""""""Ammani ta kalli inusa nasan cewa a zuri'ar ku karatun boko kamar kafuranci ne kuka dauke shi amma ka duba ka kani mana yarda hakan ya jawo maka cikin rayuwar wahalar nan da kakeyi, sau nawa abokanka suke zuwa don taimaka maka da aiki amma ace dan bakayi karatun boko ba bazasu iya daukar ka ba, yanzu haka kakeso saratu ta tashi itama?da RASHIN Ga'ta irin wannnan? Nasan ita macece Amma a wannan zamanin ko Matan ma suna neman ci gaba a rayuwarsu ai, dije tadan nisa da tunani, Allah ya gani tana son kudi kamar ranta, yanzu saboda wani al'ada tasu ta banza zata rasa wannan gara basar kudin masu yawa haka? A banza a gofi, ammani ta karasa wajen saratu dake kuka, dije tayi saurin kallonta, babu damuwa zamu saka ta a makarantar badai shikenan ba? Ammani tace eh a takaice, dije ta kalli inusa ka bari kawai ayi yarda take son, cike da murnarta ta fice.
Kwanaki biyu da wannan maganar sai ga salame da malam haru a kofar gidansu dije, a lokacin dije na makota ma ana ta faman zabga karya wai ai suna da dan'uwa ne a burni shine ya samo mata aiki tace bazata iya ba ammani ta fanshe ta, sudai jinta kawai sukeyi Dan har sun saba da karyayyakin ta na kullum.
An daidaita komai ammani ta gama shirin ta tsaf Sai tafiya, tasan zatayi kewar diyarta sosai, ta rungume ta tsam a jikinta tana shafa kanta, kada kiyi barna kinji, saratu ta gyada kai, dije taja tsaki, kike waniyi kamar zaki barta wajen wasu muguyen mutane, nifa kanwar ubanta ce, ta fisgo saratu wajenta, ammani ta mike a sanyaye tabi bayan salame..
Sun shiga garin na kano da yamma likis, direct mansion din alhaji kabir sukayi,suna zuwa aka bude musu katoton gate, ita dai ammani Sai kalle'kalle takeyi kawai, gaba daya rayuwarta bata taba ganin gida mai kyau da girma haka ba, sun shiga makeken falon a nan suna tarar da wata kyakkyawar mata a zaune, hannunta daya rike glass 🍸 cup Tana sipping juice dayan kuwa wayace mai tsadar gaske sai faman amsa kiranta takeyi, su ammani suka samu kasan kapet suka zauna, sun dade suna jiranta ta karasa kafin daga bisani tayi wata yatsina tana kallonsu, ta nuna salame, ya na jiku shiru ne har na kusan canza mai kawo min yar aikin ma, salame akayi kasa da murya, wallahi hajiya abunne sai a hankali kiyi hakuri, ta nuna ammani, ga wata nan na kawo miki ita, babu abunda ba zata iya ba matar dan uwana ce, hajiya ta kalli ammani kayan jikinta sai da suka kusan sanyata amai, tadan tabe baki, tunda dai ridwan zatayi wa aikin ina ruwanta da kyaftarta, ta juyar da ido tunda shi ya jawo wa kansa irin wannan rayuwar ko a ha'bar zaninta.
An nuna wa ammani dakinta da kuma aikinta, hajiya layla ta kallesu,ni zan tafi sai na sake dawowa ta juya cike da kasaita ta fice, mamaki ya dami ammani ance ankawo ta aiki amma gashi dai babu kowa ma a gidan, gashi dai gida kamar aljannar duniya amma bata ga alamar wani dan adam ba bayansu biyu ba a cikinsa.
Suna zaune tare da abokiyar aikinta wata yar kasar gwarawa mai suna lami, sai dai kawai sukaji kamar anyi barin kwanoniya, a tsorace suka mike, lami tace, ina tunanin ranshi ya dade ya tashi ba, ammani cike da mamaki tace waye shi? Kyauta tace shine mai gidan nan ba, ammani tace a cikin zuciyarta dama akwai mutum a cikin gidan kenan bayan su? .
