*HUDAH Y'AR KARYA..*55

1.6K 113 20
                                    

☁️☁️☁☁☁☁☁☁☁️☀
🐔 _*(HUDAH Y'AR KARYA....💁🏼)*_
         🐤🐤🐤🐤🐤🐤🐤
  🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🐛

_Written By *ASY KHALEEL...✍🏻*_

         Wattpad@asykhaleel
           Facebook Group
        Asy khaleel Novel's grp
             IG @asykhaleel

                      5️⃣5️⃣

Hankalin Momy yayi matukar tashi da ganin danyen aikin da ya Haiydar yayi, tashi daya ya canjawa yarinya halitta, fada ta rufeshi dashi sosai tana fadan,
" ka zalumci marainiya haka kawai ka kama ta da wannan irin mugun duka dan cuta"

Betsaya sauraron kalaman Momy ba ya ja cute  suka fice daga gidan,

  Mum tayi zaton asibiti zai nufa da ita shiyasa batayi hanzarin hana shi tafiya da ita ba.

   Bayan kwana biyu da faruwan haka, Momy ta kira Asy da Hudah dan taji gaskiyar abin dake faruwa, har gida suka isketa basu tsaya 6oye-6oye ba suka  bayyana mata gaskiyar lamarin,
Nasiha Momy tai masu  sosai akan su kula da Kansu, cute kam tin daga ranar ta koma gidan yayanta da zama,

    Bayan sallar magrib Hudah tana zaune a palon Mamy suna kallon Hausa film, wayarta dake gefanta yai qara, wani yalwataccen
murmushi ya bayyana a fuskarta ganin sunan daya  bayyana a screen na wayara zuciya ta sake maimata.

"Wai my husband, lallai guy din nan kanada aiki a gabanka, yazama dole in goge name innan, inko nayi sake Sawad yaga wannan naga takaina"

  Answer ta danna tare dayin sallama, kusan 5mins tayi shuru tana sauraronsa fuskarta cike da annuri ga dukkan alamu tanajin dadin kalaman dake fita daga gare shi, daga bisani ta zaro idanu alamun tadan razana, jin ya ambaci gashi a kofar gida,

"Lallai guy din nan ya cika dan anace yanzu seda ya gano gidan mu". Maganarsa ya katse zancen zucin da take,

" Haba gimbiyata wannan jan ajin  da kike min ya isa  dan Allah  a barni haka, mi yasa bazaki tausaya min ba?  yau  in har banyi tozali da fararan idanun ki ba, tabbas bazan sami  kyakkyawan bacci ba, Hudallah wlh duk wani tunani na nakine kece ta  farko a cikin ruhina dake nake kwana dake nake tashi Dan Allah ki daure ki fito  mugaisa koda na second  daya plz my sweet baby Cikin murya mafi rauni ya karasa maganar wai duk dan yasamu shiga a wajanta,

yanke kiran tayi batare data furta komai ba, sannan tamiqe bayan ta sanar da Mamy tayi bako,  

dakinta ta nufa ta daura karamin hijabi a saman black jallabiyar dake jikinta ta fita ..

   Jingine yake a jikin motarsa ya harde hannayen shi saman kirji kafarsa daya kan daya,  yana ganin fitowanta ya sake dai-dai ta tsayuwansa yana aika mata sakon murmushi har ta karaso gabansa,

    "Assalamu alaikum" tafada cikin sanyin murya.
Sai daya sauke ajiyar zuciya, kafin ya iya amsa mata sallamar, daganan suka tsundoma cikin hira irinta masoya.

Yayinda Abdallah  ya zage yana karanto mata kalaman kauna dayake shi gwanine a wannan fannin, ita dai Hudah jinsa kawai take sai idan taji ya fado wata kalmar tayi murmushi, acan kasan zuciyarta, sosai ta masu daya bata  waje gudun kada yajawo mata fushin Sawad dinta, tasan kadan daga aikin Sawad ta ganshi kwasam agabansu, dayake shi zuwan bagatatan yake mata, dan haka ta matsawa Abdallah da cewa,
"dare yayi fa, gashi banyi sallar isha ba"

   Abdallah ya tsareta da mayun idanunsa masu rikita mata lissafi, ba shiri ta sadda kanta kasa ta rasa dalili ko alama bata  jure kallon sa.

  " na fahinci kina tsoron kadda wanda ya fini matsayi yazo yaganmu tare ransa ya 6aci, shiyasa kike korata ko?"

     Dasauri ta daga kai ta kalleshi azuciyar tace.
  "Kaji guy dinnan kamar ya shiga  zuciyata. Afili cewa tayi
  "Haba dai taya zan kori kyakkyawan masoyi kamar ka, kaima kasan ba haka bane, sauri nake kada in rasa sallah kaga yanzu tara saura .

Abdallah ya kada kai yana murmushi,  ko ba komai yaji dadin yabon data masa, duk da yasan abin da ta fada ba haka bane sodai take yabar wajan maybe akwai wanda bataso su hadu dan ya lura kamar a tsorace take,

  Motarsa ya bude ya fito da wata katuwar leda wanda cike take da kayan ciye ciye, aciki harda kudi dubu dari   ya saka a envelope  tare da wata farar takarda wanda ba komai bane aciki sai kalaman soyayya, da irin yanda ta mamaye zuciyarsa lkc daya har yake bayana mata cewa, in har bai samu amincewan ta ba, babu shakka rayuwansa zata kasance cikin Matsala,......

*KING ASY KHALEEL...*✨

*HUDAH 'YAR KARYA....*Where stories live. Discover now