chapter 27

2.4K 219 14
                                    

'Amal hankalinta a tashe ta kira haydar,dama yana kan hanyar zuwa gidan ne,yana isowa suka kwashi Ridwan zuwa asibiti,saratu gaba daya ta fita hayyacinta,tsoro,fargaba da dana sani ne duk suka dame ta,hijabi ta saka kawai itama ta samu me adaidaita yabi bayan su.

Emergency suka kai ridwan,dr ya shiga duba sa cikin gaggawa.
Amal dake zaune tana waya da hajiya layla ta hango saratu a rakube gefe ta hada kai da gwiwarta a durkushe,ta kashe wayar tazo ta tsaya mata a kaai.

   Ke wai wacce irin mayyace ne huh! Wane irin bad lock gareki?idan har kina kusa da ridwan toh fa shikenan babu shi ba zaman lafiya,kullum yana kan ciwo da wahala! Ki fita daga rayuwarsa mana har abada hakan sai yafi makale masa da kikeyi kina jawo masa musiba..

    Saratu dake ta zubar da hawaye ta mike daga tsugunnen da take,ta kalli amal cikin ido,bana tunanin kina da ilimin addinin ko kadan,kin manta duk abunda ya samu bawa toh jarabawa ce daga Allah?

  Amal ta daga hannu ta wanka mata mari,don't tell me nonsense you witch!get the hell out of our lives!
   Nurse ce tazo wajensu,ta kalli amal,pls kidan rage da'ga murya haka a asibiti kike...

Amal taja tsaki kawai,dr ne ya fito ya kalli amal sannan ya kalli saratu dake tsaye tana zubar da hawaye, yace who among you is his wife?

    Amal tayi saurin zuwa wajen dr,i am dr ni ce nan matarsa...
Doc ya kurawa saratu ido,ya kalli amal kije ki biya bills toh,ta gyada kai da saurin ta tana barin wajen.
   Dr ya karaso gaban saratu da gaba daya hankalinta baya jikinta,ta zurma duniya tunani sosai.

Yace sannu ko?ta dago da jajayen idanuwanta, tace yauwa da dashashshiyar muryarta.
  Yace na fahimci kema matar patient dinnan ce ko? Mata biyu ne dashi..
   Saratu tayi shiru,yace ki shiga ya farka kuyi mgn,ta ware ido ya farka ya jikin nasa dr?

   Dr yace ba wani damuwa he was just in a shock ne kawai,tace mun gode da kokari doctor sannan a sanyaye tayi dakin gabanta na faduwa ..

Dr yayi murmushi, shi bai san meyasa wasu matan kishi yake sanya su sabon Allah ba,ya gama lura Amal na musgunawa wannan yarinyar, ya girgiza kai yayi tafiyarsa.

Tana shiga ta hango sa kwance idonsa a lumshe,ta karasa wajen sa tana kallon fuskarsa,tausayin sa take ji sosai,shi de gaba daya rayuwarsa bai san miye jin dadi ba,ta dauki alkawarin zata shayar dashi gaba daya jin dadin duniyar nan,amma gashi yayi mata nisa yanzu..

   Kuka ya suboce mata,ta fara magana kasa'kasa,ban san dalilin daya sa na kasa hakura dakai ba duk wannan shekarun,nayi tunanin wata rana zamu sake kasancewa tare da juna,ta riko hannunsa,ina sonka tamkar raina,u asked who i am right, am your RIDSA,am Sarah your first love...

   Duk tunaninta ko barci ne ya dauke sa,tana dagowa suka hada ido dashi,tayi kokarin ja da baya...
  Taji ya rike hannunta gam,ta kura masa ido,kafin tace,am sorry boss..

Da murya mai sanyi yace,what do you think you are doing?
   Ta rikice tana goge idanuwanta, dai dai lkcn Amal ta fado dakin,ridwan ya sakar mata hannu da sauri..
Amal ta karasa ta rungume sa,am happy you are all fine now,but you scared me honey...
Yayi murmushi kawai idonsa na kan saratu da takeji kirjinta yayi mata nauyi,ta juya ta fice kawai daga dakin.

A waje sukayi karo da haydar,ya kalle ta cike da tausayi,ya jikinsa?tace da sauki,haydar yace yanzu miye shawarar da kikayi?
Ta runtse ido,sai munyi mgn da ikram,ya gyada kai,toh shikenan.

