☁️☁️☁☁☁☁☁☁☁️☀
🐔 _*(HUDAH Y'AR KARYA....💁🏼)*_
🐤🐤🐤🐤🐤🐤🐤
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🐛_Written By *ASY KHALEEL...✍🏻*_
Wattpad@asykhaleel
Facebook Group
Asy khaleel Novel's grp
IG @asykhaleel4️⃣4️⃣
Tinda Asy ta fara magana Hudah ta zama kamar status, dai-dai da ga6ar jikinta bata iya motsaya duk dan kada afadi wata kalmar da bata jita ba,
Yanda ta tattaro dukkannin nutsuwar ta bana tunanin ko sallah take tana taro hankalin ta haka, ohh ya Allah ka shiryi masu irin wannan hali amin.Itama dariyar ta biye Asy suka dan taba, daga bisani Hudah ce ta dan tsagaita sannan ta daura da cewa,
"Wlh kawata duk abunda kika fada hakane kuma na yarda dake, ina matukar farin cikin haduwata daku, sedai ni ina ganin ba yanda za ayi in zama kamarku, sbd ni iyayena talakawa ne hasalima mahaifina ya dade da rasuwa, suturar ma ni keyi ma kaina abinci kuwa sai Mamy tayi sana'a take siya mana, kinga ina zanga abunda zan dinga ci har jikina yayi irin naku?
Sannan ni a tsarina ina kyamar yin bleaching sam banason kurajen nan irin na masuyin bleaching , kinga ba wai kauyanci ne ya hanani zama irin ku ba, kawai rashin wadatane dan haka cute tayi koskuran kirana villager"Dariya Asy ta sake yi sannan ta ce,
"Ba kinga halin kauyancin naki ba, ana kaiki kina qin zuwa, ance miki ke bakauya ce kinqi yarda, to bari kiji har yanzu kanki a duhu yake, mudin da kike ganin mu wasune kinga matsayin mu ne?
Kinsan sirrin mu ne?
Maybe ma kin fimu wani abun, duk yanda kike tunani ba haka abin yake ba, kawai idan ka iya takunka dolene adama dakai, waima kina shiga social media kuwa?"
Asy tadan dakata tana sauraron Hudah dake cewa,"Eh na taba bude whatsapp sedai ban Dade ba naga 6ata lkc na zanyi abanza, na rufe shi"
"Ai naga alamun haka da kina harka da mutane a online tabbas da kinfi haka sanin wasu abubuwan, amma karkiji komai ki koma online zamu hadu soon, zan hadaki da classic ladies fitattun matan da suka amsa suna mata,
Sannan ya dace kisan bawai yawan tara sutura kadai shike futo da yarinya ba no, wani lkcn tara kayan beda wani amfani idan kika lura babu wacce takeso aganta da kaya yau in wani hidimar ya taso a sake ganin ta dashi, kokari ko wacce take yazamana kullum kalar shigarta daban, ko ba haka ba kawata?Ajiyar zuciya Hudah ta sauke ta ce,
"Hakane wlh don ni kaina wasu kayan nawa har mantawa dasu nake, atsarina indai nayiwa kaya sawa biyu zuwa ukku wlh sun suremin sedai inta ajiya"
"Toh kin gani ashedai kin gane abunda nake nufi, shin waima da kike fadin baki da abunda zaki gyara jikin ki, ina kike samun na dinki ko kina nufin wani keyi miki ne,
Naga dai akalla dressing dinki na yau abeja kudi ba ya lashe sama da 25k kai zema iya fin haka yanda kika hada komai to match ina kika samo kudin?"Wlh ni nakeyi kin san inada sana'ar hannu, babu kalar dinkin mata wanda banayi, yawancin ankon bikin nan duk ni na dinka su, toh matsalar dayace dazaran kudin sun shigomin kaf a kaya nake narkar dasu, don ni gskia Allah ya sani banason aganni cikin qasqantacciyar shiga"
Sosai Asy ta jinjina mata sannan ta ce,
"Ke ashema kina da sana'a mai kawo kudi, to bari kiji abunda baki sani ba, wannan dressing din ba irin ta zakiyi ba a yanzu,
Zaki daina saka atamfar kasa da 20k
Zaki daura lace harna sama da 50k
Zaki saka material komai tsadarsa
Zaki saka voyel, shadda irin ta yayan manya,
Zakiyi shigar larabawa, turawa, indiyawa inyamurai yarbawa, ke in takaice miki har mota Zaki shiga kisha sha'anin ki da ita irin na Wa'inda suka isa, kuma duka a kudin da basu taka kara sun karya ba,
Amma abin sirrine sai mun hadu zan sanar dake yanda tsarin yake,
Yanzu abunda nakeso dake duk wasu kudin da zasu shigo miki, ki dage da gyara jikin ki ya zama boobs naki sunyi duma duma hips naki ya fito sosai abubuwan zaman nan suyi tandama tandama ga fadi ga tsini, ya zamto ko wani juyi in kika yi suna fadin ya kagani?
