☁️☁️☁️☁️☁️☁️☁️☁️☁️☀️🐔
_*(HUDAH Y'AR KARYA..💁🏻♀️)_*🐤🐤🐤🐤🐤🐤🐤
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🐛_Written By *ASY KHALEEL..✍🏻_*
_*Wattpad@asykhaleel _*
*_IG@asykhaleel_*7️⃣2️⃣
*_AFTER 5 YEARS!._*
Hudah na hango ta fito daga keke napep, tana rataye da baby girl wanda akalla ba zata wuce 6 months ba,Daga bayanta wani magidanci ya fito mai kimanin shekaru arba'in aduniya (40 years) shi kuma yana dauke da baby boy wanda zai yi wuya ya cike shekaru biyu da haihuwa (2years)
Sai kuma yar matashiyan yarinya wanda zata iya kai shekaru goma (10 years) kenan inji bature,
Basuyi garajan fito da kayansu dake. cikin napep ba,
Hudah ta bukaci me napep da yadan dakata ta shiga ta gani ko gidan da suke nema shi din ne dan taga gurin gaba daya ya canja mata kamanni.
Koda tashiga wasu sababbin fuskoki ta gani hakan ba karamin fadar mata da gaba yayi ba domin.
Idan akwai abunda zata mance a shafin rayuwan ta to lallai banda wannan gidan koda kuwa an rusheshine aka canja sabon gini tabbas zata bada shedan nanne filin gidan ubanta,
Bayan sun gaisa da mutanen gidan, nan Hudah ke tambayar, "dan Allah ko kunsan tsufaffun zama agidan?"
Daya daga cikin matan ta bata amsa da cewa,
"Wlh bamu sansu ba, amma ki shiga maqwaftan mu akwai dadaddun zama a layin".
"Su Maman Samira nanan?"
Hudah ta tambaya, matar tace itama ta tashi sunyi gidan kansu a hayin na iya amma dai Maman Safeeyah tananan naji ance ta dade a gidan, Hudah tayi musu gdy tare da juyawa ta fito.Tin a kofar gida taci karo da yarinyar da ake kira Safeeyah ta zama katuwar budurwa,
Kallon Hudah tayi na kusan minti biyu kafin ta furta.
Aunty Hudah dan Allah ke nake gani?"Hudah ta sakar mata murmushi ai da gudu Safeeyah tazo ta rungumeta tana ihu ga Aunty Hudah ga Aunty Hudah.
Abinka da ghetto erea mata da yara a kayo waje wa'inda suka santa harda hawayen farin ciki,
Maman Safeeya ta rungumeta sukayi cikin gida,
Bayan angama farin ciki Mmn Safeeyah tai masu rakiya har kofar gidan Huzaifah dake 'yan majalisu (Dutsamma street.)Suna isa Hudah ta qame qam a bakin gate din gidan,
Kallonta takai ga Maman Sadeeya tace,Yanzu wannan gidan na Huzaifa me?"
Mamman Safeeya tai dariya tace,Mai kikeci na baka ke zuba ai kallo na daga ciki Hudallah kedai ku fito da kaya a sallami me napep ko kwa samu Ku huta da yan yaran nan,
Bugawa sukayi maigadi ya bude bayan yan tambayoyi yaje ya isarwa masu gida cewa ga baki awaje wai sunce ace maku su Maman Safeeyah ne, ba 6ata lkc aka bashi izinin ya bude masu duk da sunyi mamaki meyakawo Mmn Safeeya da magriba,
Gaba daya suka dunguma cikin gida akabar Usman awaje sai yayi alwalla ya shiga masallacin kofar gidan danya gabatar da sallah.
Shigarsu yai dai-dai da Samira ta fito daga part dinta tana rike da farantin abinci zata nufi shashin Mamy,
Karaf idanta ya sauka akan Hudah, chak ta tsaya kamar wacce akaiwa allurar soja.
Cikin murmushi Hudah ke tinkarar inda take ai ji kake tasss ta saki tiran hannunta ta doka uban tsale tare da fadin
"Aunty Hudah kece nake gani??

YOU ARE READING
*HUDAH 'YAR KARYA....*
Romance*HUDA YAR KARYA* _Labarine akan wata yarinya mai suna huda wadda ta dauki karyan dunia ta daurawa kanta alhalin ita ba yar kowa ba_. _Matashiyar yarinya ce mai tsabagen San karya da San gayu da shiga ta alfarma dansan abun dunia, Wanda kallo daya za...