chapter 18

3.1K 216 3
                                        

' gidane irin na tsarin larabawa, ya hadu karshe ba wani girma ya cika ba kawai dai yanayin tsarinsa abun burgewa, Tariq  ne yayi musu ja gaba har zuwa ciki,  a wani corridor suka hadu da wata budurwa balarabiya ce mai kyau, ta bude baki tana kallon Ridwan, Ridwan ya nuna ta, yace, ANISA! Ya kira sunanta, ta rungumesa cike da murnar ta, saratu ta kura musu ido tana kallon ikon Allah, tariq yayi dariya yace, Anisa you are still behaving like a baby, say Salam to SaRah she's ridwan's wife.
  Anisa ta ware ido, MashaAllah Salam sister in law ta rungume saratu.

Wani daki suka shiga kamshi ne ya bugi hancinsu, a nan suka tarar da wata dittijuwar mata zaune akan royal chair tana can carbi, anisa cike da murna sosai tayi nusu ISO a wajen Ammah wayo kakar su Ridwan kenan(tariq da anisa cousins dinsa ne, mahaifiyar su ta rasu uncle din Ridwan wato kanin sabiha kenan, ya dawo dasu wajen ammah)

    Kuka ta fashe dashi ganin dan jikan nata, sai ta tuna da diyarta sabiha, Ridwan ya rungumeta yana lallashinta, tariq kuwa yace da ita, look here Ammah Ridwan brought his wife with him, tayi saurin mikawa saratu hannu, saratu taje wajenta ta gaishe da ita da turanci, ta shafa fuskarta ta shiga yi musu addu'a da harshen larabci.

Sai da kyal sukaci abinci,  dan Ammah ta tsare su a dakinta har sai da kawunsu wato mahaifin anisa da tariq kenan ya dawo daga aiki, sannan ne tariq yazo ya kwashe su zuwa dinning table, a nan saratu taci abincin da bata taba cin irin sa, tayi zaton zata kasa ci ma, amma jin taste din sai gashi harda su kari.

Daki babba anisa ta kaisu, tayi musu sai da safe sannan ta rufo musu kofa.
     Saratu ta shiga scanning din dakin, Ridwan kuwa dama waya yake yi da daddy dinsa, ta tsaya gaban standing AC sannan ta juyo daidai lkcn Ridwan ke ajiye wayar hannunsa kan bed.

   Tace, ya Ridwan wannan miye ne? Naji yana fitar da dumi da zafi haka. 
Ridwan yazo wajenta, ya dungurar mata kai, yar kauye kawai, AC ne mana.

Saratu ta yatsine fuska, ai nima din na san  miye AC ko, amma ba irin wannan ba, ni na bango na sani, sannan kuma Ac ai ba zafi yake fitarwa ba ko? Ta rike kugunta sanyi yake fitarwa ko jakkin kauye ma yasani bare ni.
      Ridwan ya kwashe da dariya, yarda take zuba zance ne yake basa dariya.

   Saratu tayi dan tsaki kawai taje wajen gadon ta tsaya, ta ya'fito shi da hannu, ya tsaya yana kallonta, ta haye gadon ta shiga raba tsakiyar bed din da kananun pillows, Ridwan dai nasa kallo kawai.
    Tana gamawa ta dago tana wurga masa fararen idanuwanta, dont cross this line ok? Ta fada da turancinta dabai goge ba.if you do you are death!
Ridwan ya hade fuska yace, banda fa son kai RIDSA, kalla side dina fa, naki yafi yawa, saratu ta sauko gadon tana cewa, ni ai ina yawo ne idan ina barci, kai kuma babba ne zaka iya manegi ai ko?

Ridwan ya gyada kai a sanyaye, taje wajen akwatin ta, ta dauko rigar barcinta mai kyau, ikram ce ta hada mata kayanta, ta yatsine fuska, ni bazan iya saka wannan ba muna daki daya da ya Ridwan ba.
    Ridwan shi a lkcn ma har ya shige toilet ya sako nasa kayan.
   Ya iske ta tayi tagumi, yace hey kiddo! Me yafaru ne?
Ta turo baki, kalla fa rigunan da ikram duk ta saka min wai na barci kenan.
   Ya kurawa rigunan ido, duk masu spaghetti  hand ne, wasu kuma da tsagu, yace toh miye ki saka mana..
Ta make kafada, yace toh nidai barci nakeji RIDSA, kinga zansha drugs dina.

Kamar zatayi kuka ta mike, gashi yanzu ta saba da canza kayanta idan zatayi barci, taje zata kwanta, Ridwan yace kin fasa canza kayan ne?
Ta gyada kai, eh sai da safen mu.
   Yadan lumfasa, yaje wajen kayanta, ya dauko mata doguwar riga ta barcin, sannan ya nemo wata jacket tasa marar nauyi dama uniSex ce maza da mata duk zasu iya sakawa.
    Ya dauko su yazo wajenta, gashi je ki canza wadan nan, ta mike tana kallon kayan,sannan ta amsa taje ta sako, ga kamshin Ridwan a jacket din, ta saki murmushi, lkcn yana shan drugs dinsa taje ta kwanta, shima ya kwanta yana kashe wutar dakin.

Rashin Ga'taKde žijí příběhy. Začni objevovat