Chapter 4

3.1K 260 13
                                    

Salamu'aliakum anyi sallah lafiya? Nasan kunjini shiru ko am really sorry 🙇 Afuwa.

Ammani tayi saurin riko diyarta ta manna a jikinta, dije ta dago tana fadin ah ah su ammani ne  a gidan namu'cike da burin kunyarta, ashe zaki zo yau din? Har nake cewa yaya inusa yau munji ki shiru ko lafiya dai?

  Ammani tadan saki fuska tana rike da hannun saratu, lafiya lau aikin ne ban samu gamawa da wuri ba, saratu ta makale ta kam, daki taja diyarta tana mamakin mugun hali irin na  dije, ace har diyar yayanki baki bari ba, lallai dama tasan sai anyi haka, ta cire hijabinta ta dauko bakar ledar data shigo da ita, nama ne na tsire da soyayyar doya da kwai masu dumi ta zaunar da saratu suka hau ci suna yar dariyarsu gwanin sha'awa, a take ridwan ya fado mata a rai ko yaci abincin data ajiye masa oho?

Dije na jiwo dariyarsu taja wani dogon tsaki, ta zari hijabi ta shige gari abunta, washe gari inusa na tsakar gida yana shan kunun dawa,  dije na kusa dashi tana sidar kwanon dumamen tuwunta  anji girkin ammani mai dadi, ammani ta juyo daga to'yar kosan da take tace, dama inaso ne na sanar muku, dije tace lafiyar dai ko! Ina fatan ba korar ki akayi ba a wajen aikin ko?

  Ammani tace ko daya, dama zuwa na ne na sati sati ya koma a duk krshen wata, inusa yace karshen wata kuma? Yana jinjina maganar, ammani tace eh wallahi aikin ne ya karu, dije najin tace aiki ya karo tasan cewa kenan za'a kara musu kudin albashin, ta washe baki cike da murnarta, toh ai babu komai sai kiyi zamanki kawai miye aciki, saratu yanzu ai ba yarinya bace ba tunda har zata fara yiwa kanta wanka, ammani tadai kauda kai, dan tasan ba wani kulawar kirki dije kewa yi diyarta ba.

Ranar litinin da safe Secretary din alhaji kabiru yazo har gida ya dauki ammani, kasuwa suka shiga a nan ya kwashi kaya masu kyau da tsada ya siya mata, sannan ya kaita wani makeken asibiti mai kyau da tsari, anan suka shiga  ofishin likitan ridwan, ammani dai sai kalle kalle takeyi cike da kauyanci.

Doctor ne ya shiga yi mata bayani akan ciwon da ridwan ke fama dashi, matsala ce daga kwakwalwarsa, tun bayan accident din daya same su tare da mahaifiyarta,har yanzu bamu gane  kowane irin ciwo ne ya same shi ba, an kaishi Germany duk dai maganar daya ce, ba'a san komai dangane da ciwon ba, shiyasa da muka gane yarda ciwon ke tasar masa, sai muka sa aka kadaice shi a wajen da babu yawan jama'a,  dan yana yawan samun attacks ne idan ya shudanyu da mutane ko da yana nan hospital mun sha wahala mutuka dan kuwa ko magana ya daina yi da kowa, yana cikin babbban shock da trauma.

    Ammani data nutsu tana jinsa tace, ban gane karshen ba, likita yace, yana bukatar kulawa da kauna daga wajen wani dan hakan ne kawai zai iya taimaka masa.
   Ammani taja lumfashi tana tausayawa ridwan mutuka.

A bakin gate aka ajiyeta da tulin kayanta, ta leko kusa da malam haru dake zaune yana jin redio, dan Allah malam haru ko zaka saka min hannun nan, ya kuwa mike da sauri ya taimaka mata suka shige da kayan ciki, ta zauna tana kallon iyayen kayan dake gabanta, lallai Allah mai iko ne, kwana daya gashi rayuwarta ta canza, ta dauki set din da aka ce mata uniform ne da zata ringa sakawa a cikin gidan, ta saka tana kallon kanta, skirt ne baki da riga ja, sun amshe ta sosai da ammani mai kyau ce, ga kuma jikinta na fulani,lami ce ta shigo dakin da gudunta, tana maida lumfashi tace, ammani ban gani yallabai  ba fa! Hankalin ammani yayi mutukar tashi, da sauri suka fice kamar mahaukata suka shiga neman sa.

Gaba daya gidan babu ridwan babu alamar sa, hankalinsu in yayi dubu ya tashi, ammani jiki na rawa ta fito waje compound din gidan, ta duba ko ina babu shi, ta zagaya bayan gidan a nan ta hango shi zaune a gaban swimming pool idanuwansa kyam akan ruwan, ammani ta sauke lumfashi mai nauyi sannan ta karasa wajensa ahankali...

