Team RIDSA 💖
'Washe gari zazzabi ne ya rufe ta sosai sakamakon kukan data sha,da kyal taja jikinta zuwa toilet tayi alwala tazo ta zauna tayi sallarta.
Ta mike kamar zata fadi ganin karfe 6 yayi,da kyal taja jiki zuwa kitchen.Ridwan ya tsaya da jogging din da yakeyi yana tunanin ko ya kafar ta ta? Bai san meyasa ya damu yarinya haka ba?
Yaja tsaki yayi hanyar komawa cikin gida.
Yana shigowa kitchen din ya hango ta sai layi takeyi kamar zata fadi kasa...
Cikin sauri yayo kanta ai kuwa ta zube jikinsa a sume.Hankalinsa ne ya tashi kwarai,ya sure ta zuwa falo ya kwantar akan 3 seater yana kallon fuskarta da dan kumbura tayi fayau.
Ya mike yaje ya debo ruwa yazo ya shiga yayyafa mata,hankalinsa a mutukar tashe.Girar idanunta ne ya fara motsi kafin ta bude idon da yayi mata nauyi..
Akan fuskar Ridwan kwayar idonta ta tsaya,ta rasa dalili amma shes so afraid idan har abada ridwan ya kasa gane ta a cikin rayuwarsa.Kuka ta farayi kawai babu shiri,ridwan ya rikice ya shiga tambayarta,jikin ki yayi tsanani haka ne?
Shine jiya baki sanar min ba?Ya koma kitchen yana runtse idonsa,haka nan yake jin kukan da takeyi yana ratsa jikinsa sosai,ya dauko cup ya hado tea sannan ya dawo wajen ta tana ta faman kukan ta.
Ya ajiye mug din akan table yazo yace da ita,stop being a baby mana?get up..
Saratu ta mike kawai ta rungume sa tsam tana sake sakin wani kukan takaicin.
Ridwan yayi mutuwar zaune kawai,why is she hugging him like that,tausayi ta basa dan haka ya kyeleta kawai tayi me isar ta.Janye wa tayi da sauri tana ja baya kadan a kunyace.
Ya miko mata mug din,shanye wannan bari naje na samo miki magani,ko muje asibiti ne?
Ta girgiza kai,ya wuce abunsa yana fadin,kada ki sake ki tashi daga nan ina zuwa.'Sai daya dauki 30mins kafin ya dawo,ya tarar da ita a nan saman sofa barcin wahala ya dauke ta.
Tsayawa yayi yana kare mata kallo,tayi wani irin juyi zata fado daga kan kujerar...Ridwan yayi saurin dukawa yasa hannunsa ya taro ta da hanzarin sa..
Lumfashi ta saki tana motsa lips dinta,zuciyarsa ta shiga bugawa,kansa ya fara juyawa,ya maida ita kan kujerar da sauri,sannan ya sake sungumarta zuwa dakin dake kusa da nasa,ya lura bata iya barci a karamin waje ba tana da yawan juye juye.Yana fitowa kofar ayman na zuwa wajensa,yace good morning daddy,ridwan ya shafa kansa,mrng my boy.
Kitchen suka sauka, ridwan ya zaunar da ayman sannan ya dauko iPad dinsa ya shiga duba recipes masu sauki na breakfast..
Da kyal ya samo egg omelet da potatoe balls,ya shiga aikinsa sanye da apron lool he look so charming 😉, ayman nata masa dariya..'Farkawa tayi sakamakon mafarkin da tayi da Ridwan,ganinta tayi a daki ta shiga ware idonta,ledar magani ta gani a gefenta,jikinta yadan yi karfi sbd barcin data dan samu,ta sauko daga kan gado ta dauki ledar hade da fitowa dan ta samo ruwa tasha.
Kamshi ne taji ya mamaye falon,da mamaki ta karasa kitchen din..
Can ta hango gogan naku na kokarin soya potatoe balls dinsa,ta saki murmushi tana binsa da kallo,he's so handsome n cute...Ayman ne ya hango ta yazo ya riko hannunta, look anty my daddy is cooking for us today...
