☁️☁️☁️☁️☁️☁️☁️☁️☁️☀️🐔
_*(HUDAH Y'AR KARYA..💁🏻♀️)_*🐤🐤🐤🐤🐤🐤🐤
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🐛_Written By *ASY KHALEEL..✍🏻_*
_*Wattpad@asykhaleel _*
*_IG@asykhaleel_*6️⃣9️⃣
Asuban fari Mamy tayi shirin fita bayan ta hada kudinta naira na gugan naira dubu dari biyar ta tafi gidan su Asy dan ta iske megidan.
Tsoro take ji karta nufi mutanan da kudin suzo su cuceta tinda ba imani ne dasu ba, ga kuma zazza6in da take fama dashi dakar ta isa bakin titi.
Tajima kafin ta samu abin hawa haka tayi tsaye gefan titi tana jiran a dai-daita, sai makyarkyatan sanyi take yi,
Sosai Dad din Asy ya tausaya ma wannan baiwar Allah ganin yanda take jin jiki amma haka ta doko sammako, ya kuma yaba da kokarin ta na hado kudi masu yawa haka akwanaki kalilan,
"Kai gaskiya tashin hankali babu dadi Allah ka shirya mana zuri'a"
Abin daya fada a ransa, sa'annan ya maida dubansa ga Mamy yana cewa.
"Yanzu kije gida insha Allah zantafi yanzu in kar6o miki 'yarki kuma zanyi iya kokari akan mgnr dan ganin an gama komai ayau nima zan kara wani abu akan kudin nan mudai samu a kashe case din a yau.
Haka kuma ya faru Dadin Asy bai saka ko sisin kwabonsa ba, a iya kudin Mamy yaje masu dasu nan sukaita mazurai yace.
"Ku wasu irin mutane ne da za kuce bakusan kaddara ba, ai duk wani dan kasuwa dolene daman wata rana yayi asara"
Aifa dole suka safko ,kasancewar shima yanada yar matsayin sa a gwamnati, bayan sun dai-daita daganan suka dinguma akayi gurin hukuma nandai suka kashe maganar aka bashi Hudah ya kaita har gida gaban Mamy.
*** *** ***
kuka take kamar ranta zai fita Momi ce tazo zata shiga kicin, nan ta iske ta kwance saman carpet bata ko matsa daga inda suka barta ba, har lkcn kuka take kamar karamar yarinya murya harya dishe mata.
"Dadai kin rungumi qaddarar ubangiji zaifi zama khairan agareki"
Momy ta fada lkcn da tabi ta gefanta zata wuce,
Dasauri Asy ta yunkura tai saurin rike kafafun Mominta tana fadin."Dan Allah Momi kiyi wani abu akan maganan nan wlh kasheni Dadi yakeson yayi inhar ya hada ni da wannan bagidajan,
Momy yanzu ke kin amince a daukeni akai wannan surquqin dajin?
Saida kuka saba min yaruwa tare daku na taso cikin gatana sannan zaku yar dani takan nai muku laifi,
Dan Allah Momi ki tausaya min, ku ceci rayuwata Ku hukunta ni ta wata hanyar ba wannan ba, wlh ko garin nan mukaje ziyara bana kaunar hada ido da wannan gaulan,
Mutum wani chakarere dashi baki baya ko rufuwa, amma a rasa wanda za a aura min sai shi!"Tana kaiwa nan tasake fashewa da kuka.
"To sakar min qafa natafi tinda kin kai aya, kuma kome zaki fada Tasu'u dai dan uwanki ne na jini, kuma baki isa ki canja maganar Dadin ki ba, sannan surquqin daji da kike magana nan ubanki ya fito dan haka kar in sake jin wannan maganan a bakin ki kinsan dai baban ku baya magana biyu, bare kuma da kunnin ki kika ji har sau uku yana rantse miki akan sati biyu masu zuwa za a daura auranki da dan uwanki Tasu'u, kinko san kedai kamarki kinyi kadan kisa yayi kaffara saukin ki daya ki rungumi kaddara"
YOU ARE READING
*HUDAH 'YAR KARYA....*
Romance*HUDA YAR KARYA* _Labarine akan wata yarinya mai suna huda wadda ta dauki karyan dunia ta daurawa kanta alhalin ita ba yar kowa ba_. _Matashiyar yarinya ce mai tsabagen San karya da San gayu da shiga ta alfarma dansan abun dunia, Wanda kallo daya za...