☁️☁️☁☁☁☁☁☁☁️☀
🐔 _*(HUDAH Y'AR KARYA....💁🏼)*_
🐤🐤🐤🐤🐤🐤🐤
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🐛_Written By *ASY KHALEEL...✍🏻*_
Wattpad@asykhaleel
Facebook Group
Asy khaleel Novel's grp
IG @asykhaleel4️⃣7️⃣
Cikin takon ta na isa da taqama ta kutsa kai cikin dakin.
Wani mugun kallo tabi Asy dashi batare data furta komai ba,
A6angaran Asy da Hudah ba karamin firgita sukayi ba,
Gaba dayansu numfashi suke saukewa, Asy ce ta iya furta.
"Amma cute kin cucemu, wlh duk nayi zaton Mama ce taji hirar da mukeyi ko kuma yaya Musa, dan walakanci Ashe..Cikin fushi cute ta dakatar da ita da cewa,
"Common yimin shuru, wlh ban tabbatar ke wata sauna bace sai yau, nayi kusan 5 minutes ina knocking dan banzanci bakiji ba kina can kina zuba kamar bishiyar kanya, aganin ki kinyi gwanin ta ne, to wlh ki canja tsari wannan zubar mana da aji kike"
Tana kaiwa nan taja dogon tsaki, afusace tayi gaban wardrobe ta hankade kofar kaman shine yai mata laifin.Asy kam binta da ido tai, ganin tana kokarin 6alle mata murfin wardrobe yasa ta cewa,
Cute wai kanki daya kuwa, sai wani abu kike kamar kinyi tatil, inji dai ba shishan kika shawo min ba?Mugun kallo ta Watso mata sannan ta sake maida hankali ga tufafin dake shirye a ma'adanin su.
Wani yellow mayafi ta janyo wanda yakasance tamkar mahadi ne da super java dake jikin ta,
Linke mayafin wuyarta tayi, sa'annan ta yafa yellow din,
Batare data kalli daya daga cikin su ba, ta juya zatabar dakin.
Asy tayi murmushi tana girgiza kai, ganin fita zatai dagske, tadan kwantar da murya ta kira sunanta,
"salheart"
Chak ta tsaya kamar wacce aka tsayar da remote. sedai bata yi kokarin waiwayowa ba, bare kuma Asy tasa ran amsawar ta,"Ina zakije ne haka?
Shine tambayar da Asy ta jefeta dashi.
Tayi kusan 2mnts kafin ta bude baki ta ce,
"Bamuyi dake zanshiga central market ba?""Ohh hakane fa nadan manta, so kin fito da mota ne, plz dan jirani mana in dan watsa ruwa, inaso ki saukeni tudunwada Mama ta aikeni gidan aunty Hafsa"
Sai a sannan cute ta juyo ta sakarma Asy wata uwar harara, sai kuma taja dogon tsaki tana cewa.
Ajirgin sama nake ba mota ba, dayake bani da aikin yi bari in tsaya jiranki harki gama sokancin ki, tana kaiwa nan ta fice tabar dakin.Dik wannan abunda ake, koda ta wutsiyar ido cute bata kalli inda Hudah take ba, bare tasan anyi tsiranta awajan,
Asy ta danyi dariyar yake, sedai sam bataji dadin abinda cute tama Hudah ba,
Kallon ta tamaida ga Hudanllah, wacce ta qame guri guda tana gallon ikon Allah.
Amemakon taga 6acin rai atare da Hudah, wani abun mamaki murmushi ne kwance bisa sarbadediyar fuskar ta, don ita yarinyar tagama burgeta irin su tafiso arayuwa, aganin ta sune mata masu aji.
"Kawata kiyi hakuri da halin cute miskilancin ta over wlh, ammafa idan yan mutuncin suna kusa sekiga kamar ba ita ba" cewar Asy,
"Laah ni wlh hakan da takeyi naji yarinyar ta kara burgeni sosai she is socialize wlh pls ki bani no inta da address zan gwada sa'ata mugani don tsarin ta yamun, inason miskilin mutum, har gida zanje na same ta nasan ba zataqi sauraro na ba" .Asy ta kadakai tace
"Saikinyi Hudancy, zakuwa kinyi mamakin tarban da zatai miki, salheart tana da mutumci sosai, inhar kikaje gidansu tasan darajan baqi. Amma yanzu tana gidan yayanta bata cika kai kawaye gidan sedai in ta koma gidan Mama,
"Owk itama nan area take?
"no tana kawo ne wani lkc kuma tana gdn yayanta kinsan yarinyar yargatace takarshe, dayake Dad dinsu ya rasu kuma itace Auta, matsalar daya, ko kadan yayunta basa mata da wasa kuma basa cika sakar mata kudi, woww aida munga abu wajan salheart,"
Daria sukayi Hudah tace gata da iya sakawa mutum suna, jiya an kirani yar village, ke kuma yau kin zama sauna lolz"Cikin dariya Asy tace.
"Saima kinga sunayan samari awayar ta zakisha dariya, kowanne da sunan da tayi saving no dinshi, irinsu transper, ashobi, hamago, qanqamo, wayau yasan naqi, ke abun se ita lolx.Ni kuwa nasan dalilin kirana haka,
Shirar data tsinkayo munayi CE bataso, tasan tabbas yau zakiji sirrin mu, zai zamto kamar tsirara kike kallon mu, ni kuwa tinda kika nuna kinason ki qaru da ilmin mu komin fushinta saikin shigo cikin classic ladies, barima muci gaba lkc yana ja kafin Mama ta ji shirun yai yawa,
Mungama da fannin gyaran jiki kinji amfanin fruits kuma karki riqeshi da wasa sai mu koma..._Wani fanni kuma zasu koma? Sekun biyoni, Vote, cmmnt, follow da kuma sharing shine farin cikin ku a gareni_
*KING ASY KHALEEL* ✨
YOU ARE READING
*HUDAH 'YAR KARYA....*
Romance*HUDA YAR KARYA* _Labarine akan wata yarinya mai suna huda wadda ta dauki karyan dunia ta daurawa kanta alhalin ita ba yar kowa ba_. _Matashiyar yarinya ce mai tsabagen San karya da San gayu da shiga ta alfarma dansan abun dunia, Wanda kallo daya za...