Chapter 19

3.5K 213 11
                                    

This chapter is dedicated to all TEAM RIDSA much love😍

'Dije,ammani har ma da inusa cikin gaggawa suka shigo garin kano gaisuwa, dan jin rasuwar alhaji kabiru ya mutukar girgiza su ba kadan ba.

Saratu na ganin su ta rungume ammani tana sakin kuka sosai, tun bayan kwana daya kenan likitoci ke kan Ridwan amma babu wani sauki, sai sume sume da yake fama dashi, gashi ko shiga dakin ma an hana su suyi, hankalinsu a tashe yake sosai.

Ammani ce ta shiga matsa musu da cin abinci, dan hajiya da ikram ma duka ba kanta ne sai kuke kuke sukayi abun tausayi, toh balle saratu da mijinta ke can yana fama da ciwo.
Dije dai na gefe guda tana yiwa saratu fada, dan ba karamin ramewa tayi ba kwana daya kacal.

Kwana biyu Ridwan na fama da sume sume abun tausayi duk ya fa'da ya rame sosai, jikin nasa babu sauki.
Hajiya layla da hajja meena ne suka shigo side din, lokacin hajiya na dakin ta tadan samu barci.

Ammani suka kalla cikin tsana da kyama, hajiya layla tace, ammani ina son magana dake, ammani tace toh hajiya, saratu ta dago tana kallon su, hajja meena ta wanka mata harara, hajiya layla tace kema ta'so yar rashin kunya ko gaisuwa baki iya ba, saratu ta mike a sanyaye dan bata da karfin maida musu mgn yanzu, dije ma ta mike zata biyosu, hajja meena ta yatsine fuska, waya gayyace ki?
Dije ta tsuke baki, ni kuwa aka gayyata tunda har kuka kira saratu da ammani ai ba mai tsame ni a ciki kuwa.

Hajiya layla tace, ai dama ku yan kauyen nan da shegen son junan ku kuke, kyeleta tazo kawai.

Can kitchen suka shige, hajiya layla ta wani daure fuska, kamar yarda kika sani, ni ba kaunar auren Ridwan da wannan yar taki nakeyi ba, gabansu ya fadi ras, saratu ta kura mata ido.
So nakeyi ki dauki diyarki ku bar gidanmu da rayuwar mu har abada...

Dije ta dafe kirji tace, a'uzubillahi minal shaidanil rajim.
Hajja meena taja tsaki, wa kika gani yayi maki kama da shaidani a nan huh! Inace ma alhajin da shine ya ha'da wannan auren babu shi yanzu. Kuma shi Ridwan din yanzu ta lafiyar sa yake yi ba ta wani mata ba.

Ammani tace, haba hajiya, miji bai saki matarsa ba kawai hakanan sai mu dauke ta mu tashi, ai hakan bai dace ba ko?
Dije tace kwarai kuwa.
Hajiya layla ta daka mata tsawa, ke ammani har akwai dacewa a tsakanin mu daku! Kin san munfi karfin hada zuri'a daku kawai dai kulle'kullenki da kikayi yasa alhaji ha'da wannan auren, yanzu kuma babu shi dan haka ki kwashi diyarki ku kara gaba ehe!

A nan dai suka shiga threatening dinsu ammani, hajiya layla har fadi takeyi, indai har ammani bata raba Ridwan da diyarta ba toh lallai zasu rasa Ridwan din shima, ta ware ido, ina tunanin by now ammani kinfi kowa sanin halina da abun da zan iya aikatawa, hankalinsu ya tashi sosai,saratu na kuka tace, inna na yarda zan bar shi har abada, nafi kowa son Ridwan ya rayu nafi kowa son ya samu ingantacciyar lfy, tunda su basu da imani mu muna dashi, kuma ba dukiyarsu muke kwadayi ba..
Dije ta kwabe bakinta, ke wacce irin gidahuma ce ne? Mijin naki bai sake ki ba zaki barsa! .

A takaice dai korar ka're su Hajiya layla sukayi wa saratu da yan iyayenta, abun babu dadi Ana ta zaman makoki Amma rashin mutumci kawai suke dankara musu.

A ranar hajiya layla ta kira dr tace dashi tana son ganin sa, daya zo suka ma'ka masa makodan kudi akan yayi wa Ridwan allurar da zata saka ya samu memory loss, likita yace babu damuwa zai yi masa duk yarda suke so, hajja meena tace, kuma zamuje malam shima yayi nasa aikin yanzu, sannan ya mantar dashi wannan shegiyar yarinyar da uwarta, suka yi dariya cike da dadin samun nasarar su.

'Sati daya kacokam saratu an kasa gano kanta, kullum kuka takeyi gashi ta ki cin ko abincin kirki, dije takaici duk ya ishe ta, gashi dai yanzu an ci musu wulakanci an hana su samun dadin rayuwa, kullum itama cikin bakin ciki take, inusa al'amarin haushi yake basa sosai dan ya riga ya yanke hukunci, bazai taba yarda ya sake aurar da diyarsa bada ra'ayinta ba, zai bata damar zaben mijinta, ammani kuwa kukan zuci takeyi, addu'ar ta daya Allah ya tsare mata yallabai, koda basu tare dashi addu'ar su zata kasance tare dashi.

Rashin Ga'taDonde viven las historias. Descúbrelo ahora