'A zaune ya tarar dasu duka a falon hajiya layla, fuskarsa kamar garwashin wuta yace a harzuge,mommy why!
Why did you have to humiliate Sarah like that! Ta mike tsaye cike da fusata, Ridwan, ni kake wa tsawa haka! wuyanka ya isa yanka ko? Sannan ina so kayi wa wannan ballagazar matar taka fa'da ka koya yarda da zata san yarda ake daraja mutane ba, tunda a gidan su ba'a bata tarbiyya ba! ..Ridwan yaja lumfashi, you are not my mother! So banka dalilin da zai sa ki matsa wa matata ba, shes not ur inlaw why the bully! tunda kina nuna min tsana da tsangwama ina kyele ki mai yasa sai kin dorawa diyar mutane tsanar itama!
Sannan ya kalli su Amal, duk ranar da wadan nan mutanen suka sake shiga harkar matata bazan kyalesu ba, i do not care the hell what they are to you!Ya juya zai tafi hajiya layla ta tsaida shi da cewa..
Kana wasa dani Ridwan ina tunanin ka manta yarda na hallaka mahaifiyar ka ko!!!!
Gabansa ya fadi, take idanuwansa suka kada sukayi ja.Ya juya kamar wani kumurci, idan har a baya bana da karfin kare mahaifiyata daga mugun sharrin ki yanzu yayi murmushin bakin ciki, bazan taba bari ki taba min matata ba na kyaleki..
Bai jira mai zata ce ba ya fice abunsa....
Tunda ya fito yake neman lumfashi ya rasa, gaba daya jikinsa rawa yakeyi, da kyal ya karaso gidan sa.
Hajiya da saratu na zaune a falo sunyi zugum'zugum, ikram na fitowa daga kitchen rike da cup din ruwa a hannunta ta hango sa sai jan kafarsa yake yana kokarin shigowa ciki, ta saki cup din tayi gunsa cikin gudunta, ya Ridwan are you okay!Da sauri su hajiya suka yo kansa suma, saratu duk ta rikice, ta riko sa tana kara fashewa da kuka, tamkar ba Ridwan din da ta sani bane, gaba daya ya canza, jikinsa duk tsikar jikin sun tashi..
Hajiya sai sallalami takeyi, ikram jeki maza ki kira kabiru..
Da gudu taje ta dauko wayarta, hajiya, saratu da indo da kyal suka kawo sa cikin falon, gaba daya hankalinsu a tashe yake, Mom Mom kawai yake fada da muryarsa da duk ta dishe abun tausayi.Saratu ta mike kamar mahaukaciya, tasa hannu cikin aljihunsa ta dauko wayarsa, mom ta nemo a cikin contracts kai tsaye ta danna kira...
A lokacin kuwa ammani na zaune a gidan su hafiza se fira suke sha, dije ce ta shigo gidan bako dan lullubi tace, wai ke ammani mai yasa ne baki ajiye wayarki a kusa dake ne, ina makewayi amma nake taji tana kuka.
Ta mika mata wayar tana saka hannu cikin kwanon dake gaban umman hafiza, ina kika samo zogaye?Ammani ta dauki wayar cike da murmushi a tunanin ta ko yallabai zai mata tunin takardun saratu ne.
Muryar saratu taji cikin shashshekar kuka.
Inna inna Ya RIDWAN babu lafiya! Inna mutuwa zayyi ko! Na shiga uku na..
Cikin sauri ammani ta mike, gabanta na dukan uku uku, yallabai ba lfy saratu? Ya akayi hakan ya faru ba ya samu lfy ba?Saratu ta shiga bata lbrn yarda komai ya faru, cikin tashin hankali ta shiga gayawa saratu yarda zata taimake sa kafin likitan sa ya karaso, ita kuwa a take ta kira inusa ta sanar masa da cewa zata je kano yallabai ba lfy.
Saratu cikin gaggawa tazo gaban sa, hannunsa ta kamo ta rike kam sannan ta kalli indo, je ki kawo min sabon towel da ruwan dumi, hajiya ta buga uban tagumi, ikram ta dawo tana fadin su daddy na zuwa da dr, saratu ta shiga goge masa fuskarsa tana murza hannayensa.
Cikin lokaci kalilan sai ga dr da alhaji kabiru sun karaso.
Dakin sa aka kaisa sannan dr ya duba sa, yana masa allura ya dawo hayyacinsa, barci ya dauke sa.
Ya kalli alhaji kabiru, ina ammani ne? Nasha fada muku a daina tuna masa da baya dayawa, his Trauma can easily come back, he have to completely over come it.
Alhaji kabiru ya jinjina kai, hajiya ta shafa fuskarsa bawan Allah, Allah sai ya maka sakayya..Cikin dare ne ammani ta iso gidan, hajiya ta shiga labarta mata yarda komai ya faro, tausayin yallabai takeji mutuka, ta shiga dakinsa a nan ta tarar da saratu a zaune a tasa sa a gaba tana kallon sa, ammani ta dafa ta, tayi firfigit ta dago da kanta.
Rungumeta tayi tana kuka, ammani ta shiga lallashinta, tace je ki kiyi sallah kici abinci ki kwanta zan kula dashi, saratu ta gyada kai sannan ta mike ta fice.