Chapter 5

3.2K 243 8
                                        


'Ridwa ya kurawa takardar ido, ammani ta sake kusanto da takadar gabansa meaning ya amsa kenan, sai daya fito da hankicinsa fari tas sannan ya kama takardar ya amma, ya karanta hade da kallonta da sauri a  gyada masa kai tana fadin,ni bana jin turanci kaima kuma baka jin hausa sosai ko? , dan haka ta shiga masa bayanin kurame, zan koyar dakai hausa nima ka koyar dani turanci, kaji?

   Sai daya dauki 5mins sannan ya gyada mata kai, tace yauwa ko kai fa toh maza ci abincin ka ta nuna masa tray din da ta shigo  dashi, ya sakar mata murmushi itama ta mayar masa.

Bayan shekaru 13

'Budurwa ce yar kimanin shekaru sha bakwai 16 da haihuwa, doguwa ce siririya mai kyawun fuska,bakace amma ba can ba zan iya cewa dark chocolate  ce.

     Fuskarta a murtuke jikinta sanye da riga ta atamfa da zanin kodaddiyar shadda ja, kafafunta sanye da sudaddun silifas hannunta rike da wata bakar leda, tunda ta baro gungun jama'ar dake ta kokowa da ta'da kura take bude hanci tana wani kwafa.
    
SARATU! SARATU! Taji sai faman kwala mata kira akeyi, cike da harzuka ta juyo tana kallon mai kiran nata, hafiza tace, wai ke mai yasa ne yar rigima ce ne  ! Saratu ta banka mata wata uwar harara hade dayin kwafa tana yatsine fuska, ke hafiza wallahi ki shiga taitayinki, kinga dai muna yar dadi dake ko! Dan haka kada ki sake  kawo min maganar wadancen azzaluman mutanen, hafiza tace amma baki kyauta ba wlh saratu ace sun baki sadaka amma zaki watsa musu shinkafarsu a jiki, bai dace ba wlh, saratu tace ai kadan ma suka gani indai ni ce, yanzu ace dan muguwar mugunta ta mutane ina fa ji sukayi waya da alhajin dake bamu sadakar amshi tashin yace du a bamu mu'du shida'shida amma kalla ta shiga girgiza ledar dake hannunta, ko tiyya daya basa cika mana, hafiza ta girgiza kai dan tasan ko mai zata fadawa saratu bazayyi tasiri ba.

Bako sallama haka ta fa'do cikin gidan tana kwala wa dije kira, Dije! Dije!

Dije dake zaune akan taburma da salame a gefenta tace gani nan yar dije, saratu tayi wurgi da ledar hannunta a tsakiyarsu tana fadin, wash Allah na,ta zube a kasa tana sakin lumfashi sama sama.

Dije ta kalleta da sauri tana jinjina ledar hatsin da saratu ta shigo da ita, ke yar nan mai nake gani haka ne? Ta shiga duba ledar tana fadin, kodai kinyi sabolanci naki ne akan hanya ledar ta huje wannan sai kace mun roko, saratu ta tsiru baki, babu wani sabolanci dije, wallahi wadan nan mutanen mugayen banza ne, da kunnena fa naji alhajin na fada musu yarda za'a rabawa mutane shinkafar, amma dan zalinci kalla abunda suka bamu.

  Dije ta yatsine fuska, ni ban san mai suka dauke mu ba wallahi, sai kace mabarata ki barni dasu kawai,saratu tace ni ai tuni naci mutuncin su harma fa da gali dan gidan mai unguwa, salame ta rike baki tana kallon idon Allah, ko gaisuwa bata samu daga saratu ba, dan haka tace, su saratu manyan gari..

    Wani irin kallo saratu ta wurgo mata da gefen ido, idan Akwai wanda ta tsana toh wannan salamen ce, tufar da yawo tayi ta mike tana kakkabe zaninta ta shige dakin dake gefensu.

'Washe gari tunda asuba dije ta tashi saratu,  wani irin juyi tayi,  idanunta cike da barci tace, wai ke dije layin fanfon nan fa yanzu ya ra'gu, duk yaran ma ai sun tafi ci ra'ni, dije takai mata duka, ke ni da Allah can tashi ki debo mana ruwa, babu wanda yakai ki asarar sa ai gashi kona alwala  babu bare na shayin safe, saratu fuskar nan a kumbure ta mike tabar dakin tana gunguni, silafas kawai ta zura ta jawo hijabinta dake rataye kan kofa ta fice..

'Tana zuwa ta tarar da abokiyar fadar ta, yatsine fuska tayi ta karasa cikin kasaitar ta, rabi ta harareta ta kalli asiya dake kusa da ita, kinga wannan ballagazar ko?

