☁️☁️☁️☁️☁️☁️☁️☁️☁️☀️🐔
_*(HUDAH Y'AR KARYA..💁🏻♀️)_*🐤🐤🐤🐤🐤🐤🐤
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🐛_Written By *ASY KHALEEL..✍🏻_*
_*Wattpad@asykhaleel _*
*_IG@asykhaleel_*6️⃣1️⃣
Figan jikinta tayi rai a6ace take fadin, "gaskiya kayi hakuri bazan iya ba" tana kaiwa nan ta bude murfin motan ta fito jiki a kasalce ta nufi cikin gida, direct dakinta tashige tafada saman bed zuciyarta cike da tunani iri iri, wani 6angaran tana shakka akan Abdallah, inda zuciyarta ke raya mata anya kuwa Abdallah son da yake furta min gaskiya ne?
Tin daga ranar Abdallah ya canja salon takunsa yanzu ya dakar da zuciyar shi besake nunawa Hudah maitarsa akanta ba, a6angaran Hudah itama d'ar d'ar take dashi don ta tsorata da yanayinsa, ta fara sakin jiki dashi ne ganin yanzu har yadan rage zuwa gidansu ba kamar yanda ya saba kusan kullum suna tare, koda Hudah ta tambaye shi dalilin rage zuwa da yayi ko tayi masa laifine, anan ya cikata da dadin baki yana fadin "hakan shine mafita agaremu my wife, ko kadan banason aikata ba dai-dai ba akanki shiyasa nadan ja baya da zuwa, yacigaba da cewa,
Hudallah bazan boye miki ba kin hada komai wanda duk namijin daya kalleki tabbas saiya kai zuciya nesa, babban kuma yanda kika gwane a6angaran soyayya ga wasu zafafan kalaman kauna da suke fita cikin zazzakar muryan nan taki mai fidda ruwan sauti, uwa uba kallonki wanda shi yakan sa in mance duniyar da nake, bare kuma ki hada da murmushin nan mai kunshe da sakonni. Kai agaskiya nafi kowa dacen mata..
Wayan hanunta tadan bigeshi da ita tana cewa,
"Kafara kenan ko? wannan bakin naka ko gidan radio sai haka, mutum yaita zuba ba sassautawa"Dariya yayi zai cigaba daga inda ya tsaya, Hudah ta tari numfashin sa da cewa,
"Yanzu dai ba wannan ba maganar ankon Muhibba kaga saura 7weeks kuma na fada maka har KT zanje mata biki, so kudi zaka bani isassu kaga inaso in hada kaina sosai tayanda babu shegiyar da zata min kallon raini ehee, kasan Muhibba yar babban gida ce dole za a tara classic ladies kaga kaima baza kaso Hudanka ta fita daban ba ko?Ta ida maganar tana mai fari da ido, murmushi Abdallah yayi aransa yana jinjina tsarin da Hudah ta daurama kanta, ita dai a koda yaushe tana son tayi shiga ta alfarma, tuni ya karanci ba abinda tafiso kamar ta fita cikin kasaitacciyar dressing don haka ya dage wajan nuna bajintan sa lokaci lokaci yakan dauketa zuwa plaza ta zabi kalar kayan da sukai mata, wannan dalilin ya kara mata sonshi shiyasa besha wuya ba wajan mamaye zuciyarta, cikin murmushi irin ta masoya ya dubeta yace,
"Dadina dake qosawa ai ina sane gimbiyata, yanzu nawa kike ganin zasu isheki har kije ki dawo?"
"Kai zaka kani ai, in yaso sai in dawo a motar haya, yanzu ka bani 100k inaga zasuyi"
"Owk kina ganin sun isa zasu wadace ki?"
Abdallah ya tambaye ta, a takaice Hudah ta bashi amsa da,"Insha Allah zasuyi"
Da haka dai Abdallah ya sake samun damar yau darar Hudah a karo na biyu ta sake aminta dashi har yakai ta dena wani kokwanto akansa ta saki jiki dashi sosai ganin yanzu ma akasari in yazo awaje suke hira sa6anin da dasuke yi a moto..
*AFTER 2 MONTHS*
Misalin 5:30 na yammacin ranar Sunday ranar data zamo rana mai matukar qunci da bakin ciki ga Hudah ranar da bazata manceta ba a shafin rayuwanta.
Kwance take gefan gado tana editing wasu hotona datayi a phone dinta, riga da sket na English wears ne a jikin ta kasancewan sune kayanta na zaman gida.
Ita kadaice a gidan Mamy ta tafi gidan suna, Sai data kammala girkin da Mamy ta barmata sannan ta watsa ruwa agurguje tayi simple make up tana kammalawa ta fara gyaran pics.Kiran Abdallah ne ya shigo wayarta take taji wani sanyi ya ziyarci zuciyarta da sauri ta manna wayar a kirjinta tasaki ajiyar zuciya, kasancewar dik yau bataji muryan shi ba ta kira shi wayarsa a kashe, dauka tayi tana mai adduar Allah yasa ya dawo ne don tana missing nashi ba kadan ba, dake ya sanar da ita zedanyi tafiya na kwana biyu, yau kwana ukku kenan rabanta data sashi a ido,
shiyasa kewarsa ya addabe ta gashi inda yake akwai matsalar network basa samon junansu kowani lkc, sai data shagwa6e fuska tamkar yana ganinta ta fara magana tana dad'a narkar da murya, katse ta yayi da cewa
"Gani a waje my Hudah please come out"Dirowa tayi daga saman gadon, dasauri tasaka hijabinta tayi waje, sosai ta tsorata dajin yanda yai maganar,
Tana fita cikin motan ta afka dan ta matsu dasan ganin halin dayake ciki. Jajayen idansa ya watsa mata batare daya furta komai ba, itace tayi karfin halin kiran sunansa,
"Abdallah lfy? Meke damunka kwana biyu kacal naga dik ka canja plz bakada lfy ne? Tana maganar ne kamar me shirin 6arkewa da kuka coz tausayinsa daya mamaye ta. Hannunta ya rike yanadan murzawa idonsa kam akan Hudah itama shi ta watsama nata idanun, dakyar ya budi baki ya furta,
"My Hudah ina cikin. Matsala ki tausaya min plz"
Yana kaiwa nan bejira cewanta ba ya ja motar suka bar wajan. Tsananin tsoro da firgici ya bayyana a fuskar Hudah, sedai ta kasa furta komai illah kanta data hade da guiwa kirjinta na dukan tara tara ko me Abdallah yake nufi?......Readers amsa na gunku...muji ra'ayinku, kafin muje nxt page

YOU ARE READING
*HUDAH 'YAR KARYA....*
Romance*HUDA YAR KARYA* _Labarine akan wata yarinya mai suna huda wadda ta dauki karyan dunia ta daurawa kanta alhalin ita ba yar kowa ba_. _Matashiyar yarinya ce mai tsabagen San karya da San gayu da shiga ta alfarma dansan abun dunia, Wanda kallo daya za...