☁️☁️☁️☁️☁️☁️☁️☁️☁️☀️🐔
_*(HUDAH Y'AR KARYA..💁🏻♀️)_*🐤🐤🐤🐤🐤🐤🐤
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🐛_Written By *ASY KHALEEL..✍🏻_*
_*Wattpad@asykhaleel _*
*_IG@asykhaleel_*7️⃣0️⃣
Salati Mamy takeyi cikin rudani tama rasa yanda zatai da Hudah,
Ana cikin haka saiga Huzaifah ya shigo, Mamy ta qwala masa kira tana fadin..
"Zo Huzaifah ka temaka min ta sume"
Dagudu ya fada cikin dakin ganin yayarsa akwance malala ga Mamy akanta amma ta rasa abinyi.Dasauri ya fito ya dibi ruwa suka dinga shafa mata a fuska zuwa kanta, can tasaki ajiyar zuciya, atare sukai hamdala Huzaifah ya fita da sauri yana cewa,
"Mamy bari in samo a dai-daita mukaita asibiti aduba ta kinga kyarma kawai take"
Mamy ta tari numfashin sa da cewa,."Bafani da kudi Huzaifah na hannuna ko dubu daya basuyi"
"Allah zai rufa asiri Mamy" yafada tare da ficewa a guje.
Dan uwa kenan mai dadi, gaskiya ne kalmar hausawa hannunka koya rube baka cire shi ka yarda Allah kasa mudace.
Bayan likita ya baiwa Hudah temakon gaggawa, ya fito ya miqama Huzaifah farar takarda yace suje pharmacy su amso wannan allurar,
Ba jimawa Huzaifah ya dawo da ledan magani, ya isa ofishin likita ya sanar masa an siyo, likitan yace yaje yana zuwa, Huzaifah ya nufi room din dayaga Mamy ta shiga inda aka kwantar da Hudah,
Sun dan jima likitan beshigo ba, ganin Hudah tana ta bacci an saka mata drip, Huzaifah yace,"Mamy bari indan fita kozan samu rancen kudi karsu sake rubuto wani abun bamuda kudi"
Mamy taraka shi da addua tana saka mishi albarka. Dafitar sa likitan yashigo bayan yayi mata alluran ya juwa ga Mamy yana cewa..
"Mama munfa gode Allah kadan ya rage yarinyar nan ta fara bleeding, gaskiya da an rasa abinda take dauke dashi, wai maiya firgita ta haka ne?"
Mamy data tsare doctor da ido, cikin rashin fahimta ta ce,
"Ban gane ba d'annan meke damunta ne?""Toh a iya binciken mu mungano tana tare da damuwa wanda hakan na iya haddasa mata matsaloli da dama, nafarko in baku shawo kan komai ba tana daf da samun matsala a zuciya sannan sanadin tsoratan da tayi kiris ya rage tayi 6arin cikin jikinta...
Azabure Mamy ta mike tana fading,
"Likita me kake cewa ciki take dashi yar tawa ciki?""Qwarai kuwa Baba tana da shigan ciki amma meyasa kika damu haka batada aure ne?"
Zubewa Mamy tayi sharaf a kujera, daqyar ta iya furta,
"Tana dashi sedai ba a ko tare ba mijin nata bama ya garin yanzu haka""OK amma lkcn da aka daura auren yana nan?"
Mamy ta amsa mai da "eh yana nan"Likita ya jinjina kai tare da fadin.
"Haba Mama shine zaki damu kanki, ai koda awa daya yayi bayan daura aure ya isa ya bata ciki, kufa kuna gida baza kusan lkcn da zai ke6e da matarsa ba, kinsan mu yaran zamani akwai dabara"
Ya karasa magnar tare da zare safar hannunsa sai dariya yakema Mamy.Jinsa kawai Mamy keyi tana binsa da eh, ita kadai tasan abunda take saqawa a ranta.
Yana fita ta fashe da kuka ta jima tanayi, bakin ciki yasa ta tashi ta futo bakin titi ta tari abun hawa aka kawota gida,

أنت تقرأ
*HUDAH 'YAR KARYA....*
عاطفية*HUDA YAR KARYA* _Labarine akan wata yarinya mai suna huda wadda ta dauki karyan dunia ta daurawa kanta alhalin ita ba yar kowa ba_. _Matashiyar yarinya ce mai tsabagen San karya da San gayu da shiga ta alfarma dansan abun dunia, Wanda kallo daya za...