chapter 21

3K 177 5
                                        

'Washe gari sukayi musu sha tara ta arziki sannan mansoor da kansa ya kai su airport, minal tace dashi mun gode sosai ya mansoor,ya saki murmushi babu damuwa minal idan na shigo kano inshaAllahu zan neme ku mu gaisa ko?

   Saratu dai hankalinta na can wajen amsa wayarta,tana kashe kiran ta kalleshi,mun gode kwarai mansoor ta karashe mgnr da smiling,yace your welcome Sarah,yarda yake wani kallon cikin idanuwanta ne yasa ta dauke kai da sauri taja hannun minal muje gashi can an fara announcing.

Karfe biyar na yamma suka iso garin kano,direct mai daidaita suka samu har cikin anguwarsu.
      Murna sosai akayi da ganinsu,wajen ammi suka sauka wato gidansu minal kenan,dama Ayla na can wajen su ramla,tana ganin su tayi wajen minal,tace oyoyo ya minal dina,saratu ta dan harareta,nifa?

Tayi wajen ta itama,my ya Sarah is back kin siyo min sweet?
Saratu taja chicks dinta,shazumami kawai ban siyo ba.

        Sai da sukaci abinci mai rai da lfy dan ammi gwanace wajen girki sosai,saratu ta mike tana cewa,ke minal ni zan dan shiga gida wlh a gajiye nake.

    Minal ta kalli ramla dake kallon TV ramla dauki kayan sarah kikai mata gida,ramla tace wai se yaushe zaku bamu tsarabar tamu ne?
Sarah tayi dariya ku bari se da safe yanzu kam we got no energy,minal tace Wlh bana son halin yaran nan,se kace kun bamu ajiya daga durowar mu se asking tsaraba sukeyi.

  Har cikin gida ta rakata suka gaisa da ammani da dije,dije ta hau tambayarsu wai ance habujan nan kamar kasar waje take ko?
   Minal ta kwashe da dariya,ke dai dije bari kawai se kinje ki gano wa idon ki.

Bayan sati daya yau weekend ne bata da aiki,dan haka tayi shiri ta samu ammani a tsakar gida tana tsintar wake,bata sanar mata haduwarta da ikram ba har yanzu dan tasan hankalinta ne zai iya tashi kawai.

   Tace inna wai ina dije tayi ne,naga ta dauki Ayla abokiyar yawon ta tun safe ban sake ganin su ba?

Ammani tace,wa! Ai suna kasuwa wai zata shiga siyan kal'wa kawar ammi ke so ayiwa diyarta daddawa wacce zatayi aure nan Zarah ko?

Saratu tace,eh Zarah ta kawo min katin gayyata ma ni da minal.
Ammani tace,sai kuyi shiri kam dan naji ammi tace har sun fitar da anko,saratu na kokarin ficewa tace,zamuyi bari naje wajen minal din.

A compound dinsu taga motocin da bata shaida ba,ko abbansu ne ya dawo?ta tambayi kanta,kafin tabi ta kofar baya ta shiga ta kitchen.
     Minal ta iske na girki a kitchen din,tace wow ashe na zo a sa'a yau kam, shinkafa da wake my favorite, minal tayi dariya ai kinsan ba ke kadai ce ke son rice n beans din ba ko?
   Saratu ta zauna kan kujera tana fadin,daga ni se Ya Ammar ne masoyan rice n beans,minal tace yanzu kike mgn ya ammar nake dafawa..
Saratu ta bude baki,kai dan Allah ashe yau ne zai dawo?ko ya kira ya sanar min ma ta tabe baki.

Minal tazo taja hannunta,can falo suka shiga inda ammi ke zaune dasu ramla,tayi saurin gaishe ta,ammi tace ,kodai bakwa girma wlh...
  Minal tace,ammi wai ya ammar bai fadawa sarah ya dawo ba shine zan kaita su sulhunta ko,sukayi dakin sa.

       Bude kofar sukayi kawai da sallama suka shige ciki .
A lkcn ammar na tsaye gaban wardrobe dinsa yana duba kaya,juyowa yayi yana kallonsu cike da fara'a.
   Saratu ta daure fuska tana rike kugunta,minal tayi masa signal da ido,yasan laifin sa dan haka yazo gabanta ya hade hannayensa biyu.

    Am so so sorry sis surprised nake so nayi miki ne,saratu tadan kallo fuskarsa,kyakkyawane ammar, kalar fatarsa caramel color ce mai wahalar samu,dogone sannan baya da jiki,yana da kananun idanuwa da dogon hancinsa mai kara masa kyawu,duk a cikin gidan su minal Ammar yafi su kyau.

      Ta lumshe ido ta bude,toh shine zaka fadawa wannan? ta kai wa minal duka,minal tayi yar ka'ra,kefa ta daban ce mai yasa ya ammar ze min surprise ta kashe mata ido daya,saratu ta harareta,ammar yace hope am forgiven? Ta gyada kai tana murmushi yace yauwa ko ke fa sis,ya zauna kan bed yana nuna musu tsarabar da yayi musu,cike da murna sukayi masa godiya.