Zama tayi a kusa dashi, da sauri yaja gefe jikinsa na rawa lumfashinsa na fita sama'sama, ammani tayi kokarin fadin, kwantar da hankalinka, ridwa idanuwansa suka firfito, ya shiga shure shure, ammani na kokarin rike sa amma ina... Sai dai ta tsinci kanta cikin ruwan dake gabansu, gaba daya hankalinta ya tashi, ta shiga nutsewa tana tashi sama, ruwan babu wani yawa amma a wurin ammani kamar a cikin wani te'ko (ocean) take, ta sadakar da sake wata rayuwar dan ridwan da gudu yabar wajen....

Dije tafe rife da hannun saratu sai kuka take tana jan majina, islamiya ce naga sun dosa inda yara suke a zazzaune malaminsu na koyar dasu darasi.

   Ko sallama dije batayi ba, ina shi malamin yake! Waye zaisa kuturin hannunsa ya dukar mini diyata babu gaira babu dalili, malam ya karaso da saurinsa, haba haba dije ace kinzo wajen da ake ambaton Allah amma babu ko sallama..

  Dije taja tsaki, shi fa imanin nan a zuciya yake, ta rike kugu da gani dai kaine wanda ya duki saratu ko?
  Malam yace nine nan dije, ya za'ayi yarinya kamar wannan a aiko ta islamiya wata shidda kenan babu kudin makaranta , dije ta rike baki, yanzu naji bayani,makarantar islamiyar ce sai an biya kudi? Kace dai kawai sana'a ka fara da yaran mutane! Malam yace ke!  dije ni zaki fadawa wannan danyar maganar! Dije ta girgiza kai toh nidai ina da abubuwan da zanyi da kudina, ta fisgo saratu tana fadin, kada ki damu ai babanki saukarsa harta fi  uku mu ma da aka sani jikokin malamai sai sababi take tana zage zage...

Ahankali ammani ta bude idanuwanta, haske ta gani ya haske mata ido gaba daya a tunaninta ko mutuwa tayi, tayi kokarin mikewa a nan tayi arba da fuskar ridwan, tayi saurin zama tana kallonshi cike da mamaki, jikinsa a jike ya tsugunna a gabanta sai kallon ta yakeyi kawai, bakinta a sanyaye ta saki murmushi dan ta tabbatar shine ya taimakota ta fito daga cikin ruwan.

   Nagode ta fada masa, yadan lumshe lashes dinsa, tace gashi duk ka jike jikinka, anan kuma kawai kallonta yayi, tace mai yasa bazaka min magana ba? Yadan saki fuskarsa, sannan ya mike tsaye kawai ya fice abunsa, hakan kuwa ya saka ammani damuwa, kodai ya kurmance ne basu sani ba?

Lami ta samu a cikin dakinsu, lami ta mike da sauri, lafiya ammani ina kinje tun dazu? Ta kalli jikin ammani da yake a jike, ana yin ruwa ne a waje? Ammani ta girgiza kai, sannan ta nufi inda kayanta suke tana fadin, wai ni lami kin taba ganin yallabai yayi magana kuwa?

Lami tadan daga kanta sama, eh toh kinsan shi din bai dade daya zo nigeria ba, ammani ta kalleta, ba alhaji bane babansa? Lami na kokarin saka bra tace, eh shine ba amma mamansa dan Qatar ne wani kasa ne haka.

    Ammani tace ah'woo baya jin hausa ne kenan? Lami tayi dariya, ko yaji kadan ne,dan mamanshi tayi shekara daya ne kawai a nigeria kafin nan ta mutu, ammani tayi murmushi yanzu ta gane matsalar ashe dai ta yan kurma take masa.

Washe gari da safe ta hada masa break dinnan sannan ta tsare lami ta rubuta mata wasu sentence da turancinta itama na gwari gwari, bata ajiye masa a bakin kofa ba sai tayi knocking kofar, shiru sai da ta dauki minti goma sai gashi ya bude, ta sakar masa murmushi sannan ta kutsa kai cikin dakin, yabi ta da kallo kawai, ta ajiye masa a abincin a kan center table tana kallon girma da tsaruwar dakin ba'a magana, ridwan ya zauna a kan gado yana binta da kallo, shidai ya fahimci matar nan na son kusantar sa ko mai yasa oho.

    Ta mika masa takardar hannunta,fuskarta dauke da murmushi...


Please
Vote
And
Comments

Rashin Ga'taOnde histórias criam vida. Descubra agora