01

4.2K 185 4
                                    

*RA'AYI*
'''Na Safiyya''' (Mrsjmoon)

'''Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah mai kowa mai komi,ina rok'onsa da sunanayensa tsarkaka da ya yi min jagora abisa adukkan lamurana da dukkanin lamuran al'umman manzon tsira Abul fatimatul zahra'u. Allahumma salli wassalim ala saiyiduna muhammmadun wasaalim.( sallallahu alaihi wassallam)'''

*01*

Shiri takeyi cikin rashin kuzari,sam batajin dad'in *Ra'ayin* data d'orawa kanta, rana tsaka na yawon zuwa club,alhalin ita kotaje bata rawa balle  zuk'an abin maye, hasalima ko ruwan wurin tana k'yan k'yamin shansa amma dai duk da haka duk yanmaci idan bata ziyarci club ba batajin dad'i, sai dai in bata gari,nan kam sumul takejinta har tayi tajin kamar kar takoma Abuja.

"Mitcheww!!" Taja tsaki mai sauti "meye Matsalata ne ni ZAHRA?, Allah kakawomin d'auki alfarmar Annabin farko da karshe."

Ta fito cikin takunta na takama wanda ya zame mata d'abi'a tun fil'azal,abinda mutane da dama suka kasa ganowa har suke mata duban Girman kai da gadarar nuna ita d'in d'iyar masu tarin arziki ce shiyasa take hakan,, nan ko abinda basu saniba shine Zarah mai saukin haline da tausayin na k'asa da ita, inkaji  harshenta kuwa to da 'yar uwarta Zulfa'a ce wanda suka zamo kamar  masu ganin hanjin nuna, takama da nuna mulki wannan ajininta suke tun kuwa tana 'yar mitsitsiyarta.

"Sai ina haka k'anwata?"

"Aunty zanje duba mamin Hafsat ce jiya tacemin anyi admitting dinta zazzabi ke damunta"

"Ohk adawo lafiya,ace ina gasishe da ita."

"Tam zataji."

"Am Adon 'yan mata."

" na'am Aunty "

"amma tare da su Zubaida yakuje ko?"

"No aunty bama su san zanfitaba kuma dan Allah ko sun zo nemana kice kin aikeni gidan Aunty Muneerat."

"Zarah! Zonan ki sanar dani gaskiyar inda zaki."

Cikin sauri ta fice tana dariya,tana jin Zainab na kwalla mata kiranta amma sai ta kwasa da gudu ta fice ta kofar baya ta fad'a motarta ta fice daga street din.

Wurine wanda yacika ya batse da 'yan mata tare da samari,wasu suna rawa rungume da nuna,wasu shaye -shayen sukeyi wasu kuma zaune suke suna hira irin ta soyayya.

Wuri ta samu mara yawan hayaniya ta zauna tana bin kowa da idanu, fuskanta babu alamar walwala,k'asan ranta kamar wuta, iya tunaninta ta rasa gano dalilin da yasa takejin son zuwa club alhalin bata samo komi cikinsa sai takaici.

Gyara zama tayi tana la'antar wasu masoya dasuka baje suna ta aikata masha'a a gaban bainar jama'a basako jin kunya.

Lumshe idanunta tayi tana jin wani yarrr, tsigan jikinta yana tashi, istigfari tasoma ja da hailalah cikin ranta atake taji ta dawo natsuwanta, ta mik'e da sauri sai kuma ta sunkuya tana tattara phone, pose tare key d'inta.

Tana shirin d'agowa taji saukan hannu a mazaunanta ko kafin ta ankara saijin anmata wani k'yak'yawan runguma tare da sunsunata mata wuya.

Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, tasoma ambata cikin ranta,cikin gaggawa ta janye cikinta ta fuskanci wanda ya yi mata wannan aika aikan, dogone bak'i mai kyan sura amma dakagansa kaga tantirin dan duniya.

Fasssss!! Ta sauke masa mari ta kuma d'aura masa wani wanda sai da ya kusa kaiwa k'asa wasu samari suka tareshi.

"Look at you, foolish, irresponsible, naive, good  for nothing like you har ya isa yasa dirty hand d'insa ya yi touching my body?, to wannan shine first and last dazaka kara taba jiki mai daraja irin nawa arayuwarka."

Ta tofa masa yawu a fuska ta bar wurin cikin takama.

Ihu ta shewa ya kaure wurin dama tun sanda sound din marin ya fito, wurin yayi tsit kowa yakoma kallon ikon Allah.

Tsawa ya daka masu duk sukayi tsit.

"Ni Jimie sai na wulak'anta rayuwar yarinyar can ko ta halin k'ak'a,ni ni ni!! Ta mara ta zageni ta tofamin slaver, wallahi ko zan rasa raina saina d'au fansa ta kowani fanni, saina koya mata hankali I swear."

"Jimie! Jimie!! Jimie!!! Haka suka soma fada cikin ihu da sowa suna kuma tafi.

