Chapter 7

3.3K 237 0
                                        

'Kada ki wani damu sa'ade, ai wannan hadin yamin kwarai da gaske kema kinsan bana mgn biyu,Auren saratu da Jibrila kamar anyi an gama ne!
    Wani irin faduwa gaban saratu yayi ras!
Jakar dake hannunta ta fada kasa! Dije na jiyo motsi a tsakar gida tayi saurin fitowa tana latsa
e yar wayarta ta tura ta karkashin taburma, kamar an wurgo ta haka ta fito tana kallon saratu  dake tsaye tamkar gun'ki..

   Ke lafiya kika fado min gida babu sallama sai de naji ki kawai!saratu tayi banza da ita, dije tace ikon Allah, kikayi wani tsaye kamar an da'sa ki, saratu ta kalleta idanun nan har sun kankance, dije dawa kike magana yanzun nan?
Dije ta kalleta da sauri, dawa fa nake mgn inace kinsan ni kadai ce a gidan kema?

Saratu tace, wlh ni dije babu wanda zaimin auren dole!
Dije ta watsa mata harara, ke din banza! Ai in gaya miki a cikin dangin mu kaf babu wanda ya bijire wa zabin iyayenmu sai mahaifinki, dan haka wlh wlh kema bazaki watsa min kasa a ido ba ehe!
Saratu ta turo baki, ni karatu fa nake yi, kuma ai an daina wannan auren dolen,  mutum yaje yasha wulakanci a banza!
Dije tace karatun naki na shirme! Kin manta kema ba wata tsiya kike tsinanawa karatun ba!

Saratu ta duka tadau jakar ta, ni bazan iya auren wannan jibrilan ba Allah ya sani, dije takai mata duka tayi saurin shigewa daki da gudunta.

Ridwan ya kalli haydar dake tsaye a gabansa,yanzu Summer outfits suke so kenan? Hydar yace, eh dan nayi mgn da CEO dinsu daga can paris din, ridwan ya gyada kai hade da cewa fixed a meeting for us this weekend, yana kokarin daukar blazer dinsa hydar yace, sir your dad is looking for you in his office, ridwan yayi dan jim kafin nan ya fice.

A zaune ya tarar da daddy dinsa yana amsa waya, ya samu waje ya zauna fuskarsa babu walwala, daddy ya kashe kiran da yake yana kallonshi cike da farin ciki, Allah ya gani he's proud of his son, ba karamin farin ciki yayi ba ganin yarda Ridwan ke overcoming Trauma dinsa.

    How are you feeling son?
Ridwan ya daga girarsa daya, am alright, daddy yace ya aikin fa? Ridwan yace alhamdulillah, sai mgn suke jefi'jefi cikin rashin sabo da juna.

'Karfe hudu na yamma ridwan ya baro company, yana tafe cikin motarsa yana sauraren fav song dinsa har ya iso gida.
   A compound ya hango ikram da wata a tsaye suna daukar selfie, ya fito bayan yayi parking yana tafiyarsa cikin kasaita, ikram ce ta hango sa cike da murna tace, oh ya Ridwan welcome back!

    FADILA dake kusa da ikram ta ware ido tana kallon kyakkyawan da ikram ta kira da Ridwan, wani irin kyawu yayi mata harma yafi kyau a fili akan a pics dinsa da take gani wajen ikram. 
   Ridwan ya tsaya can gefensu yana fadin, wannan gayun haka Ikram sai ina ne?

Ikram tace yau ne birthday party din suhaima can zamuje,Fadila ta matso itama tana fadin, Ya Ridwan ina wuni?
Se lkcn ya kallo inda take, cike da rashin sanin fuskar yace, lfy lau,hakan kuwa ba karamin haushi ya bawa fadila, kusan duk weekends tana zuwa amma har yanzu bai santa.

ikram tace please ya Ridwan ko zaka ajiye mu ne? Wlh bala driver ne mommy ta aike sa har yanzu bai dawo ba, tayi kasa da muryarta, kaga ma fa Maman kaduna kullum se ta tambayeka wlh, tunda kaji sauki pls bro ka kai mu mana, ta karashe mgnr cike da shagwaba.
   Ridwan yace, fine let me freshen up ya juya ya shige ciki abunsa.
Sai daya dauki 30mins sannan ya sauko kasa, yayi shigarsa cikin wando jeans da  polo shirt dinsa yayi mutukar kyau, ammani ya samu a kitchen ya sanar mata zai fita, ta juyo tana fadin, abinci fa, yaace sai na dawo mom, tace kasha meds dinka dai ko? Yace nasha mom ya sakar mata murmushi ya fice.

A wani madaidaicin gida yayi parking, ikram tace zaka iya shiga? Cike da consigned dinta, yadan tabe baki zan iya i think, fadila dai jinsu kawai takeyi, ita ba karamin burgeta Ridwan yake yi ba, gashi dai kamar arabs well tunda ruwa biyu ne ba abun mamaki bane.
   
Saratu ce ta tunkaro gidansu, har sun fara waec dinsu kuma alhmdllh ana taimaka musu sosai, gajiya sosai takeji a jikinta sanadiyyar nisar da makarantar tasu tayi da kauyen na su, mutane ta hango sai fitowa sukeyi, mata ne amma ta kasa shaida suwaye.

Rashin Ga'taOù les histoires vivent. Découvrez maintenant