Salamu'aliakumIna fatan munyi sallah lafiya?shine babu wacce ta bani goron sallah ko🤔, no wahala zaku sha late update ai😂.
Ga wani dai labarin nan na kawo muku, ina fatan zaku soshi,idan akwai masu son DOCUMENTS na novel dina ayi min mana private.
Wannan kirkirarren labarine bai faru ba, ni na zauna na tsara abuna, idan nayi kuskure Allah ya gafarta min amin.
Bismillahil'rahmanil'rahim
""""""Wannan wacce irin rayuwa ce muke ciki?babu babban ciwo da bakin cikin rayuwa irin fatara da talauci suyi wa mutum atutu!
Dattijuwar matar dake tsugunne a gaban wata tsohowar rijiya ta fada tana buga wani uban tsaki hade da mikewa tana kakkabe zaninta na jar atamfa dayaji jiki duk ya kode yayi fari tas dashi, daga bayanta taji an gwada mata kira, DIJE! DIJE! Tayi saurin juyowa tana kallon mai kiran nata fuskarnan tata a murtuke, a tsiwace tace, wai ke lantana fi sabilillahi ban miki fadan kirana da kike haka ba ! Sai kace wacce ki ke bin tsohon bashi! , lantana dauke da bokiti a ha'barta ta karaso tana fadin, maida wukar dama tambayarki kawai zanyi, dije ta dauke dan ruwanta rabin kwalla jawur dashi tace, ina jinki sarauniyar yan gulma, lantana ta yatsine fuska, dama naji ne wani jite'jite a garin nan, wai mai kudin nan daga cikin burni mai gonaki da gidajen gona, wai yana neman ma'aikata a gidansa duk su jummala da shatu sun nemi shiga wajen malam haru mai gadinsa..
Dije ta tabe baki duk zancen banza ne wannan! Ke banda duhun kanki ina za'ace wai mai kudi kamar wannan da muke jin labarin wai yana cikin jerin layin masu neman shugaban kasa zai zo wannan kuturin kauyen namu yace yana neman ma'aikata! Lantana tace nima dai haka nake ji wallahi, amma fa ance da gaske ne ta karashe maganar tana tufar da yawu, dije ta wanka mata harara ai sai kije ki shiga layin masu asara ni ina ruwana mai na hada dake, lantana ta murgude bakinta, duniya a kauyensu babu wanda take shakka kamar dije, masifaffiyar mata ce ta karshe, auren ta biyar amma gaba daya babu wanda akayi rabuwar arziki da ita, asalima har karya diyar kishiyarta tayi, yanzu haka dai a gidan yayanta take zama ta tsangume matarsa..
""""""Gidane dan karamin gaske,dakuna biyu ne kacal da dan tsakar gida da bazai wuce taku goma ba, sai dakin rumbunsu a gefe, Gidan jar kasane tukuf da rufin kwano, dije na hango dauke da kwallar ruwanta ta shige cikin gidan nan kamar mahaukaciya har da wasu ka'ra ta tsinto a hanya.
A tsakar gida ta dire kwallar tana jefi da ka'rar hannunta sai faman waige waige takeyi,murhu ta hango da tukunyar kasa a kai ta karasa ta bude murfin ,wani irin dogon tsaki taja mai sautin gaske sannan ta fada cikin daki a harzigenta.
Kwance ta tarar da matar yayanta Ammani, yar kimanin shekaru 20,da yar diyarta mai kimanin shekaru uku zaune a kusa da ita, ammanin kuwa sai nishi takeyi da kyal kyal da gani dai tana jin jiki.
Dije ta daka mata tsawa akai har tana harbi da boo din dake bakin kofar, Ammani wai wacce irin jaaka ce ke ne eyyeh! Ya zaki daura ruwa tun dazun bakiyi ko talge ba! Tun kafin na fita debo ruwa fa na bar tukunyar can na tafasa!salon bake ce mai fita nemo itacen ba ko! Ammani tayi kokarin mikewa, wallahi yaya jikin nawa ne babu dadi tun dazun, dije taja tsaki, toh kuma sai mai ! Shikenan dan bakya jin dadi sai mu mutu da yunwa ko mai! Kallah da Allah ji yarda yarinyar nan duk ta fige yau dinnan kawai saboda yunwa tun kokon safe, ta figo yar diyar tana ficewa, maza ki kokarta ki fito ragguwar banza kawai!..
Yau juma'a kuma yau ce kasuwar garin tasu take Ci, dan haka tun bayan sallar juma'a garin ya cakale da jama'a sai tururuwa sukeyi, dije tayi tsaka da tsamin ta ta lafta mai a jikinta tana kallon yar diyar yayanta dake wasa kusa da kayanta, ke! SARATU aa'kul dinki! Yarinyar ta juyo da majina cike da hancinta dije tace Uwaki! Dama kece mai karya min daddawata ko! Yarinyar tayi rau'rau da ido, sallamar Ammani ce ta katse dije daga yiwa SARATU ashar,ta dauke diyarta tana fadin, yaya ki fito lantana na jiranki a tsakar gida, dija tace toh gani nan ta burguza hijabinta da satin ta daya kenan babu wanki ta fice.
Sun bazama cikin kasuwa babu abunda suka siya in ba maula da gulmanmakin jama'a da sukeyi ba,salame ce ta tare su a gaban shagon mai kayan marmari, ah ah yaya dije ce! Dije ta juyo tana washe baki, ja'ira! Wai salame ce ne! Salame ta tuntsire da dariya, yaya nice dai kuwa ai na dawo garin tun shekaran jiya, goggo rabi ta shaida min sakon ki, lantana tace ikon Allah wai salame ce haka? Kinyi fari wallahi, sai tsuke tsuken bakin takeyi, dije tace kedai bari nima naga canji ai daga zuwanki burni? Ta rike baki.