Ranar zungur suna wajen ammar,sallah kawai ke tashin su daga firar da sukeyi,ammar mutum ne mai ji da kansa ga miskilancin tsiya, amma idan yana gaban minal da saratu sai ka rantse da Allah mai saukin kai ne shi.

Washe gari ya kaisu har gidansu zarah suka siya anko,shine ma ya biya kudin,daga nan gidan tela sukayi,style iri daya za"ayi musu.
  Da yamma kuwa Ammar ya suri Ayla dasu ramla suma yakai su siyan ice cream.
  
Ranar bikin zarah ne ikram ta kira saratu,tace sun shigo garin kano ko zasu iya haduwa?,saratu tace da ita yanzu zata wani biki ne amma gobe inshaAllahu zataje su gaisa,ammar ne ya tsaya a gefenta,yace u look beautiful... ta saki murmushi har na kai ka?nasan se ka rikita yan mata yau din nan,ammar ya kwashe da dariya kin cika zolaya sarah,ke bazan rikita ki ba kenan ko?
Zatayi mgn minal ta karaso suka shige mota suka tafi.

Dinner party ne wajen ya hadu sosai,su saratu sukaje wajen amarya da ango suka gaisa dasu ammar dama shi abokin angon ne dan haka nan suka barshi sukaje neman wajen zama,minal ta mike tace ina zuwa pls sarah hango wasu frnds dinta da tayi.

    Saratu na nan a zaune wata mata dake kusa da ita da yaronta suna cin abinci,yaron nata kallon saratu dan haka se ta mika hannu,mashaAllahu ya sanun sa,maman tayi dariya sunan sa Ridwan...

Gabanta ne yadan fadi,nice name Allah ya raya shi,drink din dake hannun yaron ne yadan bata mata kayan jikinta ,maman ta hau bata hkr tace babu komi bari naje na samu ruwa na goge.
    Can bayan hall taje wajen masu ra'ba abinci,ta dauki robar rowa ta fito waje.

   Tana cikin goge kayanta ta hango wata taso ta shaida ta..
  A tsarace ta ware ido robar hannunta na faduwa akasa.
AMAL ta fada bakin ta na rawa,ganin tayo wajenta se tayi saurin gudu ta boye wajen wasu flowers dake can baya,lumfashinta na fita da sauri sauri.

     Wani katon kadangare ta gani wajen kafafunta, taja baya da sauri tana kokarin faduwa a tsorace sosai.
   Ji tayi an riko ta cikin sauri ta fadon kan mutum.
A tsorace ta kira sunan Allah,tana ture sa da karfin ta..

   Are you okay?
Taji amon sautin muryarsa cikin kunnenta,wani irin yanayi ta shiga da kyal ta dago tana binsa da kallo kamar taga fatarwa..
Idanuwanta kamar zasu zazzago...Ridwan ta fada a cikin zuciyarta da sauri kodai mafarki takeyi ne....

   Shi kuwa kallon rashin sani yake binta dashi,yasha gayunshi ya wani kara gogewa kamar bashi ba da gani yana cikin hutu sosai.
   Saratu tayi mutuwar tsaye,ya sake maimaita question dinsa,hey are you okay?

   A take ta gane cewa bai ma shaida ita ba,wani irin kululu ne ya tsaya mata a wuya,idonta ya ciko da kwalla,taja baya da sauri sai ji tayi an riko hannunta.
Minal ce,ta kalleta lafiya sarah mai ya kawo ki nan?ina ta faman neman ki..
   Ridwan ya juya kawai ya wuce abunsa yana sake waiwayon ta,whys she looking scared????
  Yana shiga hall din Amal tayi saurin zuwa ta rike hannunsa,sweetie ina ka shiga ne i have been looking for you since?
Ridwan ya shafa fuskarta,i went outside to ans an urgent call..
     Minal taja saratu suka dawo cikin hall din,zaunar da ita tayi tana mika mata robar ruwa,are you alright?
Ammar ne ya karaso wajen su,ya kalli saratu ragguwa kawai hala har kin gaji ne?
  Sarah tayi murmushin ya'ke kawai,idonta na sauka kansu Amal da Ridwan dake manne da juna..
Ta mike zumbur tana fadin,minal muje gida,kinga har tara tayi inna zatayi min fada..
  Cike da mamakinta suke kallonta,ammar yace calm down muje muyi musu sallama ko?
     Tana tafe tana kallon su Ridwan. ..
    Dago kan da zayyi shima sai suka hada ido..
   Ya kura mata ido shima...
Amal dake ta masa mgn taji shiru dagowa tayi ta kallesa,ganin hankalinsa ma gaba daya baya wajen ta tabi kwayar idonsa da kallo dan ganin miye ya dauke masa hankali haka...

Rashin Ga'taWhere stories live. Discover now