’kiran sallar asubahi ne yasa Ridwan yin mi'ka cike da barci a idonsa, yayi rolling kan bed dinsa yana karanta addu'ar tashi daga barci, cak ya tsaya a firgice ya mike zaune da saurinsa, ji yayi yaci karo da mutum.
Cike da mamaki ya hango mutum can karshen gadonsa ta rufe jikinta gabadaya da blanket, ya sauko daga kan gadon da saurinsa ya karasa wajenta yana tsananin mamaki, ko waye ya shigo masa daki? Dan harya manta da wata matarsa dake next door, dama gashi shi sarkin tsoro ne, matsawa yayi kusa ya janye blanket din gaba daya daga jikinta...
Firgita yayi sosai ganin dogon gashinta ya rufe gaba daya fuskarta, yaja baya da saurinsa, ita kuwa saratu cikin barcinta mai nauyi taji sanyi yana ratsata, cike da shagwaba fara magana cikin muryarta mai tsaki, haba dije ki rufo min kofar dakin mana sanyi nakeji wlh....
Tana wani juyi fuskarta ta bayyana tangaran...Mutuwar tsaye kawai Ridwa yayi, cike da mamakin ganin yarinyar, dama itace diyar Mom dinsa? Ya fada a sarari, sai daya dauki minti biyar a tsaye yana kare mata kallo hade da tunane tunane sai can daga bisani ya koma ya rufa mata bargon, sannan ya dauki kayansa da duk abunda zai bukata ya fice daga dakin.
Sai shidda saura saratu ta farka daga barcinta mai dadi, harda mafarkin wannan kyakkyawan tayi ma, dauke da salati a bakinta, idonta a rufe tana mi'ka hade da hamma.
Ware ido tayi sosai tana kallon inda take, baki bude tayi saurin mikewa zaune tana fadin, yau na shiga uku! Ina na kawo kaina kuma? Tabi dakin da kallo, yafi nata girma sannan ya hadu karshe komai a kimste tas dashi se wani kamshi mai dadi ke tashi...
Ta lallaba tana san'da harta bude kofar ta fice da gudu, dakin ta ta dawo taga ashe kofofi ne guda biyu a wajen jere, taja tsaki Allah dai ya taimake ta wannan yaron bai ganta a ciki ba, toh ba dakinsa bane ma kenan? Ta rike kugu aikuwa can zan koma abuna, gadon yafi taushi gashi kuma harda su kwabat na saka kaya, tayi yar dariyarta har wushiryarta ta bayyana.
Wanka Tayi ta saka duguwar riga wacce ta amshe ta sosai, fuskarta fayau dama ita ba gwanin kwalliya bace, ta daura dankwalinta ture kaga tsiya, sannan ta sauko kasa, a lkcn har Ridwan yabar gidan ma, abinci ta hango a dinning ta waiga taga babu kowa ai kuwa ta karasa wajen, ta shiga hade miyau ganin dishes kala'kala gashi duk ya tsakure su ne kawai baici dayawa ba, ta zauna ta hau ci abunta, indo ta fito ta kofar kicin, tace anty ina kwana, saratu na saka'cen hakoranta tace, ina kwana ai kece antyna tunda kin girme mini sosai ko?
Indo tayi murmushi kawai tace, dama yallabai ne yace mu tambayeki abunda kike so a girka na rana(lunch)
Saratu tadan ja tsaki, lallai ma dan rainin wayo, wato ya barta da yunwa jiya shine yau zai wani turo a tambayeta abunda takeson ci, ta kalli indo kiyi min tuwo kawai da miyar kubewa, indo tace toh shikenan kawai ta fice.Ta mike ta koma sama, dakin sa ta sake shiga, taja lumfashi kai gaskiya tana godewa Allah daya kawo ta cikin wannan daular,ta tuna da irin nasu dakin,tadan girgiza kai, talauci baiyi ba, hango wani babban photo tayi an juya shi, ta karasa tasa hannu ta dauko, hoton alhaji kabiru ne da mahaifiyar Ridwan, ta saki baki tana fadin, lallai Allah yayiwa wannan matar kyau, but tana mata kama da wani? Ta tabe baki ta maidashi tana mikewa, taji ta taka wani abu, tasa hannu ta dauko, drawing book dinsa da bussines card din sa a ciki, ta shiga kallon zanen kayan da yayi a ciki, very unique , tace nan din dai dakinsa ne, ta tabe baki, ko ina ya kwana jiya bai shigo ya same ta a ciki ba?
Karfe biyar na yamma zaman kadaici duk ya gundureta, taja tsaki hade da mikewa, taje ta tsaya a bakin window tana leken waje, garden din gidan ne ya dauki hankalinta sosai, dama gashi lkcn damuna ne ko ina yayi kore shar...
Tace tab ai sai naje na bawa idona hakkinsa, tayi kasa da saurinta.
Kofar da taga indo na shigowa nan tabi itama, aikuwa sukaci karo da indon dake ta faman girki, tace anty ina zakije? Saratu tace wasu flowers ne na hango a waje, wajen ya burgi ni ne wlh, indo tayi dariya, sannan tace idan kika fita, akwai wata hanya da tayi hagu toh a nan ne wajen, saratu ta washe baki nagode ta fice cikin saurinta.