Team RIDSA 💖
'Ammar yazo ya dauke ta sukaje har school din su Ayla,dadi ne sosai ya lullube Ayla ganin parents dinta sun fi na kowa haduwa,friends dinta na ta ya'ba Ammar.
'Bayan kwana uku,Ammar ya samu abbansu a falo,ya sanar masa da cewa shi fa yana son saratu kuma aurenta yakeso yayi,abban yaji dadin hakan dan kuwa ya yaba da tarbiyyar saratu sosai,bai taba ganinta tsaye da wani saurayi ba.
Minal ce ta fito daga kicin dan fadawa abba babu gas,jin suna mgnr kawarta se ta labe tana jinsu, ta daka tsallen murna dama ita damuwarta kenan, idan akayi auren ta next month bazata ji dadin barin saratu a gida ba,tayi tayi da ita ta fito da wani amma se tace ita bata da kowa ai.
Mami ta samu a daki ta idar da sallah,ta di're kan bed tana dariya mai cike da farin ciki sosai,mami ta juyo ta kalleta,ke lafiya kika shigo min ba ko sallama sai dariya?
Minal tace ai mami ni yau cikin farin ciki nake,yanzu naji ya Ammar na fadawa abba yana son Sarah...
Mami tace kai haba dan Allah?ta washe baki,minal tace wallahi,mami tace toh madalla Allah yasa ayi damu nayi farin ciki kwarai.'''Hajja meena ta kalli Amal,yanzu kina nufin wannan mayyar yarinyar sai da ta sake dawowa rayuwar ridwan?duk wulakancin da muka musu bai ishe su ba kenan!
Amal tace wlh mom ni ma nayi mamaki sosai sai dai kawai fa na ganta..Allah yaso ma ridwan din bai san wacece ita ba.
hajiya layla taja tsaki,toh ai duk laifin naku ne...
Suka kalleta a tare,tace eh mana,kun manta me malam yace damu ne?ya fa sanar daku cewa.. zuciyar ridwan ba zata taba son Amal ba kawai zama zasuyi bawai dan zai so ta ba.kuma indai har wannan yarinyar bata manta dashi ba ,bata cire sa daga cikin zuciyarta ba,toh lallai shima zuciyarsa ba zata taba mantawa da ita ba duk da he can't remember her....
Amal taja tsaki,zan sake komawa wajen wani malamin,ba sai mu canza wani ba,na lura wannan tsofon bai san miye aikin sa ba,tun yaushe ridwan ya mallaka min zuciyarsa huh!
Hajja meena tace,nima dai ban yarda da wannan malamin ba,hajiya layla ta daga kafada nidai yamin kuma naga sa'a a cikin aikinsa..
Kiran ikram ne ya shigo wayar hajiya layla, ta mike tana barin wajen,hello my baby?
Sai yanzu kika ga damar kirana ko?missed call mawa nayi miki yau dinnan?
Ikram tace,toh ai kece mommy kullum ina tunashe ki wlh kiji tsoron Allah,wai ni me ya Ridwan ya tsare miki ne haka kika tsane sa?Hajiya layla tace,ke bana son sakarcin banza ba na hanaki yimin wannan mgnr ba?kullum baki da abun mgnr se ta ridwan?
Ikram tace dolene na fada miki gsky mommy tunda dai ni mai kaunar ki ce.. yanzu ace mommy harda ke su Amal zasu hada kai suyi wa ya Ridwan fake child!
Gaban Hajiya layla ya fadi ras,tace fake child kuma !!cike da mamaki sosai...Ikram tace eh mana wato basu sanar dake ba kenan?toh abokin mansoor shine fa doctor din ya Amal din a can kasar south Korea,kuma duk ya fayyace mana komai...
Hajiya layla taji wani irin haushi ya lullubeta yanzu dama amiyarta zatayi mata haka?lallai biri yayi kama da mutum,wato dan su kwashe dukiyar ridwan ko?tace mai ya fada muku ikram?
Ikram ta zauna tana fadin,ya Amal tabbas ta samu ciki amma cikin nan ya zube tun yana wata biyu,sai taci gaba da karyar cikinta har ta kai lkcn haihuwarta,doctors dayawa ta biya aka samo mata yaro dan kasar nigeria wanda iyayensa sukayi hadari aka kawo su nan asibitin,toh mommy Ayman ba jinin ya Ridwan bane ba,kin fi kowa sanin manufar su,kuma ko ke basu sanarwa ba kinga kuwa ba mutanen arziki bane...Hajiya layla ta kashe wayar zuciyarta na tafarfasa,ta mike dan komawa dakin hajja meena...
Sai ji kawai tayi suna ta gulmarta,suna shawarar yarda zasu kawar da ita daga cikin plan dinsu,Amal har cewa tayi su kashe ta kawai tunda ba uwar ridwan bace ta gaske,kuma ma ai ridwan shi ke da duka dunkiyar,me zasuyi da hajiya layla.
ta dafe kirji tayi tana ja da baya,bata taba tsanmanin cewa hajja meena da Amal zasu ci mutumcin ta ba haka.
