☁☁☁☁☁☁☁☁☁☀
🐔 _*(HUDAH Y'AR KARYA....💁🏼)*_
🐤🐤🐤🐤🐤🐤🐤
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🐛_Written By *ASY KHALEEL...✍🏻*_
Wattpad@asykhaleel
Facebook Group
Asy khaleel Novel's grp
IG @asykhaleel5⃣9⃣
Sai bayan sallar azahar Abdallah ya dawo gidan aunty Jameela, cike da annushwa ya shigo harya sauya shiga cikin wata farar shadda da bakar dara sai bakin takalmi, sosai dressing din ya amshi jikinsa ya fito kamar wani limami, suna hada ido da Hudah ta watsamai harara, dasauri ya karasa gareta yana daga mata girar ido, cikin mintuna kadan saigata tana dariya, dake Abdallah ya iya tattalin mace komin fushinki yanzu zai sakaki farin ciki.
Sunjima suna hira da aunty sai bayan sallar la'asar sukai mata sallama, anan ta cika Hudah da tsaraba kala kala, har mota ta rakasu, sannan ta maida dubanta ga dan uwanta ta ce .
"Inasan ganinka da dare akwai maganar da zamuyi,
Abdallah ya saki murmushi dan yasan mgnn bazai wuce..
Saida ya shiga kasuwa ya jibgar masu kayan abinci kala Kala, Hudah kam 6angaran fruits tafi karfi anan ta shiga dibar iya wanda tafiso,Bayan yasa an shigar masu da kayan abincin, dakansa ya shiga cikin gida ya sanar da Mamy bukatarsa nasan ya turo magabatan shi dan har yanzu Hudah taki bashi dama, Mamy abin nema ya samo take ta bashi dama tareda sanyama abin albarka,
Godiya yayi sosai ya tashi yana mai matukar farin ciki ya fita waje danya jira sarauniyar tashi ta fito suyi sallama, a6angaran
Hudah samum zuciyarta tayi cikin kunci, sam bataji dadin hakan da yayi mata ba, ta rasa dalili ko kadan bata kaunar yayi mata maganar ya turo magabansa da sunan zasu zo neman auranta, aranta dai nata matukar san kasancewan su ma'aurata sedai da zatar yai mata mgnr sai kuma taji bata bukata, ko miye dalilin haka??
Ganin batada niyar fitowa ya daga waya ya kirata yana maiyi mata kirari,
don yasan yau akwai rigima, fitowa tayi tana kumbura baki, cikin qwarewa Abdallah ya fara lallashin ta da kalamai masu dadi ya kuma bayyana mata cewa.
Shi mutum ne mabukacin mace ba kadan ba, ya daura da cewa,
"Sannan bana so wani abu ya shiga tsakani na dake batare da kin zama halaliyata ba, Hudallah a duk lkcn da nake tare dake ina shiga wani hali wanda ba lallai ki gane hakan ba please ki bani dama in mallakeki, don bazan iya cigaba da kallonki in zauna lafiya ba, ko kina so in fara aikata sabon Allah ina bin Matan banza? Haka ya dabaibayeta da kalamai masu dadi sai gata tana murmushi, sosai takejin sonshi yana kara jiga kowani ga6a da jijiya na jikinta, ta tsareshi da fararen idanunta tana masa wani irin kallo mai dauke da sakannin kauna kala kala, yayinda shima yake gwada mata nashi salon atare suka saki dariya mai sauti .Abunda bata sani ba shine, Sawad yayi kusan 5mins ya tsaye a gefe yana kallon su, Abdallah kadai yaga lkcn daya iso, dagangar yaki mata alama dashi yayi hakan dan ya cusa masa haushi, ji yake kamar ya rungumeta sai yayi tunanin bai horar da ita rematch ba, da rungumeta zeyi agabansa, waiwayawan da zatai sukai 4eyes da Sawad, ita kadai yake kallo idanun sa sunyi jawur zuciyarsa tacika taf da bakin ciki, a lkcn ganin Hudah yayi ta zame mishi kamar kwalta saboda baki, jiki asanyaye ta juya zataje gareshi, Abdallah yai saurin damke hannunta yana mata wani irin kallo, fige hannun tayi tana kokarin kwacewa yasake damke hannun, yaki sakinta, saima janyota da yayi ya jingina ta a gefansa jikinsu na gogan juna ya saqala hannun sa a kafadarta, take jikinta ya fara kyarma, Abdallah kuwa jikinsa harya mace yana neman ya birkice, cikin wata kalar murya yai mata rada a kunni.
