Chapter 20

2.5K 189 2
                                    

'Juyowa yayi yana cire sunglasses dinsa ya sauke lumsassun idanuwansa akan ta.
   Saratu taja baya da saurin ta.
Yace da husky  voice dinsa, lafiya? Whats the matter lady? Ganin bai shaida ita ba.

Saratu ta sai'ta kanta dan zuciyarta se bugawa take, tace am sorry i mistake you with someone, yace babu damuwa da gani musulmi ne dan Arewa,ya sakar mata murmushi sannan ya juya ya wuce abunsa.

  Minal ce ta karaso wajenta da saurinta, wai lafiyarki kuwa Sarah, tun dazu aka kawo mana abinci amma najiki shiru, gashi lkc ma yana ta tafiya.
Ta juya tana fadin, muje toh sarkin korafi kawai.

Uku da rabi daidai ta shiga TV station din, babban gaske ne dan yafi nasu branch din komai da komai.
Manager suka samu a office dinshi, yayi farin cikin ganinta sosai, ya shiga introducing dinta da ma'aikatan wajen, sannan ya bata script  din tambayoyin da zatayi, aka shiga da ita chnaging room, anan akayi mata make up mai sauki,ta kuma canza kaya zuwa riga da skirt na english wears sun amshe ta sosai, minal tace wow dole na dauke ki nayi updating a status dina cos am statuless yau dinnan.

Saratu ta kai mata dukan wasa, bana son zolaya minal, minal ta dauke ta hoto tana fadin, lah kinga har  3 seen wlh kuma harda YA AMMAR ma, saratu ta hade rai, minal tayi dariya kinga yayi commenting ta shiga nunawa saratu wayar, saratu ta mike, baki da aikin yi wlh hakanan kika biyo ni dan ki matsa min, manager ne ya shigo yayi kiran Saratu ta shiga studio, taja lumfashi sannan ta fice with full confidence dinta.

Kallon babban bakuwar tasu tayi, wata lady ce yar kimanin 27,shes a successful business woman, ta mutukar burge saratu sosai, a nan suka fara airing show din, saratu na wurgo wa babbar bakuwarta questions masu ma'ana ita kuma tana bata amsa a sa'ke cike da barkwanci.

Karfe Biyar daidai suka rufe shirin sallama, DEEMA HAMMAD ta mikawa saratu hannu suka gaisa, tace am a big fan of yours Sarah, saratu taji dadi sosai, tayi mata godiya.

Sun fito da minal dan tafiya gida, motar deema tasha gabansu, ta sauke window tana murmushi, Sarah dear muje na ajiye ku mana, minal ta tabo saratu dake kokarin rejecting, saratu tace toh shikenan mun gode deema.

    A cikin mota tace dasu, yunwa nakeji wlh, why not muje can gidana muci abinci please Sarah, saratu tayi dan jim, sannan tace ba damuwa muje.
    A maitama ne gidan na deema, bai wani  cika girma ba amma ya tsaru kam, ta kaisu falon ta tana fadin, ku zauna bari na fadawa cook abunda zai girka mana, suna zama minal ta bude baki, ke kinga aljannar duniya ko? Saratu tadan yi shiru tana tuna farkon ganin gidan su Ridwan haka ta ganshi kwanin kyau.
   Suna nan zaune sai ga yaron deema dan beauty dashi  ya fito daga wani daki da gudunsa, ya gaida su yana kallon saratu, ta sakar masa murmushi ya mayar mata shima sannan ya haura sama wajen mamansa.

    Deema ta sauko tana basu hkrn ajiyesu da tayi, dinning table suka zauna suka hau cin abinci, jefi jefi suna firar su, suna kammalawa saratu tace zasu tafi dan dare yayi, deema tace toh ngd sosai bari driver ya kai ku ko?ta Kira diver ya dauke su suka tafi,hakanan take jin hankalinta ya kwanta da saratu sosai,shiyasa ma ta amshi har numbar ta.

Washe gari sukayi shirin tafiya studio,minal ta kalli saratu dake daukar jakarta,gsky wannan Deema din shes so kind wlh,saratu tace,she is gsky ba kowa bane mai kudi irin ta suke da kirki,minal tace ni tana burge ni wlh,yau ma da ita zakiyi shirin ne?saratu ta girgiza kai nima ban sani ba but i don't think shes d one.

Karfe biyu suka shigo studio din, manager ya shiga jinjinawa saratu, bayan awa daya ta gama shirinta minal tace kinyi kyau yau fiye dana jiya,saratu ta daure fuska,kin cika zolaya wlh salon kice zaki dauke ni ki daura social media, minal tayi dariya,ai ke bansan daga wane century kike ba wlh,ashe kamar ki ko dan whatsApp din nan bakya yi sai fama da text mssg ,saratu ta murguda baki eh din naji dai,minal tace yauwa this week fa ya AMMAR zai dawo ,saratu tace kai dan Allah cike da farin cikin ta,minal tace haka ya fada min jiya dai,kinsan halin kayanki,saratu tace Allah ya dawo dashi lfy,munyi missing dinsa dayawa wlh.

