http://cookiteasycom.blogspot.com/
This is my new food blog, i got recipes in there for you pls visit n share. Thank you
'Da safe a dinning suka hade, yana zama ya dan kallota, itama din kuwa shi take kallo, gani yayi ta sakar masa murmushin ta har yar hushiryarta na bayyana, ya samu kansa da ya maida mata martani, sannan ya gaisar da hajiya.
Hajiya tace, ni gaskiya wadan nan kayan soye'soyen naku ba da'da ni da kasa sukayi ba ta ture plate din gabanta, saratu tace nima dai hajiya ban bana son cinsu wlh, ko nayi mana dumame ne? Akwai sauran na jiya.
Hajiya tace, yauwa yar albarka je ki kiyi mana ai ni naji dadin shigowarki cikin zuri'ar mu, ai irin wadan nan ta nuna su chips sai su Ridwan yan gayu ko?
Ridwan yayi dariya haba hajiya kema din ai kina ci idan Mom ce tayi ko..
Saratu dake kokarin shigewa kitchen tadan tsaya jin ya ambaci Mom, mai yasa yake mugun son innarta hakane bayan yana da tasa mahaifiyar..Ikram dake shan orange juice tace, ai kuwa dai nima ban manta ba har su samosa kinaci fa, hajiya tayi mata dakuwa, ai dama ke komai yayanki ya fada kina bayansa, shekaru biyar dinne kika tuna wani abu gulman'ma..
Saratu ta kawo tuwon cike da plate ta ajiye na hajiya sannan ta koma kitchen ta dauko nata, tadan kallo Ridwan taga sai wani con yanga yakeyi da fork n knife ita kuwa ta da'ba hannu abunta.
ridwan ya mike ni na tafi aiki hajiya, hajiya ta bisa da kallo, sai ga hawaye, Allah abun godiya amma dole ne naje har garin su ammani nayi mata godiya ta musamman, Allah ya bada ladar Rainon Maraya Mai RASHIN GA'TA kamar ka Ridwan!!!!!Gaban saratu ne ya fadi ras! Tabi sa da kallo cike da tsananin mamakin furucin da hajiya tayi! Maraya? Mai rashin Gata? Kan ta duk ya daure, dama mutumin dake cikin wannan gatar da dukiyar zai iya samun Rashin gata?
Ridwan ya zagayo yana rungumeta, haba hajiya kinsan ai Mom dina babu kamarta a duniyar nan, ba mutum bace mai jiran godiya daga wani..
Hajiya tace, dole naje Ridwanu, itace fa silar samun saukin Ciwon da kayi shekara da shekaru kana fama dashi, ciwon daya hanaka samun duk wani dadin duniyar nan..sannan gashi bar yar'ta fa alhaji yace ta baka...
Ridwan yayi saurin katse ta, hajiya kefa matsalarki kenan wlh, miye na wani tuna baya a nan huh!Komai fa ya wuce yanzu let bygones be bygones .
Ni kinga ma tafiyata aiki zanyi kada nayi late, i know haydar is waiting for me..Hajiya ta share hawayenta, toh sai ka dawo, ya kalli saratu data zurfa cikin tunani, hajiya ta lura da kallon da yake wa matar tasa, sai ta tabo ta, surukar bakya zuwa rakiyar miji ne?
Saratu tayi firfigit, taga duk ita suke kallo, bata san ma lokacin data ce, ina zuwa ba...
Hajiya tace toh tashi kije, Ridwan yayi wani gaba abunsa yana takon kasaitar sa.
Saratu tabi bayansa itama..
A compound gaban motar sa, ya tsaya yana juyowa, ita kuwa lokacin bata ma san ya tsaya ba binshi take kafa'da kafa, yana juyowa sukaci karo..Kanta ya bugi kirjinsa, yadan matse lips dinsa.
Tayi saurin dagowa tana kallonsa.
Am sorry Ya RIDWAN, yabi lips dinta da kallo, yarda take furta Ridwan din yana burge sa sosai.Ita kuwa tunani takeyi, ko ta tambayeshi labarin rayuwarsa ne? Sai kuma ta girgiza kai, hakane bai dace b.
Yace wai tunanin me kike yi ne huh?
Tace babu, yace come on fada min mana?
Tace no kaje kada kayi latti, yace ai ni bana latti, ta dan kallesa, saboda kai oga ne ko?
Yayi dariya yana shigewa motar sa, sai na dawo matas...Saratu gaba daya ranar tunani takeyi, so take kawai taji miye ya faru da Ridwan a baya, miye tarihin rayuwarsa?
Suna zaune a falo da hajiya suna kallo dan ikram ma ta tafi rubuta last paper dinta.
Hajiya layla ce ta shigo kamar mutuniyar arziki, tasha babban mayafinta.
Hajiya tabi ta da kallo, tazo ta duka tace, hajiya ina kwana anzo lafiya?

YOU ARE READING
Rashin Ga'ta
General FictionRashin gaa'ta is a hausa written story, follow and vote