☁️☁️☁☁☁☁☁☁☁️☀
🐔 _*(HUDAH Y'AR KARYA....💁🏼)*_
🐤🐤🐤🐤🐤🐤🐤
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🐛_Written By *ASY KHALEEL...✍🏻*_
Wattpad@asykhaleel
Facebook Group
Asy khaleel Novel's grp
IG @asykhaleel4️⃣6️⃣
Cike da nutsuwa Hudah ta gaisa da mahaifiyar Asy, sa'annan ta kawo tsaraban turaruka masu kyau ta bata..
Kyakkyawar dattijowar da suke kira Mama, cikin sakin fuska ta amsa tana sanya mata albarka,
Daga bisani ta maida duban ta ga yar tata ta ce.
"Asy banfa gane yarinyar nan ba, anya na santa kuwa?"Mama ba zaki santa ba, kawata ce tin muna makarantan Malam yunus, karatu ta tafi can qasar Egypt kwanan nan tazo"
Asy na kaiwa nan tabi hanyar kitchen tana daria.Allah sarki Mama ta fada,
"Ashe 'yar tawa bakuwa ce, ya sunanki ne?Murmushi kadai Hudah keta zubawa, jin shareriyan da Asy ta shara lkc guda, a kunyace ta amsa da,
"Sunana Hudallah"
"Masha Allah sunanki mai dadi da ma'ana, ya karatu Hudallah?
"Alhmdulillah Mama muna ta6awa"
"Madallah to Allah ya temaka, cewan Mama, suna cikin haka Asy ta dawo hannun ta rike da dan madai daicin tray tayi ripping dinshi da wata leda mekyau.
Kallon Hudah tayi tace mukarasa daga ciki ko Hudancy!
Owk tafada tare da mikewa ta bi bayan ta suka yi dakin ta,Gefan gado Asy tai mata nuni data zauna, wani qaramin table Asy ta janyo ta aza tray din akai, sannan ta dai-dai ta zamanshi a gaban Hudah ta ce.
"Bismillah my Hudancy 'yar sudaniya... Atare suka bushe da dariya,"Aifa my Asy kin iya gillota babu ko kunya.
Ni din da ko hanyar Lagos bansani ba, rana daya harkin kaini Egypt.Cikin dariya Asy ta ke cewa.
Yo ai dressing din jikin ki na kallah take naga kinfi kama da yar qasan Egypt din, bakiga Mama harta shiga ba, wlh kin hadu Hudancy na kuma yarda bakya shigan qasqanci wanan irin kashe kala aini sakin baki da hanci nayi ina qare miki kallo.Hmmm Hudah tadan murmusa gami da cewa,
"Ah haba dai miye abun kallo a yar villg.... Bata qarasa ba Asy ta toshe mata baki tana daria."Kai Hudah baki da dama ashe baki manta ba.
To kisha kurmin ki kin tashi a yar village kin zama wise girl ..
Hudah zatai magana Asy ta tari numfashin ta da cewa.
"Yanzu dai kafin mu tsunduma kogin hira. Kidan ta6a wannan takai hunni tana 6are ledan data rufe tray din.
Fruit ne aciki ta kawo mata masu energy irin su.
Kwakwa, gwaiba, Apple, danino, inibi, kankana lemon abarba, tarkace kala kala ta hado mata duk ta yankasu kanana ta shirya su kashi kashi abun saiya bada ma'ana.Sosai Hudah ta jinjina karamci irin na Asy, don ta burgeta matuka, dubanta tayi ta ce.
"Kai my Asy star duk ni kadai wannan kayan dadi haka ina zan kaisu kaman dai mu goma zamu sha?"Duka ki take cikin ki dasu, kinga ni babban abincina kenan, bana sauraron waise an kawo na duka gida,
Ke nifa ko irin saurayi zaizo gurina yadan kirani kafin. Yana cewa mai zan taho miki dashi cewa nake fruit ko in fadi wani drink din mai energy.
Kema yanzu na baki samples don duk suna cikin plan dinmu,
Irin wannan ciman shi akafi so mu yawaita cinsu musumman mu mata,
Bawai koda yaushe ki take ciki da abinci me nauyi ba no.
Anfi so muna yawaita cin fruit wani lkc in kina da dama kiyi juice na kayan itatuwa zallah .
Ina fada miki in har kika jure cin ya'yan itatuwa wlh cikin qanqanin lokaci zakiga yanda fatar jikin ki zata sha bamban data wanda bata samun cin irin su, ga kuma qarin lafia ajiki.
Betsaya iya nan ba, indai wannan ciman ya kama jikin ki to wlh ko mijin da kika aura seyasan ya auri mace mai ni'ima, in kuwa kina da kishiya ayi dace ita din ballagaza ce, to wlh sunanta sorry dan zata kwashi kashinta ahannu.
