Chapter 13

3K 229 8
                                    


'Washe gari da safe Ridwan yayi shirinsa tsaf Dan zuwa jogging.
dama duk Sunday yana zuwa Dan motsa jikinsa sbd yanayin aikinsa na zama waje daya.

Saratu kuwa yunwa ce ke ta cin'ta sosai,Dan kuwa jiya Ridwan kiri'kiri da wainar nan Ya wuce abunsa, Ya barta da cinyar bayanta.

   tana saukowa kasa kenan ta gansu a tsaye da ikram duk sunsha kayansu na tafiya jogging abunsu.
Ikram na ganinta tace, lah yauwa Ashe ma kin tashi dama yanzu muke shirin tafiya jogging ne zakije ko its fun?

  Saratu tadan kallo sashen da ridwan yake tsaye.
yayi kyau sosai cikin black jogging wears dinsa.
tace yunwa nakeji ne wlh ikram.  ikram tace kada ki damu idan muka gama ai sai muje mu saya chicken wrap ko shawarma.
saratu a zuciyarta tace, ji yarda ya wani basar abunsa kamar bai ganta ba se wani amsa wayarsa yakeyi.
tace toh zanje ikram amma bani da kaya fa irin naku.

  Ikram tace kada ki damu ina dasu ai muje na baki nawa ki saka.
sai a sannan ne ridwan ya kashe wayar da yakeyi yana kallonsu har suka shige ciki.

    Ikram ta ba'wa saratu riga da wandonta na jogging kalar dark purple ne sun mutukar yi mata kyau, dan rigar ma da kadan ta wuce duwawunta, duk sai takeji wani iri saboda bata saba saka kaya irin haka b.

a waje suka tarar dashi a tsaye yana gaisawa da ma'aikatan gidan..
   Ikram tace,  poor ya Ridwan har yanzu bai saba da shaking hands ba, saratu a zuciyarta tace, ai da gani zayyi girman kai.. 😏

   Da kallo yabita tunda suk tunkaro shi, ta kara fitowa yarinyar da take tsab, amma tayi kyau sosai, yayi mamakin shape dinta sosai.

yace muje ko,a cikin gidan suka shiga zagayewa suna jogging, shi kuwa Ridwan cikin kwarewa yake ta push ups dinsa, saratu nata kallonsa da gefen ido, ba karamin burgeta namiji mai build body yakeyi ba, tadan tabe baki shi wannn komai ya hada abunsa.

    Sai da suka dauki minti talatin.  saratu kam tuni ta zube a kan grass carpet sai aikin kallonsu kawai takeyi.
   Ikram ce tace dashi, ya ridwan muje ka siya mana chicken wraps please, nasan yanzu ba'a kammala breakfast ba kuma sarah yunwa takeji tun dazu.

  Yakai dubansa kan saratu, tayi lamo kamar mai tunani sai tsinkar grass takeyi, yace okay muje.

   Motarsa suka nufa, saratu dai mamakin dukiyar su takeyi, ikram har zata shiga seat din gaba sai ta tsaya ta juyo tace da saratu, oops shiga nan matar mu..
   Saratu tace ah ah ai duk dayane ko, shiga abunki kawai, ikram ta jayo ta ta saka ciki.

Ridwan ma ya shiga ya ta'da motar..
Kallon saratu yayi, a takaice yace,  saka seat belt, ta juyo suka bada ido ta tsaya  tana kallonsa kawai.
yace saka mana, tace a sanyaye ina ne yake?
Dan ita duk motar da take shiga ba masu seat belt din bane ba, kuma su can kauyensu ma waya wani damu dashi..

  Ridwan ya kusanto ta, da sauri taja baya kadan tana runtse idonta, tunaninta ko dukanta zayyi ya dauki amsar tata rainin wayo.

  Ya tsaya yana kare mata kallo, sannan ya sake matsowa sosai har yana jin saukar lumfashinta.
  Ita kuwa take kirjinta yahau lugude
Ridwan ya jawo seat belt ya saka mata, sannan ya zauna shima, ta bude ido tana kallon gefen fuskarsa.

A wani restaurant suka tsaya, wajen duk motocine na masu kudi manya manya, ya bude ya fita yana cewa ina zuwa.

  Tunda ya fita saratu ke kalllonsa har ya shige ciki.
  Ikram ma tadan fito waje ta tsaya gaban motar da wayarta, saratu zaman shiru ya ishe ta dan haka ta bu'de itama kawai ta fito...

Dai dai lkcn ne wasu samari su biyu suka zo wajensu.
Ikram tace, lah  fadeel da  hussain dama ashe kun shigo kano?munyi magana da faisal yace min se next week zaku dawo ya london?

Rashin Ga'taWhere stories live. Discover now