     Tana zaune cikin studio tana jiran wanda zasuyi shirin tare da ita, mikewa tayi tsaye da sauri ganin fuskar da bazata taba iya mantawa da ita ba..
    Baki bude tace IKRAM?
  Ikram ma cikin mamaki tace SARAH?kece?
Sukayi saurin rungume junan su cike da farin ciki sosai.

    A nan show din ya fara,ikram computer professional ce a yanzu,kuma tana tallafawa yara marayu sosai,saratu ba karamin dadin firar su tayi ba.
   Show din na kammalawa suka sake rungume junan su,ikram tace,kin ganki kuwa Sarah?you look Muah da kyal na ganeki ma wlh,sarah tace ke din fa,kin ganki kuwa?in banda wannan black mark din naki na fuska bazan taba iya gane ki ba,yasu hajiya?
     Ikram tace suna lafiya,taja hannun saratu suka fice.

Minal na ganin su ta mike,dan tasan ikram a instagram sosai,a nan suka gaisa ikram tayi exchanging numbers dasu,sannan tace mijinta ne zai zo daukarta su dan jira su gaisa dashi.

      Suna nan tsaye bakin gate sai ga wata katowar mota tayi parking gabansu,saratu tace hala har surukin nawa ya karaso ne?
  Ikram tayi dariya ai kuwa dai shine,waya ta kira tace,ka fito mana honey,
Ai kuwa ya bude ya fito,mutuwar tsaye saratu tayi ganin wannan mutumin datayi mistaking dinsa da Ridwan jiya.

Shi din ma yadan yi mamakin ganinta,dan fuskar saratu ba irin wacce zaka manta din nan bace farat daya.
   Ya basar kawai ya shiga gaisawa dasu,saratu ma ta basar ganin bai tambayi ikram inda tasan ta ba.
  A nan yace su shiga ya ajiye su mana,ai kuwa har bakin kofa ya ajiyesu suna shirin fita,ikram tace yanzu gobe zaku koma kano kenan?
Saratu tace,eh dama weekend show ne next week wata zata ci gaba,ikram ta kalli mijin nata,mansoor she's a long lost friend of mine i really missed her alot,ko zamuje gida dasu ne?kaga daga can sai su tafi ko?

   Saratu tayi saurin cewa,no haba ikram ai anyi mai wuyar,tunda muka hadu ga kuma number ki bari kawai sai wataran ko?ta kalli minal dake latsa waya,minal tace aikuwa dai.
   Mansoor dake kallon saratu ta mirror yace,haba dai my love is right ku shiga kawai ku dauko kayan ku  mu tafi.
   Saratu ta shiga zamewa amma ikram tace inaa...sai ta tafi dasu.
Da kyal saratu ta yarda suka bisu.

A gidan su suka sauka,ikram ta nuna musu daki sannan tadan fita.
Minal ta tsare saratu da questions ina kika san ta ne?
Saratu da gaba daya hankalinta ke a tashe tace,inna ta taba yi musu aiki,minal ta jinjina kai kawai,saratu kuwa tsoro takeji,sai yanzu take jin bata son sanin komai akan Ridwan,tasan maybe yayi auren sa kamar ikram,wata kila ma harda yaran sa.

Ikram ta shigo bayan sunci abinci tahau yi musu fira,data kawo lbrn baya sai saratu ta Za'me ko tayi shiru,lura da hakan yasa kawai ta share itama,wayar saratu tayi ringing Inna ce tayi kiran,ta amsa suka gaisa harda ma dije.
Minal ta amshe wayar tana cewa,inna ina wuni?
Wai ina my love ne AYLA yar lukuta..
Minal ta saka hands free tana dariya,bari kiji Sarah nasan mutuniyarki sai munsha fada wajenta.
  Ai kuwa da siririyar muryarta tace,salamu'alaikum wanene ke mgn?
  Ikram tayi dariya jin muryar yar yarinya amma da gani zatayi wayo ko ta tambayi minal.
Minal ta hau fira da ita ,saratu kuwa ganin yarda ikram ma ta biye musu sai ta kwashe kayan da sukaci abinci ta fita zuwa kitchen.

Tana fitowa falo ta shiga karewa falon kallo,yayi haduwa ta karshe,can idonta yakai kan wasu pictures dake manne a bango,ta karasa wajen a sanyaye,tana cikin kallonsu duk na bikin ikram ne da gani,idonta ne ya sauka kan fuskar da ta dade tana mararin son gani,tsaye yake a baya da wani yaro a hannunsa,da gani bai ma san an dauko dashi ba,fuskarsa dauke da murmushi mai kara masa kyau.

    Kafafunta ne suka fara rawa,idanuwanta suka ciko da kwalla,dama tasan Ridwan yayi aurensa gashi ma harda yaronsa,wani irin yanayi ta shiga idonta har fara ganin  yaron yana mutukar kama da Ridwan.

    Tana juyowa cikin sauri don tafiya taga mansoor tsaye a bayanta yana kallonta,ta dafe kirjinta dan ya tsorata ta sosai ,yace sorry na tsorata ki ko,ta gyada kai sannan ta wuce yabita da  kallo....
  

Rashin Ga'taOnde histórias criam vida. Descubra agora