Ke Hudah amfanin fruit yana da yawa, yar uwa ki gwada zaki bani lbr.Bari mu koma 6angaran na Fulani da kuma mazaunai.
Akwai had'e had'en da akeyi na kunun alkama da farar shinkafa,
Kayan hadin suna da yawa domin dadi ake hada mai sosai, sai ayi garin su, kullum da safe ki malkada gyadarki ki dafa sai ki rinqa damawa da ruwan gyadan,
Bayan kin dama sai ki kawo garin madara ki zuba in kina son sugar kisa wlh akwai dadi sosai ga kuma gyara fatar jiki, yazama shine abin breakfast din ki,
Za kiga yanda nonowa zasu yi tantsama tantsama, nan da nan zaki ga kin canja,
Sannan akwai tablet da cream Wanda zaki hada dasu, na yarda da aikinsu kuma ba suda illah na gwada na kuma yaba,
Sai kuma sabulun wanka dasu mayuka, irin su turarukan jiki, akwai na Muslim akwai na bature wanda ya amshe ki shi zakiyi, ko kuma muyi mix kinsan bature shegene nashi emergency ne.Hannu Hudah ta bata suka tafa,
Murmushi kawai Hudah takeyi.
Lokaci lokaci takan dauki abunda ya mata takai baki. Sedai hankalin ta na wajan abunda Asy take fada.Asy tacigaba da cewa,
Matakin farko daya kamata ki fara dauka kenan kin tsaya sai tara tsummoki kinan adole ga yar gayu.
Yanzu kije na baki nanda 6months zakiga yanda zaki canja,
A lokacin ne zakiga masu qumban susa suna yi muku kara kaina da manyan motoci a kofar gida."Hahah kina bani dariya Asy, inafa zanga irin wa'inda kike nuji nida nake a ghetto erea!.
"Ke dalla wayace miki na miji yana kallon wani ghetto?
Ai wlh sedai in baki cika yanda suke so ba,
Tabb wai ghetto hmmm hudah dakwai sauranki wlh,
Yo namiji indai ya hanga ya ganki fara sol, yanda kike da dogon hancin nan kaman ke ki kaiwa kanki, ga kuma gashi dai-dai gwargado, ya ganki gaba acike baya masha Allah.
Nonowan nan nayi atsaitsaye kyam suna yi kaman zasu tsokale mai ido,
Maganar hips kuwa,
Duk inda kika motsa suna fadin.(Bana yara bane in ka isa taso ka taya!)
Fatar jikin ki taushi li6is, by mistake hannun ki in yadan hadu da nashi ilahirin jikinsa saiya amsa, to yashi lallausar hannu wanda ko audugan rimi albarka,
Tuni dama kin gwane wajan iya dadadan kalamai da kuma sarrafa idanuwa, dama gaki dasu dara dara tubar kallah.
Dik sanda yazo hira, cikin kissa zakina watsa masa wani sahihin kallo mai dauke da sakonni kala kala,
kutt ai wlh ko Ubanshi ne gwamnar garin nan tuni zakiga ya haukace miki, sai abunda kika ce, hidiman da baya yima uwar data haifesa shi zakiga yazo gidanku yana yi,
Gaisuwar da ko Uwarsa da Ubansa basa samun kwatan kwacin ta,
Gwuiwa bibiyu zaki ga yana kwasa a gaban iyayenki.
To ya hangi gidan dadi,
Ke wlh wani ma take zaisa a rushe gidanku amaida shi ginin zamani koda beyiwa iyayensa ba,
Hmmm kedai kibar namiji dan banzane akan mace, wlh ba abunda baza su iya ba, har kike kawo batun wani ghetto erea, wlh ko dajin rugu kike qarewanta kenan, to namiji zai iya binki indai kin hada abunda yake so.
Kedai tsaya kallon ruwa kwado yai miki qafa.
Itama ta bushe da daria harda kwanciya,
Tuni daman Hudah daria take harda su hawaye,
Asy kam ta haqiqice abunta sai zuba dogon sharhi take. saiji suka yi an baki kofar dakin da qarfin tsiya..*Oya shower me with tsantsan So😍 by voting n commenting harma sharing da masoyanku if dis chappy really made u feel something*

ESTÁS LEYENDO
*HUDAH 'YAR KARYA....*
Romance*HUDA YAR KARYA* _Labarine akan wata yarinya mai suna huda wadda ta dauki karyan dunia ta daurawa kanta alhalin ita ba yar kowa ba_. _Matashiyar yarinya ce mai tsabagen San karya da San gayu da shiga ta alfarma dansan abun dunia, Wanda kallo daya za...