Caraf a kunnen saratu, ai kuwa ta juyo a fusace ta kalli rabi,dan ubanki ni kike kira da ballagaza, akwai ma wata ballagazar kamar ki?
Rabi na wuci tayo kan saratu cike da fushi ta tsukumo wayanta, nan da nan dambe ya kaure tsakaninsu, jama'a aka taro amma babu wanda yayi kokarin rabasu dan kuwa tsoron iyayensu akeyi a kauyen, masifaffu ne na bala'i gashi kuma suna ga'ba da juna.. 

Dije na zaune gaban murhu ta ta'sa tukunya a gaba,  taji shirun yayi yawa,malam ne ya fito daga ba'yi rike da yar buta yace, wai har yanzu saratun shirun ne?

Dija taja dogon tsaki, yanzu haka tana can tabar min bokitin kan layi, tayi hanyar gabanta, malam ya girgiza kai, ai lamarin saratu sai addu'a bari na fita na di'bo ta.

Can ya hango su duk sunyi cirko cirko da rabi sai zubawa junan su Ashar sukeyi, da saurinsa ya karasa yana kwala mata kira, ke! Saratu! Tayi saurin juyawa tana kallon mahaifin nata, jikinta ne yayi sanyi sannan tsoro ya shige ta, ta dauke bokitinta ta ba'lla da gudu..

Koda ta shigo gidan dije na tsaye a zaure rike da ka'ra a hannunta.
Wani irin ribas tayi zata gudu, dije tayi saurin riko hijabinta tana fadin, ja'irar yarinyar yanzu sabida Allah sai da har rana ta fito karw'kare kika samu halin dawowa ko!

Saratu ta turo baki tana fadin, yo dije yo ba wannan wawiyar rabin bace taja ni fada, dije taja tsaki, ina ce dai baki raga mata ba ko?
Saratu ta kwashe da dariya, ai sai da nayi mata lugu lugu wlh, dije tace  yauwa yar dije shiyasa nake alfahari dake.

Abuja 2017

Ta'ko yake tamkar yana jin tausayin kasar, gaye ne ajin farko! idan nace farko i mean first class most handsome guy kenan,hadadde ne mai daukar hankalin yan mata, fari ne tas dogo, yana sanye cikin designers working  attires dinsa, ba karamin amsar sa sukayi ba duk da yau'ne ranar farko daya taba saka kaya irin wannan, idonsa lullube yake cikin dark brown shades 😎  .

  Tunda ya shigo ma'aikatar kallo ya koma kansa, secretary dinsa na biye dashi a baya yana faman briefing dinsa akan schedules dinsa na ranar, gaba daya heartbeat dinsa ya shiga racing, sauri ya karawa tafiyarsa kafin nan suka shige cikin lifter, direct office dinsa ya shige yana dagawa secretary dinsa hannu meaning ya jira sa a waje.

   Zama yayi da sauri yana rike da kirjinsa, dai dai lkcn text message ya shigo masa a waya, da sauri ya dauka ganin wayarsa ce ta gida bata aiki ba.

   'Life savior' na gani a jikin screen din, ya dauka da hanzari ya bude text din idanunsa kyam akan screen din.
'How is first day at work? Ina fatan komai ya tafi lafiya ko? Pls reply back dan albarka!
Wani irin murmushi naga ya saki cike da murna sannan ya saka kiran no din.

Bu'gu daya aka dauka,am perfect alright mom ya fada cike da shagwaba, a dayan bangaren lumfashi aka saki sannan akace, take your meds ok? Ina jiran dawowarka anjima sannan aka katse kiran.

  Aljihun rigarsa ya laluba, kamar ya sani,sai ga drugs dinsa,  ya saki murmushi shiyasa yake mutukar son mom dinsa, karasawa yayi gaban water dispenser ya dauki class cup ya diba ruwa yasha drugs din, sai sannan yayi wa secretary dinsa alarm ya shigo office din, files kawai ya mika masa yayi signing, da lumsassun idanuwansa ya dago ya kalli secretary dinsa, look haydar cancel all my schedule for today, haydar yace ok sir,  ya mike ya dauki car keys dinsa sannan yabar company din gaba daya.

A wani makeken gida naga an wangaye masa gate ya shige da sabowar motarsa mai kirar honda
    Mom! Am back Mom! Ya shiga kwala kira a makeken falon dayaji kayan mo're rayuwa.

  Ammani na gani ta fito daga kofar rike da glass cup din madara a hannunta, mamaki ne ya lullube ni, ganin yarda ta mutukar canzawa tamkar ba ita ba, sanye take cikin atamfa data tamshe ta sosai, karasowa tayi wajen sa tana murmushi tace Welcome back yallabai...

Please vote
And comments
Share

Rashin Ga'taOù les histoires vivent. Découvrez maintenant