*HUDAH Y'AR KARYA*..54

1.2K 122 5
                                    

☁️☁️☁☁☁☁☁☁☁️☀
🐔 _*(HUDAH Y'AR KARYA....💁🏼)*_
         🐤🐤🐤🐤🐤🐤🐤
  🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🐛

_Written By *ASY KHALEEL...✍🏻*_

         Wattpad@asykhaleel
           Facebook Group
        Asy khaleel Novel's grp
             IG @asykhaleel

                       5️⃣4️⃣

Kafin cikar 5mins hall din ya zama kamar anyi shara kowa ya kama gabansa. Asy da Hudah sai rakiyan friends sukeyi suna basu hakuri, wa'inda sukasan abin da ya faru sai jajantawa juna ake, wasu kuma sunama cute adduar samun lfy,

     Tin shigowansa hall din idonsa ya sauka akanta duk shige da ficen da sukeyi idansa a kanta yake, ya kasa ya tsare sosai ya qosa yaga tadan samu nutsuwa domin ya samu damar isar da kansa gareta, sedai ya lura kamar akwai 'yar wata  damuwa a tare dasu ganin yanda suka kasa zama,  cikin lokaci kalilan ya kamu da santa har mamakin kansa yake yanda ya fada tarkonta gani daya domin
A iya tarihin rayuwansa itace mace ta farko wacce farat daya ganin surar jikinta ya dimauta shi.

  Zaune yake a cikin mota ya kwantar da kansa jikin seat zuciyarsa na cike da begen yarinyar daya gani,

  Kamar ance ya daga kai, ya hangosu suna fitowa, nan take ya wakinta abokinsa dayaje yafara masa iso a wajanta,

Yayi hakan badan komai ba, saidan  yanaso yaga ya take kar6an bakinta domin yasan ta yanda zai shigar nata.

  Fitowa Fahat yayi daga cikin motar da nufin isar da sakon amininsa, ganin sunyi bakin get da kawayan su hakan ya bashi damar zama saman mota yana jiran juyowan su,  yana nan zaune yana dan latsa wayarsa sai gasu sun dawo.

   Dirowa yayi daga  saman motar, sannu a hankali yake takawa harya isa inda suka dan kebe suna tattaunawa ita da Asy,

   Sallama yayi masu cike da qwarewa, Asy kadai ta iya amsa mai  itama haka ta amsa kamar da fada, bata tsaya kallon koshi waye ba, sbd ba shike gabansu ba a yanzu,

  Abangaran Hudah dogon tsaki taja tare da janyo hannun Asy  sukabi hanyar shiga cikin Hall,

atakaice dai nan suka barshi a tsaye babu wacce ta daga kai ta kalleshi bare tasan da wanzuwansa a gurin.

     Le6ensa ya dan ciza  yana murmushi wanda shi kadai yasan manufansa, sa'annan yakoma  inda motar su.

Abdallah dake kishim gide jikin seat yana kallon duk abin da suka yiwa abokinsa kuma dan aikensa, ransa ya sosu matuka, sedai murmushine kwance bisa kyakkyawar fuskarshi ma'abociyar qwarjini, hakan da Hudah tayi ya karawa Abdallah wani haske don, kafin Fahat ya dawo harya gama tsara tayanda zai 6ulloma yarinyar,  bude murfin motar Fahar yayi ya shiga zaiyi magana kenan Abdallah ya tari numfashinsa da cewa.

  "Nooo karkace wani abu abokina, barta lokacin tane yanzu akwai ranan ramuwa tananan zuwa, yanzu bari su fito zan gwada sa'ata da kaina mugani"

Fahat ya saki murmushi tare da cewa ,
  "Kuma da alama sabon hannu ce  sedai da ganin yanayin ta zakaci qwaqwa kafin kasha zuma"

  Atare suka yi daria, Abdallah ya kada kai yace ba wani kwakwa da zanci, wacece ita wa'inda suka fita class sunbiyu cikin ruwan sanyi.
   Sunanan zaune a mota suka hango su Hudah sun fito da alama shirin tafiya gida sukayi dan ko wacce da jakarta a hannu.

Abdallah na ganin haka ya fito yana gyara zamar rigansa yabi bayansu,
Ta gefensu sukaji an ambaci.
    "hey" 
Lokacin sungama saka kaya a mota, Asy harta shige mazaunin driver, Hudah tana kokarin shigar da kafarta yace.

  please listen 2 me mana haba babbar yarinya wannan ba girmanki bane".. Dogon tsakin da taja ya sashi yin shuru, zata shige motar yai saurin riko hannunta, ai kuwa a hassale ta waiwayo da niyar wanke shi da mari, sedai sunayin 4eyes dashi taji wani yarrrr ilahirin jijiyoyin  jikinta sai da suka amsa, ba shiri ta sauke idonta kasa dan bazata jure kallon shi ido cikin ido ba, murmushi Abdallah yyi dama burinsa kenan suyi ido 4 yasan dole hakanne zata kasance, cikin salo yake jifanta da wani irin murmushi sa'annan ya ce,

   "Number naki  nakeso in bazaki damu ba!.
Kasa cemasa komai tayi, ta saka kafarta daya a cikin motar ganin har Asy ta tada motar, hunnu yakai ya zare wayar datake rike da ita, ya saka num dinsa take yakira no din. Wayar dake hannunsa ta shiga ruri, a nan dai yasamu damar aje lambarta shima yayi mata saving nashi da suna irinta masoya, sai da ya daura lips dinsa a saman hotonta dake fusar wayar alamar kiss sannan ya manna mata wayar a nata lips din, ya daga mata hannu yana murmushin sa mai bayyana kyawunsa.

   "Hmmm kaga wani wahalalle todai qwalelenka anyi maka fintinkau, inama  Sawad yana kusa tabb  da munga bala'in kishi"

Asy ce tai maganar  tare da karkata kan motar suka fice. Hudah batace da ita komai ba sema limshe ido datayi kamar mai bacci.
 

A6angaran Abdallah ba tare da 6ata lkc ba, ya wakilta wasu samari da su bisu a baya ba tare da sun sani ba, domin su binciko masa gidansu Hudah....

_Comments dinku da Votes su kadai zasu karfafamun gwiwa dan ganin kun samu nxt chappy batare da bata lkc ba_
*KING ASY KHALEEL..*✨

*HUDAH 'YAR KARYA....*Where stories live. Discover now