*HUDAH Y'AR KARYA..* 31-40

2K 181 7
                                        

☁️☁️☁☁☁☁☁☁☁️☀
🐔 _*(HUDAH Y'AR KARYA....💁🏼)*_
         🐤🐤🐤🐤🐤🐤🐤
  🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🐛

_Written By *ASY KHALEEL...✍🏻*_

         Wattpad@asykhaleel
           Facebook Group
        Asy khaleel Novel's grp
             IG @asykhaleel

                  3️⃣1️⃣-4️⃣0️⃣

    Duk wani dan abunda Hudah  tasamu a wajan aikinta iyakacin ta sanar da  Mamy ta fatar baki, amma ko ganinsu bata bari tayi, gabaki daya a kayan kwalliya suke tafiya bama  isarta suke ba, dayake ba ko wani lokaci Munirah take basu kudi ba, ahaka har tacike 4yrs tana koyon aiki, wanda a iya ka'idan plazan lokacin ne take yaye rayan aikinta indai sun cike shekaru hudu (4years,) a lokacin ne Hudah   ta matsa wa Aunty Munirah da maganar yaa kamata itama ta sallameta, ga abokan aikinta wa'inda tama rigasu zuwa duk tayi masu  freedom, sedai Munirah tace Hudallah ki kara hakuri ina sane dake,
Sosai take tunanin rabuwa da Hudah don tana amfanuwa da ita ba kadan ba, awannan lkcn yawancin customers  dinsu duk kawayan Hudah ne,  gashi a dokan plazan yaran aikinta basu da daman cin gashin kansu agaban ta, dole komin iyawanka  ka  jira har tayi maka freedom,
Duk aikin da aka kawo nata ne koda kuwa ta hanyar Ka aikin ya samu, sedai ta kanta idan tai ra'ayi takan dan sammasu na kashewa, 

      Hudallah tayi sabo da 'ya'yan masu kudi sosai a plazan Munirah,  duk yarinyar dataga alamun tana wankuwa dakyau Hudah batajin kunyar  cewa ta bata number dinta tana santa da kawa, a nanne suka hadu da classic Feedoh inda suka kullah abota mai ban sha'awa wanda har yayi sanadin kulluwan zumunta a tsakanin iyayen su,

       Classic Feedoh
'Ya ce ga Alhj Lawal, babban ma'aikaci ne a gwamnati, suna zaune a Malali Lowcost Kaduna, Alhj Lawal mutum ne mai tausayin nakasa dashi ko kadan abun hannun shi be rufe masa idoba, hakama matarsa Hajiya Hafsat, mace ce maison jama'a suna kyautatawa makusantan su, ganin shakuwar dake tsakanin 'yar su da Hudah yasa Momi ta aje lokaci ita da yaranta suka kaiwa Mamy ziyara.
Tin da Dad din Feedoh ya gane Hudah marainiya ce yake temaka masu har yakai ga sunzama tamkar yan uwa, lokaci lokaci Mamy takanje gaishesu daganan tayi gdy bisa kokarin da Dad keyi dasu,

Tsakanin Hudah da Feedoh Shakuwa ce maiban sha'awa, duk weekend suna tare da juna,  in suka hadu basa kaunar abun dazai kawo rabuwansu, tahaka dai kawancen nasu ya sami asali, sedai kuma kash.
       An samu banbancin hali a tsakanin wa'innan amienai,  kasancewar ita Firdausi tana maraba da duk wani wanda ya furta mata Kalmar so, sam babu ruwanta da kallon na wuce da ajin wance, mai kudi ko talaka duk abu daya ta daukesu, shiyasa ma  Hudah batasha wuya ba wajan kulla abota da Classis Feedoh. Feedoh ta fara  karantar halaiyar Hudah ne ganin yanda take nuna halin ko in kula ga samari, ko alama Hudah  bata sauraron masoyanta, inba dai ta gyalla ido ta hango abun data hango ba atare dakai, wato kudi,
(masu gidan rana)
Wani lkc takanji haushin Feedoh  in taga tana amsa sallamar samarin dake tsayar dasu  suna akan hanya, acewar Hudah wannan ai  zubar masu da aji takeyi, haba tarasa  wa'inda zata tsaya dasu sai wa'innan kananan qwarin,  girgiza kai Feedoh tayi hade da murmusawa  tace my Hudancy kenan matar manya,
Allah dai yanuna mani auranki lfy, harna hangoki hakimce a gidan mulki, dariya sukayi tare da bama junansu hannu.
Sosai Feedoh tazage dan ganin ta fashintar da kawarta hakan bedace da ita ba, ai baka yawaita burin duniya aranka bakasan ya rayuwa zata zo maka ba, Hudah sedai ta amsa  da toh naji Hajiyata, haka suke gudanar da lamuran su babu maijin tsakaninsu, sedai dazaran Hudah ta kauce Feedoh tana kokarin dawo da ita hanya, ammafa  ko kadan Hudah bata canja ra'ayinta ba, kusan  duk wasu friends din Feedoh masuji dakansu sunyi sabo da Hudah, dazaran wani hidima ya samu kaman biki ko birthday party  sai sun gayyaci Hudah  don tana matukar burgesu, acewar su yarinyar tayine tako wani fanni, gata dakyau ga iya dressing uwa uba tsabar iya takunta da jan class don  indai ba wanda yasan asalinta ba, ba wanda zaiyi zaton, wai Hudah ba yar wani mai fada aji bane a cikin garin kaduna,

*Sai kinyi Hudah yar karya👍🏻😛*

****

(Munirah tailoring shop)

Seda Hudallah
tayi 5years cikakku  sannan Munirah tayi mata  Freedom, inda ta hadata da shatara na arziki, don ita kanta Hudah tayi mamakin Aunty Munirah,  sam batayi zaton zata mata adalci haka ba, a iya sanin Hudah  Munirah tayi kokarin gaskene ta hadaka da karamin sewing machine, scission, da  dai dan kayayyakin aiki masu saukin kudi,
Saiga Hudah da babban keke na wuta sabo fitikil, generator sabo dal da duk wani abunda tasan tailor yana bukata sai data hadama Hudah, aifa Hudah duniya sabuwa.

