""Ridwan yayi saurin kallon hajiya layla cike da tsananin firgita,gaba daya mamaki ne sosai ya rufe sa,wai yau shine hajiya layla ke bawa hakuri tana neman yafiyar sa,oh Allah mai iko,bai taba tunanin zai iya yafe mata ba,amma ganin ta a gwiyoyinta sai zuciyarsa tayi sanyi,yasan cewa ko ba komai taga isharar ubangiji.
taja lumfashi mai dumi kafin tayi gathering courage dinta ta sanar dashi mgnr auren da takeso yayi,ya dago da sauri yana kallonta dan ba karamin mamaki yaji ba,ita dake son Amal kamar ranta?
ikram ce ta shigo dakin ta dauke da cup din juice ta zauna itama, a nan suka hau convincing dinsa da kyar ya amince ba dan komai ba sai dan shima din ya gaji da irin zaman da yakeyi da Amal,ikram tayi masa kashedi akan kada ya sanar wa amal,su bar komai a tsakanin su.'Washe gari kuwa da karfe 2 na rana aka daura auren Ridwan da saratu a karo na biyu, ango na can gidansa tamkar ba wanda ake wa aure ba,dan shi kam babu wani abu da yayi a wannan auren komai su ikram ne ke yin sa.
Amal ce makale a jikinsa tana masa shagwabar ta,wayar sa dake gefenta tayi ringing, ta yamutsa fuska tana mika masa wayar,gashi mommy ce,ya amsa yana janyewa daga kusa da ita,okay kawai ya fada sannan ya kalli amal din dake cika da batsewa,yace mommy na son ganina ne i have to go now,ta mike zumbur,wai maike damun wannan matar ne huh? Ita fa ba mahaifiyar ka bace mai yasa take wani bossing dinka haka kwanan nan,wato duk ina tsanar da take maka tayi ne?
Ridwan ya daure fuska yace,wato kin fi so kiga tana tsanar ta'wa kenan ko?me yasa bakya son zaman lfy ne huh!
Amal ta juyar da kai gefe,i didn't mean that,yaja tsaki,ni zan fita and possibly bazan dawo yau dinnan ba,amal kamar ta fasa ihu dan kuwa boka ya bata wani magani wanda takeson amfani dashi yau din nan idan har yakai gobe toh fa bazai yi aiki ba.
Ridwan ya fice abunsa cike da jin haushin Amal,shes so fucking annoying.
A wajen saratu kuwa,mansoor ne da haydar suka zo daukar amarya,ba wasu jama'a sosai dan minal ce kawai kawarta,mami kuwa ita ce ta kai ta har dakinta dan dije cewa tayi Allah ya tsare ta.(sallah babu alwala😂)
An kaita wani gidan ridwan dake cikin gari madaidaici ne amma ya hadu shima ba laifi,dan ikram da hajiya layla sai da suka kira masu gyaran gida aka gyare shi tsab ba karamin kudi suka kashe ba.
Da kuka sosai saratu ta rabu dasu minal,haydar ne ya shigo bayan sunje sun mayarda su minal din gida,ya zauna a gefen ta,gabanta nata faduwa dan kuwa har ta fara tunanin ko haydar dinne ya aure ta,ridwan bai amince ba.
Haydar yace,lallai ba wanda ya isa yayi wa Allah shishshigi,wato gashi yanzu ya sake hada ku a matsayin mata da miji,saratu ta dago ta kalle sa,yace dama hajiya ce tace na baki wadan nan ya miko mata ledar dake hannunsa, tasa hannunta dayaji jan lalle ta amsa,haydar yace,tace ki ringa basa duk safe da yamma,wani dr ne daga America yayi prescribing dinsu,insha Allah za'a dace.
Ta saki lumfashi Allah yasa,ya mike yana murmushi jin ana kiran wayarsa,yace ina tunanin angon naki ma har ya karaso,and yes,ikram ta dauki AYLA zata zauna da ita har Allah yasa ridwan ya samu lafiya,saratu tace toh ba damuwa.
A waje suka hadu da ridwan yana zaune cikin motar sa,haydar ya bude ya shiga.
Mai kake yi anan baka shiga ciki wajen amarya ba?Ridwan ya yamutsa fuska,kasan ni fa mata tsoro suke bani,duk da mommy tace wannan ta daban ce amma hankali bai kwanta ba wlh.
Haydar ya kwashe da dariya,kai abokina wlh mata kowacce da irin halinta,kai dai Amal ce kawai ka sani,amma ni madam dina ai Alhamdulillahi.
Ridwan yace ai kai kam ka dace dan kai dan ga'ta ne,haydar ya kwashe da dariya,yace pls ka shiga daga ciki ango kasha kamshi dont keep her waiting,ridwan na shirin fita haydar yace,kai tsaya! ya ban gan ka da leda ba haba abokina,ridwan ya hararesa ni fa nan daga wajen mommy nayo nan,haydar yace muje mu siya yanzu i know of a good place.'Saratu na nan a zaune shiru,ta mike taje ta leko window taga babu mota a waje wayam,ta dawo dauke da damuwa ta zauna tana buga uban tagumi,gyangyadi ne ta farayi dan kuwa kwana biyu bata samun barcin kirki,salloli takeyi dan Allah ya zaba mata mafi alheri.
