Chapter 8

3.3K 221 4
                                    



'A take taji komai nata ya tsaya cak, wane irin yanayi mai wuyar fassarawa ne ta shiga...

  A bangaren Ridwan kuwa, gabansa ne ya fadi a take, yana kokarin dauke kansa daga kallon inda take yaga taja ta tsaya cak a kan titin ga motoci sunyo kanta sai hon akeyi mata amma ta daskare a wajen.

     Kamar ya basar sai kuma ya yo wajenta cikin Wani irin saurin yaje ya kamo hannunta ya fisgo ta ya janye daga kan titin..

   Shock ne ya mamaye musu hannayensu juya ga duk jijiyoyin jikinsu, sai sannan ne saratu ta dawo hankalinta, ta kurawa Ridwan ido kamar zata cinyesa, shi kuwa fuskarsa ba walwala ya sakar mata hannu da sauri kamar ya tuna wani abu ya juya abunsa, dai dai nan haydar yayi parking mota ya shige suka fice.

  Hafiza ce tayi saurin zuwa ta riko saratu da kafafunta suka kasa daukarta, bata taba ganin mutum mai kyau kamar Ridwan ba ya rikita mata lissafi sosai, hasken sa ya tsoratar da ita, hafiza tace, lafiyar ki kuwa saratu? Ya za'ayi ki wani ja ki tsaya akan titi kamar wacce ta gaji da duniyar, saratu kasa mgn tayi dan gaba daya tunaninta baya jikinta.

Ridwan ya sauke haydar a junction, tunanin yarinyar nan yake, mai yasa baiji  komai bane daya taba ta?sema wani energy dake following a jikinsa, ya  kallo hannayensa dake kan sitiyari, da tunanin nan har ya karaso gida, mutane ya tarar a gaban gate dinsu cike, ya tabbata masu jiran daddy ne dan kullum juma'a yana bayarda sadaqa, yadan sauke lumfashi yana tunanin ko ya fita ya same su ne, dan daddy ma yayi tafiya zuwa abuja jiya, ya kashe motar ya fito, gaba daya sukayo wajen sa suka lullubesa, ga mamakin Ridwan sai bai ji ko mai ba, heartbeat dinsa normal haka ma baya tattare da wani anxiety, gashi tunda ya fito gida baisha meds dinsa, toh taya hakan ya faru? Dama meds dinsa bayan ko wane 3hrs ne drs suka ce ya sha, dan ya taimaka masa wajen cudanya da mutane, maganin zai daidaita masa heartbeat dinsa, sannan ya kuma cire masa anxiety attacks din da yake samu...

Hannu suka shiga mika masa, tsoro yakeji ya tabasu nasa, amma kafin ya ankara sai ji yayi sun shiga riko hannunsa suna gaisawa dashi, yallabai ina wuni? , wani irin mamaki ne ya lullubesa, babu wanda ke iya tabasa ciwonsa bai tashi ba se mom dinsa, itace kawai zuciyarsa ta kwanta da ita saboda shakuwar da sukayi, farin cikine ya mamayesa, ya shiga rabon kudi yana sakin murmushi..

Tunda ya shigo falon yake kwalawa Mom dinsa kira, ikram ce ta fito daga dakinta tana fadin, ya Ridwan nannay Ammani na sashen su daddy, Ridwa yayi saurin zuwa wajen ikram din, taja baya cike da mamaki dan bai taba tsayawa so close da ita haka ba, ji tayi kawai ya rungume ta yana dariya, ta dago da sauri tace, ya Ridwan oh my God are you all healed now!!!!

  Ridwan yayi tsalle cike da murna, i think i am little sis!
Ammani ta shigo ta kofar kitchen, da mamakin murnar da Ridwan keyi, tace Yallabai wani abun farin cikin ne ya faru?

  Ridwan yayi saurin  fadin, mom na warke! Mom bana jin komai yanzu! Mom na shiga mutane! Mom, mom
   Tayi dariya cike da farinciki sosai, tace ban fahimce kaba yallabai, yaja hannunta suka zauna kan kujera, ikram ma ta zauna tana murna tell us bro am eager, Ridwan ya shiga basu labarin yarda komai ya faru.

   Ikram tace, lah ya Ridwan you meeet an angle!
Ridwa ya danyi jim, what an angle?
Ikram tace, eh mana! Ba sai da ka taba ta bane ka samu lafiya! Am shes the reason..

Ridwan yadan yatsine fuska, ni Allah ne ya bani lfy dont talk rubbish,
Ammani dai sai jinsu kawai takeyi, farin ciki sosai ne ya lullubeta, tace sai ka kira mahaifinka ka fada masa ko?
Ridwan ya mike bai amsa ta ba kawai ya saura sama abunsa.

Tunda saratu ta dawo kauye gaba daya hankalinta yaki kwanciya, kwana take mafarkin Ridwan, tun dije na shareta idan bataci abinci ba hardai abun ya fara damunta dan ko fita yawo ma ta daina, ta same ta kwance da rana tsaka a tsakar gida.

Rashin Ga'taTahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon