☁️☁️☁☁☁☁☁☁☁️☀
🐔 _*(HUDAH Y'AR KARYA....💁🏼)*_
🐤🐤🐤🐤🐤🐤🐤
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🐛_Written By *ASY KHALEEL...✍🏻*_
Wattpad@asykhaleel
Facebook Group
Asy khaleel Novel's grp
IG @asykhaleel5️⃣7️⃣
Misalin shadaya 11:am, Hudah ta gama shirinta cikin skirt da riga na material, dinkin ya kama jikinta sosai ya fitar da duk wani tudu da kwari na jikinta, farar after dress ta daura asama wanda ta kasance shara shara, don zamu iya cewa, kadan ta daranma babu, sosai ake hango kayan dake jikin ta sedaifa rigar iyakace a wanjan kyau, ga wanda yasan darajansu dole a jinjinawa Hudah dan ba karamar abaya bace, tasha adon stones sai zuba qyalli take, sa'annan tayi rolling dan siririn mayafin, high hill tasaka wanda ya kasance fari tare da jakarsa itama white colour agaskia tayi kyau ainun, tana shirin fita kiransa ya sake shigowa, don yayi kusan 30mins awaje yana jiranta, dasauri ta isa gaban Mamy dake gyara gadan miya a tsakar gida, tace
"Mamy muntafi saimun dawo" tsayar da ita Mamy tayi da cewa,
"Ahaka zaki fita da saurayi dan rashin hankali?
To maza koma ki saka mayafin kirki""Kai Mamy amota zamu ba tafiyar kasa bace wama zai ganni, tana fadan haka ta fice da gudu Mamy na mgn bata saurare ta ba,
"Allah ka shirya mana"
Abinda Mamy ta furta kenan ta maida hankali ga aikin ta.Cikin takunta mai cike da salo ta bude gaban motar ta shiga tare dayin sallama, tin kafin ta qaraso Abdallah ya rikice ko sallamar bai iya amsawa ba, ganin shigar dake jikinta da kuma sihirtaccen kamshin da take fitarwa su suka nasa rufdugu saka sashi cikin wani irin yanayi mai wuyar musultawa.
Izuwa yanzu duk wani dauriyarsa ya kusa zuwa karshe, sha'awarta ke nenan zautar dashi gashi ya rasa ta yanda zaiyi ya samu damar cika burinsa akanta,
Hudah ta saki murmushin qeta, sasai ta gane yana cikin tsaka mai wuya ne, amma ta fuske, ahankali tadan daki gefan seat din da yake zaune ta ce,
" Malam In fa kasan bacci kakeji sai in koma gida dan bazan yarda ka jani kana magagi ba, salan ka hurgani a rami karage min sadaki"
Idansa ya bude dasuka canja launi suna hada ido cikin kissa tayi masa fari da ido. Abdallah yayi qwafa yana murmushi alamun zaki sani ne, batasan sanda wata siririyar daria ta kufce mata ba, sai kuma ta maida hankalinta ga wayarta. Shima baiyi gangancin koda ya janta da hira ba ya tada motar sukabar Unguwan, tabbas a yanda yakeji a wannan lkc koda kallonta ya cika yi *ABUN DA AKE GUDU ZAI FARU,* gashi beshiryawa abin ba, dole yasama ranshi salama gudun kada ya bata plan dinsa.
Direct gidan antinsa dake governor road ya nufa da ita , dake ya sanar da aunty Jamila zai kawo mata budurwan sa, tinsafe ta gama shirin tarban surukan tata, hakan yasa tanajin horn tagane bakuwarta ta iso, da gudu gudu tafito harabar gidan dai-dai Hudah ta fito daga motar, da fara'a aunty Jamila taje ta rungumeta, Hudah kam sai rufe ido ake ita adole tanajin kunya.
"Aunty zan danje wani guri yanzu zandawo plz ki kulamin da my heart"
Yanda yyi maganar da muryan da bata sansa da ita ba, shiyasa aunty Jamila saurin waigawa don Hudah kanta sedata kalleshi tai saurin kauda kai, sunayin "4eyes da aunty ta jefeshi da wani mugun kallo yayi mata Alama da ido, irin tayi hakuri i karta badashi gaban Babynsa, motarsa ya fada dasauri yana sosai kai, cikin zafin nama ya tada yabar gidan.
Aunty ta rike hannun Hudah sukayi cikin gidan, iyakar karamci Hudah ta gani awajan aunty Jamila, tana ta janta da hira, aranta jitake inama Dad dinsu wanine ya aurawa Abdallah yarinyar nan da kuwa yayi mata ta nunawa sa'a, sedai inaaa..Waye Abdallah?
Ku kasance tareda ni danjin takaitaccen lbrn sa.
*KING ASY KHALEEL...* ✨

STAI LEGGENDO
*HUDAH 'YAR KARYA....*
Storie d'amore*HUDA YAR KARYA* _Labarine akan wata yarinya mai suna huda wadda ta dauki karyan dunia ta daurawa kanta alhalin ita ba yar kowa ba_. _Matashiyar yarinya ce mai tsabagen San karya da San gayu da shiga ta alfarma dansan abun dunia, Wanda kallo daya za...