☁️☁️☁️☁️☁️☁️☁️☁️☁️☀️🐔
_*(HUDAH Y'AR KARYA..💁🏻♀️)_*🐤🐤🐤🐤🐤🐤🐤
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🐛_Written By *ASY KHALEEL..✍🏻_*
_*Wattpad@asykhaleel _*
*_IG@asykhaleel_*7️⃣3️⃣
Hudah tai dariya tare da cewa,
"Lallai dan uwa arziki na Allah, Nima na dade da gane ba maiyi sai Allah mutum bai isa ya kai kanshi inda Allah be kaishi ba,Ammafa gaskiya naji dadi sosai daka auri Samira, yarinyar tasan mutumci".
Huzaifah yayi murmushi ya ce,"Aunty Hudah ai bakiga komai ba,
Yarinyar nan tinda Mamy ta kwanta ciwo,Koma ince tin daga ranar da kika bar gida babu safiyar da ba zata shigo ta taimaki Mamy da aikace aikace ba,
Ke Aunty koda mata gareni a wannan lkc sai nayi sa'a da mai hankalin gaske ne zata kulamin da mahaifiya kamar Samira",
"So tari indai zan shigo da cefane tana gidan sai tayi mana girki zata tafi,
Ahaka randa na samo dadan yawa ina mata alheri wlh yarinyar nan inyi juyin duniya da ita ba zata amsa ba,
Wani lokaci idan na kawo cefane babu wani abun, ba zata fadamun ba, sedai taje gidansu ta samo ta mana girkin.
Anty nasha zuwa dakina in tadda Samira tayi min lafiyayyan abinci, saita fakaici idona ta kawo ta aje ta gudu sai dai in gani inyi dariya,
Nidai bantaba furta mata so ba, ammafa ina jinta araina dan gaskiya Samira akwai halin kirki tin dana auri yarinyar nan bata taba musguna min ba,Kai ko haushi na bata dana fita kafin in dawo ta manta, duk tsohon cikin nan nata ba yanda za ayi in shigo bata yunkura ta tashi ta tareni ba,
Kuma in zan kai shabiyu awaje ba zatai bacci ba sai taga dawowa ta, agaskiya Samira ta mori hali shiyasa duk abunda zan mata ko iyayenta bana kyashi dan gaskiya sun iya haihuwa"Yana kaiwa nan.
Hudah ta kece da dariya tana cewa,"Lallai Huzaifa har yanzu giyan so baigama sakin ka ba,
Wannan irin maganganu bako kunya kamar fitar tusa,Babu shakka munsan ana kai maka geji dole ka fadi an iya haihuwa.
Rufe fuska Huzaifah yayi yana dariya a kunyace yace.
"Kai Aunty bafa haka nake nufi ba, kawai halinta nake fada"
Usman yace "rabu da autyn nan taka itama jan magana ne."Allah dai yasa ka rike amana, dan wlh ku maza halin ku saiku" Hudah ta fada, can idonta ya sauka kan Khaleefa dake sukuwa a kafar Mamy kaman sun Dade da sabawa, taisairin cewa,
"Kaleefah bari mana karka karya min uwa"
Huzaifa yace,
"Aunty wai ya sunan dan namu ne?""Sunan Abba nasa" Hudah ta bashi amsa,
Mamy tace "iye kice megida ya dawo kenan"
"Ai dama nayi tunanin haka, tinda na ji kina kaleefa, ammafa banso kika rigani ba"
Huzaifah ya fada cikin raha,"Bakomai dan uwa kasa abunka ai basu yawa Allah dai ya sauketa lfy"
Duk aka amsa da Ameen.Daga nan Hudah fara basu story, ta nuna Usman nata cewa,
"Mamy kinga wanan bawan Allan shine mukaiyi karo dashi a tafiyar danayi zuwa Katsina nida Abdallah, alkcn nice na daki motarsa kuma na tsaya ina masa rashin kunya, dake lkcn bansan duniya ba ina dai zaune cikinta"
"In har nace zan baku tahirin qalubalen dana gani sanadin barin gida da nayi tabba zamu kwana mu yini ba'a kai ko ina ba"
" Duk hanyar dazan samu abinci ita nake bi, saidai na yashe namiji a shafin rayuwa ta,

ANDA SEDANG MEMBACA
*HUDAH 'YAR KARYA....*
Romantika*HUDA YAR KARYA* _Labarine akan wata yarinya mai suna huda wadda ta dauki karyan dunia ta daurawa kanta alhalin ita ba yar kowa ba_. _Matashiyar yarinya ce mai tsabagen San karya da San gayu da shiga ta alfarma dansan abun dunia, Wanda kallo daya za...