☁️☁️☁️☁️☁️☁️☁️☁️☁️☀️🐔
_*(HUDAH Y'AR KARYA..💁🏻♀️)_*🐤🐤🐤🐤🐤🐤🐤
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🐛_Written By *ASY KHALEEL..✍🏻_*
_*Wattpad@asykhaleel _*
*_IG@asykhaleel_*6️⃣6️⃣
Haka dai Hudah ta tsayama Muhibbah komai za'ayi sune manyan friends,
Maganar tururuwan samari awajan Hudah, abun ba a cewa komai kowa ya bude baki Kalmar so yake gaya mata a ciki harda manyan abokan ango.
Washe gari aka daura aure, daran ranan akai dinner,
Awajan dinner ne Hudah ta hadu da mutane iri iri maza da mata sai amsar num dinta suke,Faheem shi yafi kowa manne mata, tin daya daura ido a kanta yake rawar jiki ba abinda yafi dauke masa hankali kamar dressing din jikinta.
Wani tsadadden farin lace ne a jikinta an masa dinkin doguwar riga wanda tasha ado da stones, a wuyarta sarkan gold ne ga warawaran shi da zube sai zuba walwali suke a hannayen ta,
Ahaka take ta kaikawo cikin hall din ga wani siririn bakin mayafi ta na sagale dashi ahannun ta, ita bata yafa ba sannan bata mayar a jaka ba, akafarta bakin takalmi ne da jakar shi itama baka,
Duk inda ta juya idon jama a akanta yake ba iya mazan wajan ba hatta yan matan dake kaikawo satar kallonta suke,
Bayan taro ya tashi lfy, washe garin biki Hudah tayi sallama da amarya da iyayenta.
Ta fito zata karasa gidan Aunty sadeeya, nan taci karo da motar Faheem a kofar gida, da alama jiran fitowanta yake duk da bata bashi izinin zuwan ba,
Dayake tin jiya ta sanar dashi ayau zata wuce dutsinma.
Tsaki taja kafin ta karasa gareshi, dan ita Sam guy din bekwanta mata ba, gashi dai masha Allah babu wata makusa ajikinsa da gani akwai alamun hutu atare dashi,
Sedai ko kadan hakan bai dadata da kasa ba, dan yanzu takan danganta kanta da matar aure.
Fitowa yayi yana mata murmushi tare da fadin,
Gimbiyata barka da karasowa, Hudah tadan saki fuska tare da fadin
"Yauwa sannu da zuwa," haka yaita janta da hira kusan minti biyar, ita kam sai yamutsa fuska take sakamakon tashin kamshin shisha dataji yana yi,
Sam batason wannan abun duk da Abdallah naya sha sedai tin daya lura bataso ya dena kusanto ta mutukar yana tashin kamshin.
Dubansa tayi tare da cewa,"Toh Faheem nifa zan wuce, sai ince dakai saduwan alkairi"
Tana kaiwa nan ce da yar rakiyanta,
"Muje ko kanwata"Feheem yasha gabanta da sauri yana fadin.
"Kuje ina kuwa?""Car park mana" ta bashi amsa a takaice.
Dakatar da ita yayi da cewa, dan Allah ki tsaya haba Hudallah bafa ayima masoyi haka duk da nasan banida wani matsayi awajanki..Da wannan dadin bakin nashi har yayi nasarar shawo kanta ta shiga motarsa ya kaita har dutsinma gidan.
Aunty sadiya tayi murna matuka da ganin ta, yini guda sukai suna hira washe gari tin wuri ta gama shirin dawowa gida kd, misalin shadaya na rana ta kira Faheem ta sheda masa ta shirya, dalilin hadata da Allah da yadinga yi akan inta tashi tafiya ta kira shi suyi sallama.
Haka kuwa akai, cikin mintunan da basu wuce goma ba sai gashi ya iso.
Sosai yaso Hudah ta yarda ya kawota har kd acewar sa bata canci shiga motar haya ba, murmushi tayi tare da cewa.
"Wlh nagode kabarshi kawai" ganin ta kafe yasa dole ya hakura.
Kudi masu yawa yabata wanda akalla zasu kai dubu dari, nan sukai bankwana acewan yananan tafe next week.
Yana juya baya Hudah ta saki murmushi aranta tana fadin,
"Namiji ko dan wahala wai zezo kd next week to sai kazo nasan yanda zanyi dakai tinda kaima an yanka maka kazar wahalar.Cikin gida ta koma sukayi sallama da Aunty sadeeya, har tashan moto ta rakata seda taga tashin su tace agaida Mamy sai sunzo biki.
Sunyi tafiya mai nisa, sai da sukazo cikin daji inda babu wasu jama a sai motoci dake wucewa jefi jefi.
Wani matashi dake zaune kusa da driver a gidan gaba, ya bukaci driver yadan tsaya zeyi fitsari,
Tsayuwan motar keda wuya sukaga an yima motar zobe, wasu zaratan samari ne rike da bindigogin su,
Sunkai sama da mutum ashirin duka fuskokin su daure da qyalle,Ilahirin mutanen dake cikin motar sun firgice, nan suka bukaci kowa daya fito sannan kawanne ya tabbatar ya fito da kudin jikinsa,
Ga wanda ya rage wani abu inhar muka gano shi to hukuncin kisa ne.
Duk motar data dinfaro gudin juyawa take aguje sun kumayi sa a basa harbin su daga nesa hakan na nufin wannan motar kadai suka biyo.
Wani abun mamaki suna fitowa cikin yan fashin wani yayi gefe da Hudah ita da Jakarta,
Kafin cikar mintuna goma sun gama karban kudaden motanen nan, sannan suka umarci kowa ya koma moto banda Hudah dake shar6an kuka, wani kakkauran Matashi ya rike hannunta gam tana gani driver yaja moto suka wuce aka barta a hannun yan fashi.
*Tofa😳 yau kuma da Y'an Fashi Allah ya hudah dasu🤦🏻♀️ Ku biyo dan jin yadda zata kaya amma se naga ruwan comments sannan zan cigaba🤒
YOU ARE READING
*HUDAH 'YAR KARYA....*
Romance*HUDA YAR KARYA* _Labarine akan wata yarinya mai suna huda wadda ta dauki karyan dunia ta daurawa kanta alhalin ita ba yar kowa ba_. _Matashiyar yarinya ce mai tsabagen San karya da San gayu da shiga ta alfarma dansan abun dunia, Wanda kallo daya za...