Team RIDSA 💖
'Bayan kwanaki biyu saratu taji saukin jikinta sosai,ridwan na kula da lafiyarta ,hakan kuwa ba karamin dadi yakeyi mata ba.
Kamar yau ma tana kitchen ne,ayman na falo yana kallon cartoon, ridwan ne ya sauko ka'sa yana fadin,my boy i have to watch news now ok,ya dauki remote control din dake kan center table.
Dai dai lokacin ne faruk ya kira saratu yana sanar mata za'ayi airing show din ta a tashar BBC news, wani irin dadi ne da farin ciki ya lullubeta,ta kwashi warmers da saurinta zuwa dinning dan taje ta kalla a online.
Tana shiga falon ta hango Ridwan na shirin canza tasha zuwa BBC. ..
Gabanta ne ya fadi,idan ya ganta a cikin show din yaya kenan!kashin ta ya bushe..Kafin tayi wani yunkuri har ya saka tashar abunsa...
Ayman ya mike ya fice dan baya kaunar news ko kadan.
Tana nan tsaye taga an dawo daga tallar rabin lkc za'a fara show din nasu...Ihu ta saki babu shiri ta zube a kasa..
Ridwan ya mike da sauri yazo wajen ta,yace lafiya?meya same ki?Saratu ta matse bakinta ju'ya ce ta dauke ni i have been feeling dizzy lately ta dafe kanta.
yace sannu,ki je ki huta kawai,ta gyada kai tana kokarin mikewa tace,oops i left something on the gas,ya tsaida ita i will finish up you go n rest,ta sake gyada kai,yana shigewa kitchen tayi dugu taje ta canza tashar zuwa aljazira,sannan da sauri s tayi dakinta tana kyalkyata dariya.'Washe gari tana compound zaune,waya take amsawa, ammar ne ya kirata yana sanar mata zai koma lagos,gate taga an bude ta hango bakuwar mota ce.
Tana shirin barin wajen taji an kwala mata kira.
Cikin firgici ta juyo sukayi ido hudu da Haydar,ya ware ido cike da mamakin ganinta.
SARATU! Am really surprised seeing you here,ya a'kai hakan ya faru ne?Saratu idanunta cike da kwalla tace,ya haydar i know am crossing my boundaries,haydar yaja lumfashi tell me what are you up too huh?
Saratu ta shiga fayyace masa komai.
Yace naji dadin hakan gsky,Allah ya kawo wa ridwan karshen wannan RASHIN GA'TAr da yake fama dashi.Haydar suka rungume juna cike da farin cikin ganin junan su..
Ridwan yace dude wlh ka canza kwarai,haydar ya kwashe da dariya,na kai ka ne?kai da yan mata har yanzu ke rurubin ka sukeyi basu san tsohun ka'shi bane kai..Ayman ne yazo da gudu ya rungume haydar,ya shafa kansa yana murmushi.
Bayan sun zauna ne saratu ta shigo dauke da tray,tana tafe ne gabanta na faduwa,haydar ya kura mata ido,akan side table kusa da ridwan ta ajiye bottle water da cup, ya dago yana kallonta,miss chef nayi babban bako yau,so please prepare a nice dinner for us...Ta gayada kai tana murmushi,ridwan ya daure fuska,baki iya gaisuwa bane ko?
Tace na iya mana,yace then why r not greeting him?ya nuna haydar dake sauraren su.Tace ina wuni sannu da zuwa.
Haydar ya amsa da lafiya kawai yana takaicin halin da saratu take ciki,ace wai yau ridwan ne ya manta da ita wacece a wajen sa?lallai dole ne ya taya ta fighting su dawo wa ridwan da farin cikin dayayi rashi.Kwana biyu suka wuce,ikram ta kira ta dan jin rihoto,saratu tace mata kada ta damu Allah zai taimaka musu.
Ranar wata lahadi,Ridwan da ayman suka fita shopping dinsu, sun fito zasu shiga mota Ayla dake tare da dije ta kwace tayi wajen su da gudunta..,a lokacin dije na can na cinikin rogo...Ayman yace look daddy its Ayla,ridwan ya kura mata ido ,ayman yace Ayla your anty is in my house, Ayla ta rike kugu,is not anty is ya Sarah,n she's in abuja haka inna tace min taje aikine.
Ridwan ya tsaya sauraren su kawai,yasan da wuya ne yaro yayi karya,toh me yasa bata fadawa iyayenta gaskiya ba?ko bataso su san irin aikin da takeyi.