'Dai dai lkcn ne ammar ya kira sunan sarah ta juya cikin saurinta,sai Allah yasa amal bata ga fuskar taba,duk da haka kishine ya turnike ta,ta gaji da yarda yan mata ke rurubin mijinta haka,ba'a nan naija kawai ba har can kasar south Korea inda suke zama yanzu.
Taja hannunsa tana shagwabe fuska,haba sweetie ina ta maka mgn kayi shiru,ridwan ya juyo yana kallonta,sorry mai kika ce?ta turo baki kawai.. tace muje gida am tired, ya gyada kai yana waige waige.
Sun fito harabar hotel din ammar yaje dauko motar sa,minal ta riko hannun saratu, tell me pls sarah akwai abunda ke damun ki ko?
Saratu ta girgiza kai,tace come on nifa kawar ki ce?saratu tace zan sanar miki watarana minal amma not now pls,minal tace toh shikenan but cheer up pls.'Kwana biyu suka wuce,amma kullum saratu bata samun isasshen barci,tunanin ridwan kawai takeyi da mafarkan sa,inna na lura da ita amma ta share kawai.
Da sassafe tayi shirin tafiya wajen aikinta,Ayla ce tsugunne tana wasa da ruwan wanke wanke a cikin roba wanda ammani ta ajiye,saratu tabi ta da kallo,Ayla ta kalleta,ya sarah tayi mata nuni da hannu wai ta dan duko,saratu ta duka tana fadin,bakya jin fadan wasa da ruwan nan ko bari inna ta fito ta same ki.
Ayla ta kai bakinta kunnen sarah tace,ya sarah pls zan biki wajen aikin ki pls..
Saratu tadan harareta,miye na gulma toh bana hana ki ba?Ayla tace shiiish!idan mama dije taji ni bazata bari naje ba.
Saratu tayi dariya,sai ga dije ta fito daga bayi rike da yar bu'ta a hannunta.
Tace ai ina jinki Ayla,sarkin tsara zance ni bansan wa kika gado wannan surutun naki ba,badai kiso ne kawai muje kauye dake yau ko,shine zaki gudu wajen aikin saratu,toh bara ta watsa miki kasa a ido...Ayla ta turo baki,toh ni bana son garin nan mama dije,sauro yayi yawa..taje ta kama hannun saratu pls ya sarah kije dani i will not misbehave i promised.
Minal ta shigo gidan cikin shiri itama,Ayla taje ta riko hannunta pls ya minal kuje dani pls tayi rau rau da ido.
A haka dai duk suka hakura sukaje da ita badan son ransu ba sbd Ayla da shegen surutun ta tana iya ballo musu ruwa.Tunda sukaje ma'aikatar colleagues din su ke tashan dariya wajen Ayla,faruk ne ya tambaye ta,ita wacece a wajen su minal,tace sisters dina ne ,yayi mamaki sosai amma ya share kawai yana daukarta.
Da yamma wajen biyar da rabi suka fito gate dan tafiya gida,motar ammar ce suka hango can a tsallakensu,ya fito yana daga musu hannu,minal ta kalli saratu, yauwa sarah zamuje wajen kakar mu ne yanzu da ya ammar bata jin dadi,saratu tace Allah sarki zanso naje na dubo ta nima amma kin ga uban aikin dake gabana,minal tayi dariya,ke da faruk bansan mai yasa jinin ku bai hadu ba wlh,saratu ta tabe baki kedai jeki kawai bari mu kara gaba ko zamu samu mai daidaita, Ayla tayiwa minal bye bye kafin suka wuce.
Suna tafiya hadari na kara haduwa,ga iska anayi garin yayi sanyi gwanin dadi,Ayla sai tsalle takeyi saratu nata mata fada,yayyafi aka farayi saratu taja tsaki,yau kamar masu daidaita din na yajin aiki ne?ta fada da dan fushi ganin suna ta tafiya basu samu ko daya ba.
Ayla tayi dariya ganin yarda saratu ta wani daure fuskarta,saratu tace dariyar mai kikeyi naughty gal?
Ayla ta rufe bakinta tana tsalle kafin ta kwacee daga rikon da saratu tayi mata ta shiga gudu tana mata gwalo...Saura kiris mota ta kade ta,dan sai da aka jaa wani irin burki...
Ita kuwa Ayla bata ma sani ba ko a jikinta,dan ta juya bayanta tana yiwa saratu tsukana...
Cikin tashin hankali da fusata ne saratu ta karasa wajenta..A harzuge kawai ta daga hannu zata mare ta..
Ji tayi kawai an rike hannunta gam..
Da sauri ta dago dan ganin ko waye ne..Ridwan ta gani fuskar sa akanta shima cike da dan mamakin sake ganin ta,dan tunda suka a hadu a dinner idanunsa suka dauki hoton fuskarta.