Can gidansa ta koma,ta kwashe kayanta tas,sannan ta kira ikram,ikram hankalinta ya tashi,tace kin tabbatar ya Ridwan bai gane ki ba kuwa?saratu cike da takaici tace,he didn't recognized me ikram,am going  back home yau din nan!
   Ta rubuta masa resignation letting dinta ta ajiye kan bed taja takwatin ta ta fice.

A kofar gidansu ta iske minal na fira da saurayinta WALEED ta gaishe dashi a sa'ke cike da tsonaka yace,kawarmu daga ina haka?

Minal ta hararesa wato ka manta na fada maka taje abuja wani aiki ko?
Waleed yayi dariya wasa nakeyi ai,sannunki da dawowa,saratu tace yauwa inlaw me,minal ta amshe trolley din saratu muje ciki ki huta kawalli nayi kewar ki dayawa,saratu tace anyi haka?tana kallon waleed,yace ai kinsan gimbiyar kawai kuje ya shige motarsa yayi tafiyarsa.

Sai datayi wanka tayi sallah sannan ta zauna a tsakar gida tana cin abinci,ammani na bin ta kallon tuhuma amma ta share,dije tace kai saratu abujan nan fa ta amshe ki wlh,minal tace ai dije ko ke kikaje abuja sai kin canja zuwa fara kal dake,dije ta kai mata duka,wai me kuka mayar dani ne!ja'irai kawai..

Ayla ce ta shigo gidan,tace oyoyo ya Sarah na ta dawo,saratu ta rungume ta tsam,tace na dawo Ayla ya rashin ji?
Ayla tace ai bana yi yanzu,na zama an matah ko dije?
Dije tace ni cire ne cikin karyarki.

Washe dari ammani ta kasa hakuri,da sassafe saratu na zaune tana fire dankali,tazo ta zauna kusa da ita,saratu ta mike tana fadin,bari na dibo ruwan zafin dana daura..
Tana dawowa ammani tace,fada min gsky saratu daga ina kike?

Gabanta ya fadi,tace daga abj mana inna,ammani tace ki fada min gsky saratu kin hadu da yallabai ko..
     Saratu gabanta na faduwa ta mike tsaye,na fada miki inna ni fa abj naje,ina zan hadu dashi?nasan a wacce duniyar yake ne,ta karashe mgnr muryarta na rawa,ammani ta gyada kai, a zuciyarta tace Allah yasa yana lafiya,a fili se tace,na sha fada miki ki cire shi daga cikin ranki saratu. ..
Kwalla suka ciko idonta, ta shige daki da saurinta tana boye hawayenta.

Kwana biyu tsakani,ta koma aikinta,she is always busy bata so ko da minti dayane ta zauna tunanin ridwan.

      Ayla ce ke ta rusa kuka,ramla tace,haba Ayla an fada miki abbanmu zai je miki parents day din ki bar kukan haka,mami dake zaune kusa da su ta jawo ta jikinta,haba Ayla miye abun kukan?
Ammani tace ku barta dan Allah duk shagwaba ce kawai,Ayla tace,inna nifa babana aka ce yazo ba abbansu  su ya ramla ba...

   Gaba daya suka tsaya suna kallonta,ammani ta rasa me zata ce..
Dai dai lkcn ammar ya shigo a ajiyen shi,yace come on Ayla your daddy is here....
Tayi gudu taje ta rungume sa,yes yes yes ya Ammar is back!!ta hau rawa,suka hau yi mata dariya.

Washe gari kuwa aka shiryata tsaf,saratu ta fito cikin sauri zata fice aiki ammani ta tsaida ita,kada ki manta dan Allah karfe sha biyu ammar zaizo kuje mata kinji?saratu tayi dan jim,sannan tace toh kawai ta fice abunta.

A wajen ridwan kuwa ya samu sauki,kamar yau yana falo ne a zaune Amal da ayman sun fita,ya mike yazo kofar dakin saratu ya tsaya,daga bisani ya shiga,yabi dakin da kallo yana shakar kamshin ta,hango takarda yayi kan bed,ya dauka ya karanta tsaf.
     

Please
Vote
Share
And
Comments

Rashin Ga'taHikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin