benufa matarsa bace.

   Mamy ta sauke numfashi tana juya kai ta dube shi tace,

"Yanzu har lbr yaje ga iyayen yaran nan kai duniya ina zaki damu"
Naseer ya gyara zama yana fadin
  Ai Mamy bama  iyayen shi kadai ba kinkoji maganar nan agari yanda aketa yawo dasu, wasu na fadin kamfani sukaima sata kowa da yanda zaiji lbrn karya da gaskiya, ai mutane ba a iya masu,

"Toh ai shikenan su suka jefa kansu dolene duniya tayi dasu, bakamar ita Hudah, wancan tinda ita tana da gatanta kaga ai ita kwana daya tayi ubanta ya fito da ita,
Mamy na kaiwa nan ta fashe da kuka maiban tausayi, har Naseer yabar gidan aikin kuka Mamy take, Huzaifah keta aikin lallashi duk da shima kukan yakeyi,  babban tashin hankalin Mamy lalacewan maganar auren Hudah wannan abu shi yafi komai mata ciwo nan da nan zazza6i mai zafi ya rufeta haka ta kwana juyi a daran dai  bacci ya kaura a idonta..

Kuyi hkr dani...zaku samu cigaba Insha allah,Votes n Comments shine burina 😁

*HUDAH 'YAR KARYA....*Stories to obsess over. Discover now