'A daki ta tarar da baban nata, ta zauna cikin sanyinta,baba sannu da dawowa, yace yauwa saratu ya mu ka same ku? Tace lafiya lau , yace har kun amso jarabawar ne? Gabanta ne yadan fadi, yanzu idan baba da innarta sukaji bataci wannan exams din nata ba tasan tabbas babu ko makawa aure zasuyi mata, kuma da wannan jakkin kauyen jibrila, ita gsky babu wanda takeso kamar wannan kyakkyawan na birni.
Inusa yace yadai? Hala bakiyi abin kirki ba ko?
Saratu tadan saki murmushin ya'ke, ah ah baba ta mika masa takardar hannunta, yace kin bani? Kin manta ni din fa jahili ne bansan ko miye a ciki ba ai.Saratu ta gyara zamanta, na manta ne baba, kaga nan ta nuna sunanta, shine sunan nawa, ya kau maida duk hankalinsa wajenta, ta nuna makin ta, 120 ne tace kaga nan shine makin nawa ta washe baki, naci dayawa ko baba, kaga fa nambobi ne har uku a jere.
Inusa ya washe baki aikuwa dai kam, lallai ashe duk wasan nan naki zakiyi abun arziki, na tabbata innarki zataji dadi sosai, bari na kira na fada mata ko? Saratu ta gyada kai, tana fitowa taci karo da dije dake musu labe bakin kofa, tace ja'ira wato kin gama tsara uban naki ko! Ni na san duk karyar banza ce kika fada masa babu abunda kika tsanana.
Saratu ta turo baki, nifa dije nace miki ki daina shiga sabgata ko!
Dije tayi mata dakuwa,ke ni ki je ga daddawa can a daki ta mai kuli ce danayi jiya ki mika mata ita, saratu tayi saurin cewa, ni zan kai daddawar?Dije tace yau kika fara?
Saratu tace ni gsky dije bazan kai ba, mutum yayi ta bin layi yana wani wari..
Dije ta rike baki, yanzu ke saratu daga zana jarabawar kike wannan kar'kabon? Toh ina ga kinje jami'ar?
Saratu ta shige daki tana gunguni.Hajiya layla zaune a beauty saloon din hajja meena, cikin fira hajja meena tace, wai ni aminiyas yaushe zakuyiwa Ridwan aure ne?
Hajiya layla ta tabe baki, wacce wawiyar ce zata auri psycho kamar Ridwan?kin san dai ciwon da yake fama dashi, ai a haka zai ka're rayuwarsa.
Hajja meena tace, ashsha ai yaro kamar Ridwan with his looks ko wacce zata so aurensa koma miye dashi, hajiya layla ta kura mata ido, mai kike nufi?
Hajja meena ta gyara zamanta, dama fa Amal ce ta dame ni wlh, wai ita Ridwan takeso.
Hajiya layla ta ware ido, Ridwan kuma? Kamar dai mazan duniyar sun kare, wannan tsinannen yaron!
Hajja meena ta girgiza kai, haba aminiyas ina ganinki kamar mai wayo, ai duk dukiyar da kike kwadayin samunta Ridwan ne mallakin ta ko kin manta ne?Hajiya layla tayi zugum, hajja meena ta saki murmushi, yanzu idan Amal dina ce ta auresa kinga ai komai ya zama namu basai munyi ta wahala a banza ba.
Hajiya layla ta nisa tace, kai amma aminiyas kin iya kawo shawara mai kyau wlh, ni dama na rasa yarda zanyi na kawar wannan yaron, saboda nacin wannan ammanin, tana kula da yaron nan kamar ranta, amma kinga da Amal ta auresa komai ma yazo min da sauki.Hajja meena tadai kwashe da dariya, kedai kawai trust me, suka sake shekewa da dariya suna tafawa.
A bangaren Ridwan kuwa, har lokacin ya kasa yarda wai hes now stable, yayi tunaninsa ya gaji,komai ya faru haka da yasamu sauki farat daya yana godewa Allah sosai, dan haka yanzu ne ya fara cin lokacinsa, duk inda baya shiga yana samun zuwa yanzu, ko aiki yaje yana shiga meetings, hakan ba karamin yayi wa daddy ba.
Ammani ta same sa a garden duk ya waje takardu yana ta faman zanen sa, contract ne aka kawo masa daga lagos, ta ajiye ma sa cup din hot coffee sannan ta zauna tana cewa, yallabai bazaka dan ajiye ka huta bane?
Ya dago yace, kada ki damu Mom nan da awa daya ma zan kammala duka, gobe ne deadline din aikin, tace toh kayi maza dai dan yamma ta gabato, Amal da ikram ne suka karaso wajen, sunci gayu kamar zasu biki.
Amal na rangwada tace, Ya Ridwan ina wuni? Ya kalleta ya dauke kai, lfy ya kalli ikram sai ina sarkin yawo?
Tace ya Ridwan ka manta na fada maka yau ne graduation party din Ya amal , Ridan yadan yi shiru dan gaba ya manta, yace congratulations ta saki murmushi har dimple dinta ya lotsa, tace thanks alot dear , ina gift dina ta mika masa hannunta dayaji jan far'ce.
