☁️☁️☁☁☁☁☁☁☁️☀
🐔 _*(HUDAH Y'AR KARYA....💁🏼)*_
🐤🐤🐤🐤🐤🐤🐤
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🐛_Written By *ASY KHALEEL...✍🏻*_
Wattpad@asykhaleel
Facebook Group
Asy khaleel Novel's grp
IG @asykhaleel5️⃣0️⃣
Tin shigowan Feedoh Hudah ta fahimci akwai damuwa atare da ita, sau biyu tana tambayar ta ko lfy sedai Feedoh ta amsa mata da cewa dai2 nake dear,
Mamy tana jinsu sedai tayi murmushi dayake tin a jiya Momin Feedoh ta sanar da ita abinda ake ciki, tasan ba makawa dolene sai sun shiga yanayin damuwa shiyasa batai hanzarin sanar da Hudah ba,
Hini jingur Feedoh tayi suna tare da Hudah bayan sunyi sallar la'asar ne Feedoh ta dan kwanta gefan gado ta kife kanta a pillow tana tunanin taya zata sanar da qawarta abunda ake ciki,
Hudah ce tashigo tana rike da plate da gurasa a ciki, ganin Feedoh akwance hakan ya kara tabbata mata akwai ayar tambaya a tare da ita sanin cewa duk inda taje dazarar anyi la'asar zaka samu tana hanzarin tafia gida,
Aje plate din gurasar tayi ta karasa bakin gadon ta sake jefo mata tambayar."Wai dan Allah Mi yake faruwa dake ne daerie ?
Banyi zaton akwai wata damuwar ki dahar zaki iya boyemin ba amma babu komai ngd da hakan sedai ina fata Allah ya shigo cikin lamuranki,
Jin kalaman dake fita a bakin Hudah yasata yunkurin tashi zaune, cikin sanyin murya ta furta.
"My Hudallah kenan damuwata ba wata bace face kewarki da zanyi munriga munshaku da junan mu amma ba yanda muka iya haka Allah ya hunkunta"
Cikin rashin fahimta Hudah ta dubeta ta ce."Banfa gane in da zancenki ya dosa ba kimin gwari gwari mai hakan ke nufi?"
Anan Feedoh ta labarta mata abin dake wakana,Kanta Hudah ta dafe takasa furta komai, haka suka kasance ba wani walwala, bama iya su kansu ba, duk wanda yasan shakuwar dake tsakanin su saiya jinjina rabuwan nan tasu.
Ana gobe tashinsu, tin safe Hudah ta isa gidan danufin tadan temaka masu da shirye2.Tuni daman kayan dakin Feedoh kaf Hudah aka baiwa harda wasu kayan sawanta, Momy ma ba'a barta a baya ba, duk wasu kayayyakin aikin gidan Mamy ta barma, wasu kuma ta rabawa maqwaftan su, kwana Hudah tayi agidan, kasancewar jingin safe Dady yasa akai masu booking daman shi tuni yayi gaba kwanansa ukku kenan da tafiya, haka suka kwana suna hira na bankwana tare da baiwa junansu shawarwari ba kamar Feedoh data dage tanama Hudah naseeha.
Acan airport dakyar aka 6an6are Feedoh da Hudah rungume junansu sukai suna kuka duk wanda yake gurin ya tausaya musu, hawaye kwance bisa fuskar Feedoh ta shige tana dagawa Hudah da sauran friends inta hannu, da gudu Hudah ta juya ta rungume Mamynta tana kuka maiban tausayi....
*KING ASY KHALEEL...* ✨
YOU ARE READING
*HUDAH 'YAR KARYA....*
Romance*HUDA YAR KARYA* _Labarine akan wata yarinya mai suna huda wadda ta dauki karyan dunia ta daurawa kanta alhalin ita ba yar kowa ba_. _Matashiyar yarinya ce mai tsabagen San karya da San gayu da shiga ta alfarma dansan abun dunia, Wanda kallo daya za...