Salame tace ai kinsan na samu aikin gida a can, toh wallahi shidai ne kawai rufin asirin nawa, dije ta ware ido, ke haba! Lantana tace ashe dai aikin nan na birni gaskiya ne? Dije ta yatsine fuska, gobe dai ki shigon da sakona da Allah, salame ta fice tana cewa toh yaya inshaAllahu..
GARIN KANO
Zaune yake tamkar an dasa shi girar idanuwansa kawai ke motsi, yarone saurayi dan kimanin shekaru sha biyar da haihuwa,farine mai kyawun gaske, idanuwansa masu haske da walkiya,macece yar kimanin 30yrs ta shigo falon cikin kayan alfarma tana fadin RIDWAN! Ko motsi bai yi ba balle ya kalleta,taja tsaki, a haka dai zaka karashi rayuwarka cikin kadaici da RASHIN GATA ,ta kalli mai aikin dake kusa da ita,LAMI ki dafa masa abinci kafin ki tafi da Allah, ta wurga masa harara cike da tsananin tsana da kyamata tana jan tsaki ta fice tana fadin, wai har yanzu malam haru bai samo mana yar aikin bane...
'''''''''Dije ta wangale baki tana kallon leshi da atamfar dake gabanta, kee salame duk wannan nawa ne? Salame tace kwarai kuwa mai dakina ce ta bani nima, dije tace lallai kuwa ana samo abun arziki dai a wajen aikin nan na burni, Ammani ta shago goye da saratu a bayanta ta ajiye modar ruwa a gaban salame, salame ta bita da kallo, tana fita ta kalli dije, kada dai kice min yaya inusa sai daya auri wannan Ammani take ko wa?
Dije tace kedai bari kinsan shi da kafiyar tsiya a nan dai ya ka're,gashi ma dai aikin faskaren nashi babu wata samu aciki, ni din nan dai nice dai cinsu da shansu,yar daddawar nan da nakeyi, dije ta buga tagumi, salame ta nisa tace, toh wai ke mai zai hana ki bari taje aikin burnin itama tunda kedai nasan ko wuka aka sa miki a wuya bazaki je burni ba, dije tace Ammanin!!!? Salame tace kwarai kuwa A wata fa har dubu ashirin ake samu, dije ta ware ido ke da Allah😨....salame tace wallahi kuwa, dije ta girgiza kai amma ai kinga mata da yawa sun riga mu samun hanya wajen malam haru, salame tace kyalemin wannan kawai kedai yiwa yaya inusa bayani kawai, dije tace anya wannan kuwa zai yarda? Kinsan shi kamar a kanshi aka fara soyayya, salame tace kada ki damu duk sati zata ringa zuwa juma'a ta koma lahadi, gidan arziki zani kaita ki barmin komai kedai a hannuna, dije taja lumfashi toh nidai na bar miki wuka da nama.
Dare nayi dije ta samu yayanta yana zaune a tsakar daki da kwanon tuwun dawa da miyar kuka a gabansa, ta samu waje ta zauna kamar wata salaha sai yan dube dube takeyi ko Ammani na cikin dakin, ganin bata nan sai saratu dake ta sharar barci a kan taburma.
Inusa ya kalleta yana si'de hannunsa, da gani akwai magana a bakin nan na ki ko? Tayi yar dariyar tana susar kanta, eh toh da ma maganar gaskiya, inusa yasha ruwa ya kurkure bakinsa ya shafe fuskarsa yace ina jinki, dije ta kwashe masa maganar zuwan Ammani burni aiki, ya katse da sauri, dakata dije!
Ya za'ayi matar aure mai mutunci ta tafi har cikin garin kano aikin gida? Dije ta gyara zama, yaya wallahi da samu sosai a aikin nan, gidan mutumci za'a kaita, kuma miye ma nan da kano? Duka fa tafiya minti arba'in ce, kuma duk sati zata dawo taga saratu kaga dai irin halin da muke ciki, saratu dai macece kuma ta'sowa takeyi nan ba da dadewa ba zakaji har anzo neman aurenta, kayi tunani yaya, inusa yace tashi kije zanyi shawara da ita Ammanin, dije ta guntse baki tana wani yatsina, tana kokarin mikewa ne ammani ta shigo dama ta dade a bakin kofa tana jin zancen da suke, zanyi! kawai ta fada kai tsaye, suka kalleta da sauri, ta gyada kai zanje aikin da yaya ke son nayi, inusa ya mike, ya zaki fadi magana bakya taunata eyeh! Ammani tace zanyi mai gida amma da sharadi, ta kalli dije dake ta murna, dije tace fadi! Ammani ta nuna saratu, da sharadin zaku bari fa'iza tayi karatun boko....
Dije ta daure fuska, keeh! Ammani ya zaki kawo wannan maganar da ta dade da wucewa, nasha fada miki mu a zuri'ar mu babu wanda yayi karatun bokon nan dan haka sai dai ki sake wani sharadin naki amma ba wannan ba....ehe!!
Vote and comments 🙂
Follow me on instagram @ dee_bature
Bazaku ringa samun update akan time ba so manage

ВЫ ЧИТАЕТЕ
Rashin Ga'ta
Художественная прозаRashin gaa'ta is a hausa written story, follow and vote