'A hankali ta shiga bude idonta da sukayi mata nauyi, wani irin tsami jikinta yakeyi mata,ammani dake rike da hannunta tayi saurin kallonta, Saratu kin tashi? Ya jikin naki?
A firgice ta rungume ammani tana rusa kuka mai tsuma rai, dije ta shigo dakin cikin saurinta take fadin, ai sai dana fada muku, duk kune sanadi,n abunda ya faru yanzu Allah ya isa!
Inusa yaja lumfashi, bai taba zaton cin mutumcin zai kai haka ba.
Ammani kanta a daure tace, wai maike faruwa ne? Hawaye sun cika mata ido.
Inusa yace, wlh ban taba zaton duk rashin mutumcin da kaura(baban jibrila) ke cewa zai mana zai kai ga haka ba, sunsha samu na a cikin daji suna min kashedi, wai ba'a karya alkawari dasu ba'a ci musu mutumci su kyele mutum, ya kalli dije, wane kwadayin ne yasa ki amsar kudinsu uhm, wa ya baki ikon yi musu alkawarin zaki basu saratu.!Dije ta buga tagumi, ni kaina ban taba zaton walakantattu bane su sai yau, yanzu kamar ni zasu je suyi ta bazawa a gari, yanzu ji abunda wannan shamsun banzan yayi wa saratu..
Ammani ta dago saratu, mai ya hada ki dasu, ba kin min alkawarin karatu zakiyi ba?
Saratu na kuka tace, wlh inna ni bana tanka musu, kawai naje rakiyar hafiza ne muka hadu dasu a ahanya, sukayi ta kirana naki na amsa su,jibrila ya gaji yayi hanyarsa, ashe wai shamsu na biye dani a baya ban sani ba, sai da mukazo lungun su garba me shayi ne ya shaga gabana yana zagi na, ta fashe da kuka, ni kuma na rama shine ya dunka dukana da sandar kiwonsa da kyal nasha...Ammani kamar zatayi kukan itama, tana tausayawa diyarta sosai.
Dije tace, yanzu fa bamu da wata mafita in ba aurar da saratu mukayi ba, dan kuwa haka zamu ringa shan wulakanci daga garesu..Inusa ya kalli ammani, kwarai kuwa, dan kuwa da su ringa cin mutumcin saratu haka gwara ace auren tayi tabar garin gaba daya.
Ammani ta mike batace komai ba ta fice daga dakin.'Washe gari saratu baki harya kumbura, tana nan kwance ammani ta shigo da abincinta, ta zauna tana fadin, tashi kici abinci kisha magani.
Ta mike da kyal, ammani na bata a baki harta koshi, tasha maganinta, saratu ta kalli innarta, komai ta yanke shawara oho? , ammani ta mika mata ledar maganin, ki ringa sha kinji, yau zan koma nima, amma ina nan dawowa sati mai zuwa, saratu ta gyada kai.
Ammani na dawowa ridwan ya tareta, suna kallo da ikram ne a falo, yace welcome Mom, tace yauwa yallabai, ikram tace nanny ammani sannu da dawowa, tace yauwa ikram ta kalli ridwan duk ya rame kwana biyu kawai.
Sai da dadddare ta samu zama dashi, cikin eagerness yace, mom ina fatan kin dawo min da good news ko?
Ammani tadanyi shiru, yace please mom talk to me.Tace yallabai, ban taba sanar dakai komai akan family dina ba ko? , ya gyada kai, na fahimci kamar bakya so ne.
Tace hakane, ina da diya yar shekara sha bakwai, zaka iya aurenta?Sai da gaban Ridwan ya fadi, hakanan ya tsinci kansa da gyada mata kai bai shirya ba.
Ammani tace, toh kada ka damu, na baka yar tawa halak malak, ta shafa kansa, Allah yayi maka albarka sannan ta fice.Ridwan ya dafa kan bed dinsa, tunani yakeyi, anya zai iya rayuwa da yarinya karama haka? She's too small tobe married off mana, yaja lumfashi, well baya da wani solution yanzu he have too.
Alhaji karibu ya sake samun su da mgnr, kan cewa sati fa ya cika, ammani tayi masa bayanin komai, sai daya dauki lokaci sannan ya kalli ridwan, kai ka amince da hakan?
Ridwan yace yes daddy, ammani tace, amma inaso dan Allah yallabai ka cika min burina, ka bari tayi karatu mai zurfi, ridwan yace inshaAllahu Mom kada ki damu, tace sannan kuma inso bayan anyi auren nan ni zan bar aikina....!
Da sauri ridwan ya mike, haba Mom! Ammani tace kada ka damu yallabai, my daughter will also support u, she will be with you like your shadow ..
Da kyal Ridwan ya amince da quitting aikin da ammani zatayi, alhaji yace da ammani, zai kira kaninsa dake kaduna, idan yazo zasuje har kauyen a daura aure, yanaso hakan ya zama sirri ne a tsakanin su, so yake nan da sati biyu a kammala komai, sai dai kawai hajiya layla taji labari daga baya.

STAI LEGGENDO
Rashin Ga'ta
Narrativa generaleRashin gaa'ta is a hausa written story, follow and vote