""""''Dije ta kalli saratu Tana toshi hancinta hade da yatsine fuska, ke dan ubanki anan kikayi kashin kenan? Saratu tayi rau rau da ido tana matse bakinta, dije ta kara toshe hancinta sannan ta karasa ta fisgota tana fadin, wannan sakarcin naki yayi yawa saratu yanzu wannan dan ruwan namu dana adana shi na abincin dare shi zansa na wanke miki kashi, yarinya sai kace ku'da! mtsww, lantana ce ta banko kofa ta shigo, dije ta dafe kirjinta tana fadin, ke haihuwar jahiliya ko sallama bakiziyi ba sai dai kawai na ganki? Lantana ta rike kugu, lallai kuwa dije kinji kunya wallahi, dije ta maida wa saratu wandonta sannan ta dawo kusa da lantana tace, naji kunya? Ai ba a kaina aka fara jinta ba, lantana tace yanzu saboda bakin cikin da kike min shine kika zuga ni naki neman aikin a burni ke kika tura ammani ko? Dije ta kwashe da dariya, wai dama nan kika dosa, lantana ta zuba mata ido, dije ta jata zuwa daki, kwantar da hankalinki wannan aikin na burni ai duk bauta ce sukeyi acan, bakiga ammani bane? Gaba daya jikinta ciwo ne da sawon duka, ni dama na kaita ne dan mu dan samu nakaiwa bakin salati, lantana tace kai haba? Dije tace kwarai kuwa, suka kwashe da dariya a tare.
""""Tsaye take a bakin kofar sa, gaba daya rayuwar yaron tausayi take bata, Rashin gatar sa tayi yawa, duka satin biyu kenan da fara aikinta, amma ta soma fahimtar al'amarin gidan, ta leka a hankali ...
Can ta hangosa rakube a kan kujera yana kallon TV, saukowa tayi kasa anan ta tarar da lami tana ta faman hada abincin dare, ta kalli lami, naji kince kawun ki na waje yana jiran ki ko? Lami tace eh shiya nake ta sauri ma kin shi din ba baya da hakurin jira ne, ammani tace toh kinga barshi na karasa miki kawai ta amshi albasar dake hannun lami, lami ta saki murmushi jin dadi nagode ba, ammani ta kalli gaba daya abinci, taja lumfashi yanzu ace kullum mutum yana fama da cin abinci daya kenan?
Ta gyara daurin zanin ta sannan ta shiga girka abincin mu na gargajiya, tayi kala uku sannan ta shirya tsab ta kai bakin kofarsa ta ajiye, ta koma gefe ta zauna tana jiran taga ya fito, ai kuwa sai gashi, ya duka a sanyaye ya bude duka abincin, gani tayi kawai yayi jifa da towun ya kuma daukar dan wake ya gefar, hankalin ammani ya tashi, yana bude dish din fankasu da miyan ganye sai taga ya sauke lumfashi ya dauka ya shige dakinsa, ammani ta sauke lumfashi sannan taje ta kwashe sauran ta gyara wajen, da safe ma haka ta koma ta tarar gaba daya ya cinye komai, murmushi tayi tana kara tausaya wa rashin gata da kulawa irin nasa.
"""""'Kwanaki sunja rayuwa kuma na tafiya cikij jin dadi a wajen dije dan kuwa a yanzu harta ja jari abunta, albashin ammani dama ba ita ke amsa ba, salame ke amsa kuma ta kaiwa dije shi duka, ko pant bata siyawa saratu ba wai tunda karatu uwarta tace zatayi toh sai lokacin shigar ta makarantar yayi sai a fara kashe mata kudin, shi kuwa inusa sun shiga jeji neman itace.
Wata biyu kenan da fara aikin ammani a gidan alhaji kabiru, a yanzu kam harta haddace abincin da ridwan yafi so da safe, rana harma da dare, lami tayi mamaki kwarai da gaske dan kuwa ba'a ganewa ridwan ko kadan, idan yau yafi cin soyayyen kwai toh gobe dafaffe zai fi ci.
ana cikin haka ne watarana kwatsam sai ga hajiya layla tazo gidan, tazo ta sanar musu cewa alhaji yana gari kuma zai shigo ganin dansa da yamma.Ammani da lami sun shirya masa abinci na gani na fada, ridwan na kulle a dakin sa kamar kullum ammani ta hango hajiya layla ta haura sama, hakanan taji hakan bai kwanta mata ba dan ta gama fahimtar cewa ridwan ba dan hajiya layla bane ba.
Tana kokarin hawa benen ne taji ya saki wani irin ihu, da sauri ta karasa tana labewa, ta hango hajiya layla na dukansa kamar jaki, tana fadin, idan har mahaifinka yazo ka sake ka fada masa kaji, i will not take it lightly with you! Ammani ta rike baki da sauri ta sauko kasa tana nishi.
Alhaji kabiru ya iso dan shi dan kasuwa ne baya wani zama a kasar, yaji dadin ganin ammani bahaushiya cikin masu kula masa da dansa, yaje wajensa amma ridwan ko motsi beyi ba kamar ko yaushe, yarda yake a kwance idonsa na kallon celling har babansa ya fita bai motsa ba, alhaji ya fakaici idon hajiya dake amsa waya ya kira ammani gefe yana fadin, ya sunanki? Tayi saurin sauke kanta kasa sunana ammani, yace toh madallah ina rokon taimakon ki ina fatan zaki kula mini da ridwan da gaskiya da amana, hakanan naji kin kwanta min, ammani tayi mamakin furucinsa, yasan cewa dansa a cikin wannan halin ya barsa a haka? Tana tausayin ridwan kwarai da gaske, ta kuma lura alhaji ma kamar tsoron hajiya layla yakeyi, tace babu komai ai aikina ne, alhaji ya sauke lumfashi nagode kwarai, gobe zan aiko Secretary dina zai kaiki ki siyo kaya na kirki ki ringa sakawa, dan likita ya fada mana a kula da tsaftar masu zama a kusa dashi, dan hatta ko dattine zai iya tashin ciwon sa, inaso ki zama garkuwa a garesa, ammani tace zanyi hakan amma... Alhaji yace kada ki damu zan kara miki albashi bayan wanda layla take baki, ammani tace ba haka nake nufi ba, inaso na fahimci ciwonsa ne, alhaji yaja lumfashi zansa a miki bayani, daidai lokacin hajiya layla ta leko fuska a daure, ke! Mai kikayi anan? Ammani tayi saurin ja da baya tana fadin, dama dama, bata ankara ba taji saukar mari, da sauri ta rike kuncin ta, alhaji yace miye haka layla? Ta daga masa hannu kawai ta fice abunta.
Dije ta kalli kwanon taliyar dake gabansu sannan ta kalli saratu dake ta sidar hannunta, ke saratu! Dan iyayenki kafin na fito bayin ne kika cinye wannan taliyar?yarinya sai kace ga'ra! Saratu tace inna Allah ko..... bata karasa ba kawai taji saukar dundu a bayanta,dije ta hankade keyar ta maza jeki wajen dauda ki amso min shayi ja'irar yarinya... dai dai lokacin ne ammani ta shigo dauke da sallamarta.....
Please
Vote
And
Comments
Follow on instagram @ dee_bature
YOU ARE READING
Rashin Ga'ta
General FictionRashin gaa'ta is a hausa written story, follow and vote