Sun karasa kitchen kyauta na gaba ammani na biye da ita, a lokacin karfe sha daya ne na dare, a tsaye suka tarar dashi ya juya musu baya ga duk dangaren da glass glass na plate a kasa sun fashe.
Lami tayi saurin zuwa ta dauko plate sannan ta karasa ta zuba kalar abinci sunfi goma duk ta tsara su waje daya, ta dauko cup da ruwa da juice din lemo ta ajiye a gabansa, bai ko tanka ba ya duka ya dauka sannan ya juyo...
Sai da gaban ammani ya fadi, wannan bil'adama ne haka!? Kyawunsa tamkar dan larabawa, fari tas dashi ga fuskarsa sai dai kawai kace mashaAllahu,amma kallo daya zakayi masa kasan cewa yana tattare da Rashin Gata ga alamar damuwa,da takaici bai ko kallesu ba ya fice abunsa cikin takon sa na isa, ammani ta kalli lami cike da mamakin ganin yallabai yaro haka, shine mai gidan nan? Ta fada cike da tsananin mamaki, lami tace shine fa, ammani al'ajabi ya ishe ta.Washe gari tayi aikinta kamar yarta lami ta koyar da ita, duk inda ta shiga a gidan sai gabanta ya fadi, lallai kuwa wasu a aljannar duniya suke, tunawa da irin nasu muhallin girgiza kai kawai takeyi, tana kammalawa ta gangaro kitchen inda ta tarar da lami ta rikice girke girke kala'kala, ta zuba ido tana kallon ikon Allah, gaba daya abincin da lami tayi bata ma san irin su ba inba shikafar da taga anyi ta da nama ba jollof, lami ta kalleta tana dariya, yadai ammani ya kina kallon abincin haka? Ammani tace toh ai gani nayi sai kace za'ai wani biki ko baki za'ayi ne? dudu mu uku ne fa ko?
Lami tace hakane, tana kakorin wanke hannu kinsan shi ranshi ya dade din bana sanin mai yake so ne, tunda baya daukowa sai yana jin yunwa , ammani tace basai kiyi tambayarsa ?Lami tayi murmushi sannan ta dauki warmers dinta kawai ta fice.
Karfe 2 na rana suna sashen su sai ji kawai sukayi ana ta ba'ri, da sauri lami ta mike tayi waje tana fadin, wayyo Allahna na manta na ajiyewa ranshi ya dade abincinsa a bakin kofar dakin sa, ammani tabi bayanta, suna zuwa suka iske gaba dayan abincin dake kan dinning din ya ture su kasa, wasu kwanukan duk sun fashe, lami ta runtse ido a tsorace, ammani ta kalli hannusa da yayi ja jini na diga, da saurin ta ta karasa gabansa tana riko hannunsa, subhanallahi jini...
Lami ta ware ido, ridwan a take jikinsa ya hau rawa lumfashinsa ya fara tsinkewa, ture ammani yayi da karfinsa ta fada kan wasu fasassun plastic bowls , wani irin kara ta saki na azaba lami tayi saurin riko ta, ridwan cikin saurinsa ya bar wajen da dugunsa.
Kwana biyu ammani nata fama da jinya, gashi yaune take sa ran zuwa gida tunda juma'a tayi, lami ta kalla a gefe tana gyaran kayanta, ni kuwa lami wai maike damuwar ranshi ya dade ne? Ya akayi yake zama a wannan makeken gidan shi daya? Ina iyayensa su alhaji da hajiya?
Lami taja lumfashi, bazaki ji shi ba a bakina ba ammani, idan lokacin jinki yayi duk zaki fahimci komai dangane da al'marin gidan nan, ammani taja lumfashi toh shikenan amma ina tunanin bazan iya tafiya yau dinnan ba ni, lami ta juyo da sauri, bazaki iya ba? Ta fada da tashin hankali kinga fa yarda yayi miki toh balle ace kuma ku kadai ne a gidan, ammani ta dan nisa kafin tace a zuciyarta, wai meke damun wannan yaron ne?
Please
Vote
And
Comments
Follow me on instagram @ dee_bature
