Chapter 12

2.6K 196 3
                                        

'Wani irin shock ne ya mamaye musu gaba daya jikinsu, saratu tayi saurin mikewa tana sake gyara daurin towel dinta cike da kunya, Ridwa ya mike shima cikin kunyar yace, am sorry na baki tsoro ko?
Saratu tace, shine na gani ai baka ko kwankwasa ba, yanzu gashi ka jawo mana faduwa..
Ridwan yadan rike bayansa,yace mom ce ke son magana dake, saratu ta kallesa, Mom wace wanann?
Ridwan yayi murmushi innarki toh, ta yatsine fuska wato ma har kiranta yake da Mom dinsa ko..
Ya saka kiran sannan ya mika mata wayar ya fice.
Saratu ta fashe wa ammani da kuka, wai ita ba'ayi mata adalci ba, wato dan tafi son shi akanta ko? Dije ce ta amshe wayar daga hannun ammani dake shirin yin kukan itama, tace ja'ira ke da zakiyi mana godiya ma mun kai wannan aljannar duniyar! Saratu ta turo baki, ni bana so, dije tace ke bani son sakarcin banza, wato bukulu zakiyi min ko? Toh baki isa ba, ke din ma da ko kwatan kyansa baki kai ba, yaro kyakkyawa dashi kamar jinsin larabawa, saratu dai takaici ya ishe ta, dije sai wani ya'ba ridwan takeyi, ta ajiye wayar karkashin pillow kawai taci gaba da kukanta, a haka har barci ya dauketa...

Ridwan yaji shiru shiru bata maido nasa wayarsa ba, ya kwanta yana jan lumfashi the girl is so childish, yayi addu'a shima ya kwanta.

Washe gari da safe baya da aiki dan haka bai tashi da wuri ba, saratu kuwa bayan tayi sallah ta koma barcin ta, taji wani irin kara ta cika mata kunne, ta mike da sauri tana jan tsaki, miye haka ne? Taji ringing din ya katse, ta koma ta kwanta, ai kuwa sai gashi an sake karade mata kunne da ringing din, cike da haushi ta mike tana daga pillow dinta, sai ga IPhone din Ridwan.
Taja tsaki, ashe wannan wayar ce, ta dauki wayar tana jin haushin tashin ta da akayi, Amal ta gani a jikin screen din har da kuma picture, ta tabe baki ganin kyakkyawar budurwar data sha gayu da make-up, ita kuma wannan ko wacece?
Ina ruwana ma toh, tayi waje dan kai masa kayansa.
Ridwan kuwa yana ta shan barcinsa dan dama aiki baya barinsa samun ishashshen hutu..
Saratu kawai ta fado dakin tana cewa,ga wayarka ana ta faman kira...
Tsaye tayi tana hangosa kan bed, barcin yake ya rungume pillow, ta shiga san'do har ta karasa gaban gadon, ta kura masa ido, hes sleeping soundly kamar wani yaro karami.
Ta ajiye wayar a kusa da pillow sa, tana kokarin mikewa se kuma ta sake zama, ta shiga kare masa kallo, komai nasa me kyau ne, gani tayi yana motsa lips dinsa, saratu uwar gulma, ai kuwa ta kara kai fuskarta kusa da tasa, tana kasa kunne taji me yake fada..
Kwatsam sai ringing din wayar ya sake shigowa...
A firgice duk ta rikice ganin yana kokarin bude idonsa..
Bata ankara ba taga ya bude ido tangaren.. Sukayi ido hudu..
Ridwan cike da tsananin mamakin ganunta ya yayi kokarin mikewa..
Gani yayi tana kokarin guduwa..
Yasa hannu ya riko ta, ai kuwa dama batayi balance ba sai ta fado kan gadon.
Ya wani kura mata ido, mai kika zo yi a dakina?
Saratu bakinta ya kasa motsawa..
Jin kiran wayarsa yayi ya kara kusanto dan daukar wayar..
Kamshinta ya daki hancinta, taji kamar lumfashinta na kokarin tsayawa, da sauri tasa hannu ta ture sa gefe tayi saurin guduwa tana zuwa bakin kofar ta tsaya tana cewa, ni dama wayarka na kawo maka..
Bata jira amsar sa ba tabar dakin saurinta.