Ridwan ya juyo wujiga'wujiga dashi,da gani ya gaji sosai duk yayi zufa,saratu ta kwashe da dariya,ya hade fuska yana kashe ipad dinsa inda yake kallon recipe a video.Saratu ta karasa wajensa,tasa gyelen ta ta shiga goge masa zufar,ya juyo suka hada ido,ta sakar masa murmushi tace..give it here mr boss ta rike spoon din dake hannunsa..
Ya girgiza kai,kije ki kwanta i will finish up in a minute..
Tace nooo its my job,ya kalleta,kafin ya sake mata serving spoon din hannunsa yace if you say so.Ta shirya musu dinning sannan ta juya zata fice..
Ya tsaida ita,dawo ki zauna,ta juyo suka hada ido,ya dauke kai yana cin abincinsa,taja kujera ta zauna,sannan ta diba abincin kadan taci,duk abunda takeyi a idon ridwan ya kasa dauke dubansa a kanta,bai san me yasa ba indai tana waje toh lallai hankalinsa sai ya dawo kanta.Suna kammalawa yace da ita,ki koma daki ki huta,ta gyada kai zata fice,yace,ki koma dakin da kika fito,tadan ware ido,yace a takaice,idan kina BQ ba wanda zai san halin da kike ciki,zatayi mgn ya wuce abunsa.
Da rana ya aiko ayman ya fada mata zasu fita kuma kada tayi wani girki.
Ta shantake a daki tana amsa kiran family n frnds,sunan inna ta lalubo tana tsoron kiranta,tasan tabbas sai tayi mata tambayoyi akan Ridwan..
Kiran innar ne ma ya shigo saratu ta rikice,ta dauka suka gaisa a sanyaye,ammani tace ya aikin naki?saratu tace lfy lau ina su dije da Ayla?
Ammani tace dije na makota,Ayla kuwa na gidan mami,saratu tace ayyah yanzu kuwa muka gama gaisawa da minal,a haka firar tasu ta kare ammani tayi mata sallama.Lumfashi ta saki ta mike taje tayo wanka,hijabi ta saka ta sauko zuwa BQ ta dauko kayanta ta saka.
Sai dare suka dawo gidan a lkcn ma se de ta hada tea tasha kawai da rana dan bazata iya girka komai ba,taso tayi musu dinner amma jin anyi warning dinta se ta bari kawai.
Tana zaune bayan ta idar da sallah ayman ya shigo dauke da leda.
Ya mika mata,daddy yace na baki,ta bude taga take away ne,tayi saurin kallon sa,a restaurant kuka ci abinci?
Ayman ya girgiza kai,no munje gidan uncle ne,se muka shiga restaurant muka siya miki naki.
Ta zauna tahau cin abincin,tana gamawa ta dauki sharar ta sauko kasa.Ridwan ta hango zaune a falo gaban laptop dinsa.
Har zata wuce abunta kawai taji muryar Amal kamar daga sama.Gabantane ya fadi tayi saurin lekowa taga Amal acikin screen din laptop din, tana ta zuba masa shagwaba.
Kirjinta ne ya buga tayi saurin juyawa,daidai lkcn amal ta hango ta a bayan Ridwan.Ta daure fuska tana fadin,honey who the hell is that!?
Ridwan ya juya yana kallon bayan saratu,yace my new chef of course bana fada miki ba.
Amal ta shiga yatsina,amma baka fada min mace bace ai!.Saratu tayi saurin barin wajen.
Ridwan ya daure fuska,miye damuwarki idan mace ce?
Amal tace,but Ridwan u know i hate any woman close to u.Yaja tsaki,what do u take me for huh? Meyasa baki da aikinyi ne sai kishin banza!
Kinyi tafiyarki kin barmu,so don't tell me nonsense !a fusace kawai ya kashe kiran cike da takaicin Amal.Amal a dayan bangaren gaba daya hankalinta ya tashi,daga ganin shape din bayan yarinyar da ridwan ya kira chef dins kawai ta tsorata sosai,tasan dole ne tayi kyau!
Cikin sauri ta kira hajja meena,nifa mom am coming back to Nigeria this week,hajja meena ta hau ta da fada sosai,amal ta fashe da kuka,i don't wanna loose my husband to any bitch mom,na hakura da neman kudin,i don't care about any bussiness!!!!!kashe gaba daya tana uba uban tagumi...
Instagram @ dee_bature
Please
Vote
And
Comments