Ridwan ya shigo gidan tsit ko ina yayi shiru,ya shiga dakin farko babu kowa a ciki,na biyun ya bude a can ya hango ta a zaune tana ta sharar barcin ta,ya karasa ciki yana jan tsaki,ledar hannunsa ya ajiye yayi tsaye a kanta,gaba daya fuskarta a rufe take da mayafi,yana kokarin juyawa ya fita ,dadin barci ya kwashe ta,tayi kamar zata fado dan batayi balance ba...
Cikin hanzari ya taro ta,fuskarta ta bayyana,cike da tsananin mamaki yake binta da kallo,ya dauke ta cak ya gyara mata kwanciya akan bed,sannan ya zauna yana kare mata kallo,wai miye connection dinsa da wannan yarinyar ne?
Tunani ne ya dauke masa hankali,kafin daga bisani ya fice.Da asubahi kiran sallah ne ya tashe ta,da mi'ka hade da hamma ta mike tana bin dakin da kallo,ya akayi barci ya dauke ta haka ne?
taja tsaki hade da mikewa tsaye,ta rage kayan dake jikinta kawai tana jin haushin rashin zuwan ridwan gareta jiya,wanka kawai tayi dan bata sallah,ta fito daure da towel da saurinta jin ana ta kiran wayarta.Karo sukayi da ridwan da shigowar sa kenan dakin...
Wani irin yaarrr sukaji a gaba daya jikinsu.
Taja baya kadan,shima yadan matsa,da kyar muryarta na rawa tace,ina kwana?
Ya bi ta da kallo,itama sai ta kalli jikinta,ware ido tayi da sauri tajawo mayafinta ta rufa jikinta.Ridwan yace da husky voice dinsa, ki shirya ki fito,ya juya ya fice.
Ta turo baki,sannan ta saka kayanta kawai ta fito.
A falo ta tarar dashi zaune ga warmers nan a ajiye,yace zauna mana,ta samu waje ta zauna,yace ke wacece?Gabanta ya fadi,ta daure tace,matarka mana,ya kalleta,miye manufar ki?mai yasa kika aure ni?
Ta rasa mai zata ce dashi,yace na tabbata ba sona kike yi ba...
Kirjinta ne ya shiga faduwa,ridwan ya daure fuska,you keep appearing in my life why!?did you marry me for my money....!Idonta ya ciko da kwalla,ta mike kawai ta bar falon,da gudu ta shige daki tana kuka,wani irin abune ya tsaya mata a wuya kuka sosai takeyi..
Ridwan ya dafe kansa,why! Just why did she come back!!!!
Mikewa yayi ya fice daga gidan.'Gidan ikram yaje kawai dan nan ne kawai ze samu sukuni,yana shiga yaci karo da Ayla tana wasa a falo,ta tsaya tana kallonsa,baki iya gaisuwa ba?ta matse bakinta,good morning sir,ikram ce ta fito daga kitchen tace ah ah,ya ridwan kaine da sassafe haka?
Yace ai kuwa dai serve me breakfast ols ina mansoor ne?
Ikram tace yana daki kasan shi sleepy head ne ai,Ikram ta kalli Ayla,come on Ayla come here,da gudu taje wajenta,ikram taga ridwan nabin yarinyar da kallo,tace baka tambayi wacece ba,ridwan ya yatsine fuska,tace diyar sarah ce,gabansa ya fadi,Ayla na mutukar kama da Sarah amma ita farace sosai,gaba daya yanayinsa ya canza a take.
Sun zauna suna cin abinci,ridwan nata kallon Ayla sai tsakurar abincin takeyi,ya kalli plate dinsa,shima haka duk tsakurar abincin yake,ikram tayi murmushi kawai.Amal na can hankalinta a tashe,sai safa da marwa takeyi a falo,sai gashi nan ya shigo,ta saki kuka tana rungume shi,ya za'me jikinsa kawai yayi sama abunsa.
Saratu tasha kukanta ta gaji,ta dawo falo ta zauna taci abinci kadan jikinta duk babu dadi,kiran inna ya shigo suka gaisa,ta koma daki tana jin kanta ya fara ciwo,jikinta yayi zafi sosai,a nan ta'ke zazzabi ya rufe ta abun tausayi,taso ta kira ikram amma ta fasa.
Da daddare tana nan zufa ta rufe mata jiki, ji tayi an shigo dakin,da kyar ta bude ido ta hango sa a tsaye,ya zauna a kusa da ita a sanyaye,sai da yayi minti 15 yana nazari kafin daga bisani ya furta sunanta...
SARAH......Please
Vote
And
Comments