"Karkiji komai ginbiyata ni ba masoracin masoyi bane zan iya ja da kowa akanki.. Bekai karshen mgnr ba, yaji an finciketa iya karfi, wani wawan mari Sawad ya watsa mata, cikin matsanancin fushi yake fadin kin cuceni,
Cike da mamaki Hudah ta dafe kunci tana kallon shi, daga bisani ta girgiza kai tana fadin, ni ka mara ko Sawad?
Yau ni ka iya daga hannu ka mara?To wlh bari kaji ka mari soyayyar ka, wai ma da kabi ka takurawa rayuwata har kake kafamin dokar kar in kula kowa sekai kadai, shin kudin aurena ka biya ko ubana ne kai?..
Zata kara mgn ya sake daura mata wani marin. Abdallah baiyi wata wata ba ya daga hannu da nufin rama mata. Caraf sawad ya rike hannun sa yana fadin kaiwaye waye ubanka,? mai ya kawo ka gurinta?
Abdallah yasake dai-daita tsayuwa tare da gyara zaman rigansa ya dube shi yace "abunda ya kawo ka shiya kawoni kuma nafika matsayi nesa ba kusa ba acikin zuciyarta, miye hujjarka nason sanin koni waye ko waye ubana?
Juyawa Hudah tayi zata shige cikin gida Sawad ya daka mata tsawa ba shiri ta waiwayo da himmar taci zarafinsa, ga mamaki taga hawaye ne bibiyu kwance a fuskarsa. Hannu yakai ya share hawayen dake zuba masa yace Hudah na birki kamar yanda nabar nonon uwata, nagode sosai da rike alkawarina da kika yi, sedai ina tabbara miki akwai ranarda zaki gane ni masoyinki ne na hakika, nagode Hudah kincika yar halak, yana kaiwa nan da gudu yabar wajan, kasancewan bada mota yazo ba.
Wani wawan kuka ya kufcewa Hudah Wanda ita kanta batasan namiye ba, Cikin gida tayi aguje Abdallah yana kiranta bata waigo ba, haka shima yabar wajan cike da tunani iri iri aransa. Tindaga lkcn Sawad baisake shiga shirgin Hudah ba, sosai tadage da aika masa text naban hakuri sedai ko alama beta6a kolata ba, daga karshe itama ta fusata ta watsar dashi har rantsuwa tayi kamar yanda yace ya barta kamar yanda yabar nonon uwansa, to ita sai da ta rantse akan koshine Autan maza ta barshi kaman yanda tabar nonon uwarta, tindaga ranar ta saki jiki da Abdallah suka cigaba da soyayyansu daga karshe tabashi damar ya turo anemi auranta ga iyayenta..
Cikin satin nan sukaita karade danginta na kusa dik inda sukaje sai yayi masu barin kudi, daga karshe har zamfara wajan dangin ubanta seda sukaje kwanansu daya suka dawo iyayenta da sukace babu ruwansu da su tinda uwarsu bata nuna masu dangi ba, suna ganin mai hannu da shuni sukai naam da mgnr dake an masu barin kudi kamar ba'asan zafin nemansu ba,
Ba bata lkc iyayen Abdallah sukazo neman auren Hudallah inda suka bukaci amasu lissafin kudin komai jin mgn, da kudin sadaki da saka rana haka kuwa akayi, har qari iyayen Abdallah sukayi akan kudin da aka sara masu, nandai aka aje lkcn biki waranni hudu masu zuwa......Idan kuka yawaita comments da Votes zaku samu update ba a dadi..😀
YOU ARE READING
*HUDAH 'YAR KARYA....*
Romance*HUDA YAR KARYA* _Labarine akan wata yarinya mai suna huda wadda ta dauki karyan dunia ta daurawa kanta alhalin ita ba yar kowa ba_. _Matashiyar yarinya ce mai tsabagen San karya da San gayu da shiga ta alfarma dansan abun dunia, Wanda kallo daya za...