Fatar jikin ki tazamo lugui lugui kamar ta yaran goye, and ya zama dole ki shafa mai yanda zaki dan haska duk da kedin farar ce amma ance in kana da kyau to ka kara da wanka, maganar quraje, wannan kananan mai kike magana, ya za ayi in cire 5k in sayi mai ko sabulun wanka qwaya daya jal a 5k koma sama da haka, sannan ya sani kuraje ai kuwa da anyi bura uba dani don wlh saina mayar an biyani kudina,
So yanzu dai kinji abunda nace akwai kayayyakin tado da breast na Muslim in kina kyamar na bature, in kin shirya sai ki nemeni zan hadu miki Wanda zasu dace dake,
Zan sanar dake abubuwan da zakina chi Wanda zasu temaka wajan gyarar fatar jikinki acikin sauki,
Ina ganin anan zan dakata don bacci nakeji dear, ga kuma wayata naji ta fara bara zanar kamawa da wuta, don tadauki zafi sosai, akwai sauran bayanai dole sai gani gaki abun zetafi yanda akeso, sedai na jiki my Hudancy!."Tirqashi"
Hudah ta furta, sanan ta numfasa ta cigaba da cewa,
"Laillai fa masu iya magana sukace wani wan wani wani ko baban wani ne, ai dole ma in nemoki my Asy star Asy my mentor my lovely Asy. Dole in gano inda kike a gobe gobe kodan inji wa'innan surruka, insha Allah kuwa zaki ganni tin safe,
Sannan zan taho da10k, ko zasu isa afara kafin in karasa wasu dinkuna,?Heheheee Asy ta buga shewa jin an anbaci kudi, tasan ko banza zata yagi rabonta, ta amsa da
"Eh to sedai adan fara gyaran breast kinsan mayuka suna tsada, zamu fara da boobs nd hips, sai kuma fruit din da zakina ci b 4 kudin su shigo, dear saina jiki byee,Kit Asy ta katse kiran don kadama Hudah ta sake tsareta da wani maganar, rabonda tayi doguwar hira haka ko ita ta manta,
Dogon miqa tayi hade dayin salati ga manzon tsira, jijjiga hannunta tayi alamun gajiya ta ce,
"Wannnan yarinya duk ta wahalar dani, amma ba komai ta kawo 10k din ko banza zanci 3k don ba a banza zanyi wannan dogon bayanan ba dan uwarta.
*Oya shower me with love by voting n commenting endless if this chapter really made u feel something*
![](https://img.wattpad.com/cover/147102640-288-k260650.jpg)
YOU ARE READING
*HUDAH 'YAR KARYA....*
Romance*HUDA YAR KARYA* _Labarine akan wata yarinya mai suna huda wadda ta dauki karyan dunia ta daurawa kanta alhalin ita ba yar kowa ba_. _Matashiyar yarinya ce mai tsabagen San karya da San gayu da shiga ta alfarma dansan abun dunia, Wanda kallo daya za...