HUDAH Y'AR KARYA..71

812 84 28
                                        

☁️☁️☁️☁️☁️☁️☁️☁️☁️☀️🐔
_*(HUDAH Y'AR KARYA..💁🏻‍♀️)_*

     🐤🐤🐤🐤🐤🐤🐤
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🐛

_Written By *ASY KHALEEL..✍🏻_*
     _*Wattpad@asykhaleel _*
        *_IG@asykhaleel_*

                 7️⃣1️⃣

Haka ya isa falon  kamar wani kumurci. ya nemi waje ya zauna ba wata gaisuwa yace,

"Ina jinku meke tafe daku?"

Gaisheshi sukayi ya amsa a fadace cikin tsawa ya maimaita masu tabayar,

"Nace meyake tafe daku?"

   Mamy ta saki murmushi wanda yafi kuka ciwo. Kamar yanda taima Hajiya bayani haka tasake maimaita masa, tana kaiwa inda zata bayyana masa cewa, yarta tana dauke da cikin dansa,

Cikin fushi ya dakatar da ita ta hanyar daka mata tsawa.

"Ya isa haka"

Yana mata alama da hannu irin karta sake fado wata Kalmar, sannan ya fara da cewa,

   "Ni zaku mayar karamin yaro wato kum qullo makircin ku kunnufo mu dashi dan ku 6atama danmu suna"
Yacigaba da cewa,

"Ance idan mafadin magana wawane majiyin sa bazai zama wawa ba,

Dan haka bazan bar wannan maganar ba saina hukunta ku, saina qwatar ma dana hakkinsa kamarku kunyi kadan ku bata masa suna"
Iyakar firgicewa su Mamy sunyi, ba kamar Maman Samira da jikinta yahau 6ari jitake kamar ta tashi ta ruga SBD firgici, fadi take,

Dan Allah yalla6ai ayi hkr wlh mu bamuzo da fada ba, kuma bamusan cewa ba kuda lbrn wannan lamari ba, wlh da bamu zo bama,

Amma zanso kuyi bincike kafin ku yanke hukunci, kaf unguwan mu babba da yaro ba wanda besan Hudah da Abdallah ba kullum suna nike da junan su".

  Amemakon ya fahimta da bayanin Maman Samira dukda yasan gaskia ne dansa zai iya mafiyin haka, sai cewa yayi,

"Zakuyi bayani ne idan kuka shiga hannu"

"In banda abin naku makirci ne ai bama ku ya kamata kuzo ku tinkare mu da wannan magana ba!

Idan abin gaskiya ne ina iyayenta maza?
Ko itama yarinyar taku shegiyar ce kamar yanda tayi cikin shege batada uba ne?"

Hajiya Hafsa ta mike da sauri tana cewa,

"Kaga Abban Abdul inhar baza..

Bata karasa ba shima ya mike yana nunata da yar yatsa,

"Wlh kika sake sako min baki saina miki abinda ban tabayi ba agaban wa'innan kazaman matan, munafuka kawai"

  Dole ta koma mazaunin ta tana kuka tare dayin dana sanin kiransa dan batayi zaton haka zeyi ba,

  Cikin matsanancin kuka Mamy ta furta,

"Tana da ubanta rasuwa yayi ba shegiya bace"

Alhaji ya tari numfashin ta da cewa,

"Saboda ya rasu shiyasa kika saki yarki atiti tayi cikin banza kikazo ki likama dana?

Inma hakan ne ya tabbata yana zuwa gunta kinsan iyakar shedanun da take hulda dasu?

Ko kunsan yawan 'yan iskan yaran da take fasikancin ta dasu sai yanzu da ciki ya samu kuka rasa wanda zaku likama saimu,

Kuma idan gaskiya ne meyasa tin farko baku neme mu ba sai yanzu?

*HUDAH 'YAR KARYA....*Stories to obsess over. Discover now