HUDAH Y'AR KARYA..64

1K 96 19
                                    

☁️☁️☁️☁️☁️☁️☁️☁️☁️☀️🐔
_*(HUDAH Y'AR KARYA..💁🏻‍♀️)_*

     🐤🐤🐤🐤🐤🐤🐤
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🐛

_Written By *ASY KHALEEL..✍🏻_*
     _*Wattpad@asykhaleel _*
        *_IG@asykhaleel_*

                   6️⃣4️⃣

Sosai Hudah ta matsawa Asy akan ta saka baki a bata hayar dan kunnin gold, baya da tsadaddun kayan data amsa har kala biyu kuma kowanne da mahadin sa,

  Shi gold din da Hudah take mitar a bata, ba kowa suke baiwa hayar shi ba,  sai wanda suka tabbata tana da abun biya, gaba daya  yake dan kunni da sarkan wuya sai warwaron hannu da zube,
Babban gold ne mai tsadar gaske, tinda Hudah ta kyalla ido taga anba wata mata hayar shi, takafa mitan abata taje bikin Muhibbah dashi.

Asy tayi tayi akan ta hakura tinda sun nuna ba zasu bata ba, har take fasa mata kai da cewa.
      "Babu wata haifaffiyar cikin garin Kaduna da har zata ziyarci wani state a fadin Nigeria nan a raina mata,
Bare kuma ke Hudah wlh ko fadar shugaban kasa akace ana gayyatar fitattun 'yan mata, toh wlh bama sai kinyi renting ba za a je dake kuma dole a kalle ki,

Ballantana ke da zaki garin kauyawa irin Katsina duk kinbi kin damu kanki sai wani fadin Muhibbah kike to bari kiji koda yar gwamnar garin ce ita wlh ba abinda zata gani ajikin ki ta kushe ki, ke inma tai sake sai kin fita cinye adon, kuma kije zaki gani da idonki sai kin dawo musha lbr, kauyawa ne na gidi🙉 lolz.

Tofa na tsokano tsuliyar dodo, qafa me naci ban baka ba🏃🏻‍♀ har na hango katsinawan na hararata😜

Ko kadan kalaman Asy basusa Hudah ta hakura ba, acewanta yanda zatayi shigar tsadadden lace zefi dacewa ace ta hadashi da gold din nan,

Dan haka ta tilasta Asy sukaje  dole ta shiga tai ruwa tai tsaki har aka ba Hudah hayar gold din,
      
     Sedai akan sharadin kwana hudu kacal zeyi a hannunta, kudi masu yawa ta biya, sannan suka qara jaddada mata ko kwana daya ya kara a hannun ta saita biya kudin kwanan daya kara..

     Tin ana gobe ta gama shirya komai da zatai tafian dasu, a6angaran Abdallah sha'awar Hudah ya hanashi sukuni ido bude yake neman hanyar da zata sake sada shi da ita, tunawa yayi da halin Hudah, yasan in dai biki ya taso mata ji take kamar tai sata dan dai taga ta zarce sa'annin ta a dressing,

Dan haka ya zage komai ta tambayeshi baya mata musu, sedai  ya dauki alwashin zaiyi amfani da wannan damar wajan  magance cutar data addabe shi.

Washe gari tin safe  Hudah taje gidan wata shahararriyar mai zanen lalle.  Kudi matar ta lafta mata sosai dan taga alamunsu a tare da ita,
Kunsan halin mutanan mu na Nigeria ko market ka shiga sai an qare maka kallo kafin a sanar dakai  farashin kaya, lolz Allah ka azurta mu arziki kyakkyawa duniya da lahira Ameen.

Lalle Suhaila  ta natsu ta zanawa Hudah irinna yad'awa a social media, tin takwas nasafe take akan Hudah basu suka gama ba sai wajan shadaya na rana, ammafa duk wanda ya ga Hudah saiya yaba dayake abun ya dace da jiki. 

  Mutanen dake shige da fice a gidan me lallin sunyi zaton Hudah itace amaryan ganin  yanda Suhaila ta 6ata lkc akanta.

    Abdallah ta kira ta ce yazo ya dauketa, duk ta matsu data koma gida ko dan ta samu tafia akan lkc  dan tanajin kamun nan da za ayi a babban Hall din dake cikin garin katsina, kar ayi bata gashi  lokaci ya kure mata.

Ba a fi minti goma ba ya isa kofar gidan, dayake shiya kawo ta da safe, tana jin tsayuwan motarsa ta dauki Jakarta ta rataya sukai sallama da Suhaila ta fito,

*HUDAH 'YAR KARYA....*Where stories live. Discover now