Ridwan yayi murmushi sannan ya amsa kiran bai ko kalli screen din ba.
Muryar Amal yaji, cikin yanga ta gaishe sa, ya amsa a takaice, tace dama na kirane nayi maka tuni fa, ridwan kansa daure yace name? Tace my gift mana,ridwan yadan tabe baki, i totally forgot ne, Amal tace ok zan shigo yau tunda weekend ne sai kayi kokari and get me something special, ridwan yace ok kawai ya kashe wayar, yadan ja tsaki sannan ya mike ya shige toilet.

Kaya ya saka masu sauki, sannan ya sauko kasa danyin karin safe.
A dinning table ya tarar dasu a zaune, saratu kuwa riga ta saka da skirt na jar atamfa, kujera yaja ya zauna shima, se sannan ne saratu ta dago kai tana kallonsa.
Hada ido taga zasuyi se tayi saurin dauke kanta, ikram tace ya Ridwan good morning...
Ya sakar mata murmushi morning sis, ya kalli saratu dumamenta take ci na tuwo, baki iya gaisuwa bane?
Taji maganar sa babu shiri, tadan kallesa, ban lura dakai bane ba, ina kwana?
Yace lafiya kawai a takaice, ikram ta mika masa bowl din scramble egg da baked beans, your favorite bro, ya amsa yana fadin, need your help sis, tace name fa?
Yace Amal just called me, kinsan na manta da gift dinta..
Saratu ta tabe baki tana kafa kai ta tasha ruwa.
Ikram ta mike da wayarta a hannu, indai ya Amal ce, toh this designer bags will do, ridwan ya amsa wayar yana cewa, but tana nan zuwa yau ai, kuma nasan ko munyi order bazai samu yau ba.
Ikram tace, no mom dinsu Fadila ne ke siyarwa se muce mu amso ai ko, ridwan ya gyada kai..
Saratu ta mike dauke da plate dinta, ta shige kitchen abunta. Ridwan ma na gama break dinsa ya fice daga gidan.

Kallo kawai takeyi a falo, ikram na side din mommy, ridwan ya shigo gidan, tadan kallo sa da gefen ido, ya kalleta, baki iya sannu da zuwa ba ko?
Saratu ta mike zaune,a shagwabe tace, ka cika korafi dayawa..
Ridwan ya zauna kawai yace, ina ikram ne?
Tace tana wajen maman ku, ya kalleta, kinje kin gaida ita ne?
Saratu ta Tabe baki, banje ba, ya mike yana fadin, je ki kira min ita, kafin tace komai yayi tafiyarsa.

Tunda taje bakinkofar ta rasa yaya zatayi, can dai tayi knocking wata mai aikin ce ta bude mata tace ta shigo.
Sai da gabanta ya fadi, ganin yarda gidan ya hadu fiye da nasu ma.
Hajiya layla cikin takama take saukkwa kasa, saratu hakanan taji gabanta na faduwa, fuskr hajiya layla babu alamar wasa ko kadan.
Ta wani watsa mata kallon kyama, mai ya kawo ki nan?
Saratu ta tuna da cewa ya kamata ta gaishe ta tunda dai uwar mijinta ce, tace ina wuni?
Hajiya layla taja tsaki, da kin fito fili kin nuna halinki kawai.
Saratu zatayi mgn ikram ta sauko itama tana kiran mommy..
Ganin saratu sai tazo wajen tana cewa, ah ah Sara kin shigo nan ne?
Saratu tace, eh yayanki ne ke kiranki..
Hajiya layla taja tsaki kawai tayi tafiyarta, ikram taja hannun saratu suma suka fice.

A falo suka gansa yana kasa takalminsa, ya dago yana kallonsu, ku shirya muje na kaiko..
Ikram tace ina ya ridwan?
Yace amso jakar mana..
Ikram tace oops harna manta ma wlh, ta kalli saratu, Sara kije ki shirya kema..
Saratu tadan tabe baki, anya kuwa zanje..
Ridwan ya kallota, tadan daure fuska, kuje kawai..
Ridwan baice komai ba yazo ya wuce ta ya fita.

Karfe shidda na yamma tana daki, taji dawowarsu.

Please
Vote.
Share.
And
Comments

Rashin Ga'taحيث تعيش القصص. اكتشف الآن