'Shagwabe fuska yayi yana fadin, haba mom i told you fa ki daina kirana da yallabai din nan, call me RIDWAN pls mom, ammani ta girgiza kai sannan ta mika masa cup din hannunta, amma ka shanye ina da aiki a gabana, ya amsa ya kafa kai ya shanye tas , sannan ya zauna yana cewa, kinsan me mom,i feel better going out today, ammani ta saki murmushi dama ai na fada maka, everything will be alright idan ka cire tspro a ranka, ta dan ja lumfashi kafin tace, yallabai inaso naje gida gobe, cikin sauri yace, its been month already?
Ammani tayi dariya No kawai dai inaso naga mutan gidan ne, yadan yi jim yana tunani, tunda yasan mom dinsa bata taba ambaton family dinta ba, ya lura kuma kamar bata son yana yawan kawo mgnr, tadan dafa shi idan bakajin dadi sai na bari se next week, yadan lumshe idonsa kafin yace ok babu damuwa zaki iya tafiya ya saki murmushi , ya mike ya haura sama.
Saratu ta kalli babanta da sauri, yace wai ke wace irin yarinya ce ne huh? Yanzu ace kin shafe sati kenan bakya zuwa makaranta, dije ta leko dakin, yace yauwa dije ina tunanin ke yakamata kiyi mata fadan rashin zuwanta makarantar nan, tasan yarda innar ta ke kokari dan kawai ta samu ilimin nan amma ina ita babu ruwanta, dije ta yatsine fuska, toh ai ko'ro ta sukayi daga mkrntr ita kuma Ammanin kwana nawa kenan shiru ko kyallin ta bamu gani ba, malam ya rike baki, yanzu dije duk kudin da salame ke kawo miki babu saura?kiji tsoron Allah, Inace dubu talatin ne? Dije ta burmo cikin dakin, dama idonka nakan kudin nan yaya?
Inusa takaici ya ishe sa ya mike ya fice.
Saratu ta mike tana fadin, ni karatun ma ya fita raina wlh, dije tace shine na gani nima, shiyasa naki biyan kudin ai duk barnar banza ce kawai, saratu tayi hamma wai dije ina dumamen nawa ne? Dije tace yana can dakinmu je ki dauko shi.
Da yamma saratu ta shiga gidansu hafiza,a tskar gida ta tarar da inna mahaifiyarsu hafiza na kokarin sauke tukunya, ta gaishe ta kai tsaye tayi dakinsu hafiza, anan ta tarar da hafiza ta duke sai kuka take rusawa, da sauri saratu tace an shiga uku hafiza mai ya faru?
Hafiza ta dago dakai, se da gaban saratu ya fadi ganin yarda idon hafiza yayi jawur, hankalin saratu ya tashi, tace wai mai ya faru dake ne hafiza?
Hafiza ta fashe da kuka, wai aure za'ayi min saratu!
Saratu ta ware fararen idanuwanta, aure!? Cike da tsoro tace lallai kin shiga uku! Yanzu kema auren za'a miki?
Hafiza ta buga uban tagumi, wlh ni bana so saratu! Bana son yin auren nan yanzu, so nake sai na kammala krtn na secondary, saratu ta tausayawa kawarta sosai, tana jinjina kai tace, gaki dama mayyar boko, amma kada ki damu ba yaya hamza bane zaki aura? Ina ce ai kina son shi sosai ko?
Hafiza ta gyada kai, amma wlh ni se da auren nan yazo naji gaba daya ya fitar min a rai, saratu ta dafa ta kada ki damu kinji zan tayaki da addu'a.
Sai yamma likis ta shigo gidan su, tun kafin ta karasa ciki taji kamshin da sai wata wata take jinsa, ta murtuke fuska tana kokarin juyawa ta koma inda ta fito, taji an kira sunanta cike da murna...
Saratu! Ta juyo fuska ba walwala tana kallon mahaifiyarta,haushi sosai taji a zuciyarta, a ganinta mahaifiyarta bata damu da ita ba ko kadan,kamar yarda dije ke fada mata a kullum 'uwarki na can na rainon dan wasu ta barmin ke nan sai wahala nake!
Ammani tayi kokarin riko hannunta amma saratu ta fisge tayi ciki abunta, dije ta tarar da tire gabanta cike da kayan marmari, tasa hannu cikin tiren ta dauki kankana da sauri tana fadin, kai dije ina kika samo kayan marmarin nan haka nasan de bada kudin ki kika siyo ba?
bakin dije cike tace, uwarki ta kawo mana tsaraba, da sauri saratu ta yar da kankanar hannunta, ammani dake kallonsu ta saki lumfashi cike da takaicin relationship dinta da yar tata,ta rasa yarda zatayi tayi mending tsakanin su, tasan kuma dije ce sanadi amma ya ta iya.
Da daddare malam inusa ya dawo ya tarar da matar tasa, ba karamin farin cikin ganinta yayi ba.
Washe gari kuwa tun asuba ammani ta dukufa yiwa saratu wankinta, ko da suka tashi suka tarar da kalacin safensu harta kammala ta kimtsa ko'ina tsaf.
YOU ARE READING
Rashin Ga'ta
General FictionRashin gaa'ta is a hausa written story, follow and vote