"Keep quiet my friend.! " yace cikin tsawa, sai kuma yafice fuwww gan dinsa suka mara masa baya.

A fusace take latsa horn a bakin gate din wani katon gida ko ince Estate wanda aka yi rubutu da manyan bak'a asamar sa kamar haka *MODIBBO'S FAMILY*

Gate man ne ya bude mata, ta shige da gudu, ko gyara parking bata samu tayi da kyau ba ta fito a fusace ta nufi part din Hajja, daf dazata shiga tacikaro da Zulfa'a.

"Ke dawaye haka madam?

"Da uwarki"

"Kan butsi, umman kika zaga baki ko ji kunya ba?"

"Zanci miki mutunci Zulfa wallahi inbaki fita hanyata ba tam."

Tajuya zata wuce ,dan jan fada irin na Zulfa'a sai ta fizgota, aiko tana juyowa ta wanke ta da slaps masu kyau with anger voice ta nunata da yatsa "wallahi summabillahil azim zan'iya karkaryaki in watsar Indai baki fita life d'ita ba."

Tana juyawa taji saukan duka ta ko ina, ko kafin ta farga har ta kaita k'asa tabi ta danne taci gaba da dukanta.

Zubaida tare da Zeenat ce suka iso wurin a sukwane suka samu suka rabasu, Zulfa'a sai fizgewa takeyi ita abarta ta koyawa Zarah hankali, ita  kam Zarah bak'in ciki yahata cewa komi ganin yarda tayi mata da jiki hatta da wayarta glass din ya fashe, cije labbanta tayi ta juya zuwa part din Zainab tana ayyana abinda zata yima Zulfa'a ta huce.

Sisters wai wannan wani irin abune haka? A ce kungirma har kun kammala university amma wai baku daina rigima ba? Abin takaici wai danbe abinda ko sanda kuna yara ba kuyisaba, an dai sanku da cacan baki amma dan Allah yanzu da nonuwanku da komi wai kun zage dantse kuna danbe kai wallahi this is a scandal  to you oooo."

"Uhmmm sis Zeenat ai nikam na rasa ma abinda zance ne, illah in muku fatan shirya dai, dan abin naku yasoma wuce tunanina, kuna abu kamar wasu 'yan Matan k'auye, Haba dan Allah kukuwa, kuyi ta hakuri da nuna mana, dan hakurin shine jigon dukkanin rayuwa, Al'umman dabata da hakuri bata taba cigaba Sam.

" Tabbas kuwa sis Zuby."

"Uhmmm Sisters wallahi sai naji mata ciwo, kudubafa kuga abinda tayimin dan na mareta mi yasa bazata rama marin taba amma shine zatayimin irin wannan wulak'anci haka hmm Allah mai rabani da ita sai Allah."

"Ina jiranki 'yar club kawai, wayasanima k'ila k'waya kika sha kikazo zaki saukemin haukanku na 'yan nanaye."

Bata rufe baki ba taji saukan naushi ta dama da hagu, Zarah ce ta bata sadakansu.

Ihun azaba ta saki, tayo kan Zarah, su Zubaida suka riketa gam, dai-dai lokacin kuma Ahmad da Muhammad suka shigo parlorn.

Tsak Zulfa'a ta tsaya tare  da sunkuyar da kanta tana kokarin goge jinin da bakinta keyi, ita kam Zarah toilet tashige da gudu dan tasan zuwan natane dubi ya wani mugun kallo da Ahmad yake jifanta da shi.

"Ku samemu a falonmu dukkanku har da ta cikin toilet."
Suka juya suka fice.

"Oga yarinyar 'yar babban Gida ce kuma gidansu sun tara manyan masu mik'amai dan suna da soldier,lawyer,doctor harma da inspector haka kuma iyayayenta  manyan yan kasuwa ne,  grandfather din su kuwa dattijon kirkine mai tai makon na k'asa da shi,dan haka fad'anka da ita bamai nasara bane dubi da yarda ta kereka ta ko ina, kar dai kamanta bamu da komi tun k'ahonmu da gadaranmu grabs money, shi ne arkikinmu dan haka ka fita hanyarta kawai shi yafi."

Tass! Ya d'aukeshi da mari, "Ni jamil ka ke gayawa wad'annan nonsense talks din? To bara kaji kaine matsiyaci amma ni kam mai arziki ne, you don't know who is my father and you don't know my background, so today you will know who am I. Just wait I'm coming.

Kokafin ya fito tuni ya fice a sukwane dan yasan bingiga zai d'auko ba mamaki ma ya harbeshi ya mutu abanza dan shidai yasan babansa Kalla mai faskare ne,har yanzu kuma yasan baibar sana'arsa tasa ta faskaren itace ba, amma dan rainin sense zai wani yimasa burgan banza da wofi.

~Mrs j moon~

RA'AYIWhere stories live. Discover now