Hargida customers suke biyo Hudah da dinkuna, haka idan biki ya taso  kawayanta suna mata hanyar samun aiki sosai, irin gown din amare da sauransu, shiyasa kullum tana cikin dinkin anko, masha Allah kudi Hudah take samu bana wasaba dan bata dinkin kasa da 5k, sedaifa data samu zata shiga  market ta fatattako siyayyah, dik bikin da aka gayyaceta sai tayi anko, kuma komai set take hadawa, irinsu takalmi jaka mayafi su abun wuya komai to Match take hadawa ta yanda babu taron da zata shiga a raina mata,
  Haka dai rayuwan Hudah yacigaba da tafiya masoya kam gasunan sunmata chaah, sedai anyi rashin sa'a ba irinsu Hudah ta tsara a rayuwanta ba, tadai yarda yau  taci kudin wannan garan gobe ta wankin sha-aha-sha,
Kullum ita kenan tana wajan biki ko party, kai da abu yai abu  Hudah sai ta aje ashobi  amatsayin kauyanci, ayanzu  tsarin datake  kai shine,
Duk wani bikin daya taso  tayi cancel din   anko a tsarinta,
Haka kuwa tana kallo abokan karyan nata zasuyi ta buga-buga kowacce hankalinta baya kwanciya sai tayi anko,
Hudah sedai ta lafe da aiki yaimata yawa batada time din shiga kasuwa,
    Sharewa dasu take sai ta kammala duka dinkunan mutanen data amsa, inta dai-daici ta cika jakarta taf da kudi, sai irin ana saura 2days afara events sa'annan zata shiga kasuwa,
Idan an fitar da  atamfar 5k ne  Hudah inta tashi na 10k take saya, haka in material sukayi ita saita  sayi babban wanda aka fitar, sannan ta tsara masa dinki, maganar  high hill,  bag, costume, abun wuuuuuh,
    Haka take fasawa cikin tsararrakinta tamkar gimbiya da kuyangunta, a wani taron ma Hudah takanfi amaryan  hadewa  hakan yasa yan mata suka fara tsanarta, shine silar  lakabin da suke mata da.
    *HUDAH 'YAR KARYA*

Tin suna fada abayan idonta harya kai, ga da ga kawayenta ke kiranta da hakan, tayi masifa akan su bari bataso harta gaji ta hakura.
    Ganin abun na Hudah bana hankali bane yasa Mamy tazo mata da shawarar ya kamata tariqa adana wani abun, indata daura da yar nasihanta na cewa,
"Haba Hudallah ya kike mance matsayinki ne, kefa marainiya ce yanzu idan hidiman auranki ya taso wa muke dashi wanda zai tsaya mana?
Nayi nayi dake koda dan adashin nan kishiga kin ki, ace dazarar kin samu kudi sedai ki tafi kasuwa ki kwaso kayayyaki, ke kadai akwatunki uku ciccike da kaya, wasu kayanma kin mance kalarsu kuma kullum kokarin kwaso wasu kikeyi, wannan ai shirme ne gara kodan kayan kitchen ki rika siya kina adanawa watarana zasuyi mana rana"
  Budar bakin Hudah sai cewa tayi, "toh Mamy yanzu so kikeyi in ringa fita tsumma tsumma?
Ko kin manta ance gatan miji yafi gatan gara?
Nidai ki tayani da addua in sami irin mijin da nake so, bama iya kayan kitchen ba har dana bedroom duka da kudinsa za a hada, kinga kuwa  gara in gyara kaina ina fita dagwasgwas kona samo miki maidan maiqo maiqo, koya kikace Mamyta?"
Murmushi Mamy tayi hade da girgiza kai tace, Allah ya nufa, dukda haka adai riqa sara ana duban bakin gatari,

Ayau su Hudah sun tashi da farin cikin kammala secondary school da kawarsu  Feedoh tayi,  kayataccen celebration sukayi anci ansha anyi farin ciki, da yammaci Dady ya damkawa Feedoh dan makullin motor, woww fadar  murna bata baki, wajan Feedoh da kawarta Hudah, qanqame junansu sukayi Hudah tanajin tamkar ita aka baiwa motar tasan dai tasuce su biyu, yanzu kam dole a sake sabon taku💃🏼

Kusan atare suka koyi motor da Hudah dik sanda driver zai fita da Feedoh saita gayyaci kawarta Hudah kafin wani lkc sun iya, yanzu HK babu inda basu fita ba tare da anyi driving nasu ba,

    Bikin kawarsu  Humaida  ne ya taso  Hudah tayi dinkuna har taba uku lada, yayinda ita kuma ta fifita tata shigar, cikin tsadadden material suka halarci taron dinner da aka shirya anan Hamdala hotel  Kaduna.

*_toh masu bibiyata kundaiji cikakken tarihin Hudah, yanzu kuma zamu garzaya Hamdala hotel dan ganin wace wainar ake toyawa._*

*Now shower me with love by voting n commenting* 😍

*HUDAH 'YAR KARYA....*Stories to obsess over. Discover now