Ra'ayi.
Mrsjmoon.
*34*
A bakin shiga parlor ya dakata ya saita kanta, nutsuwarsa ta daidaita sannan ya shiga ciki d'auke da sallama.
Mommy tare da Umma Amarya ne zaune a cikin parlor suka amsa mishi, ya russuna ya gaishe dasu suka amsa tare da yi masa barka, bai amsaba sai d'an sosai hancinsa da yayi cike da kunya.
"Suna ciki, k'arasa ka gansu." Momy tace dashi.
"To Mommy." Ya amsa tare da mik'ewa ya na mai dosar room d'in ta nuna masa.
Kwance ya hangota su Zeenat suna zazzaune agefenta sai hira suke zubawa kamar ba ita ta haihunba.
K'arasowa yayi tare da sallama, suna ganinsa duk suka ja gefe, suka amsa mishi sallamar tare da gaisar dashi.
Cike da fara'a yayi ta amsa musu.
Hannunsa ya d'ora samar forehead nata ya gangaro zuwa wuyarta, yana maijin ya temperature nata yake.
Ita dai da eyes take binsa face nata cike da annuri.
Hannunsa ya sanya cikin nata ya rintse gam tare da sauke ajiyar zuciya, ya sunkuya daf da kunninta yace "Masha Allah, Alhamdulillah, yabo da dukkan godiya suntabba ga Allah mai komi da kowa da yanufemu da samun k'aruwa, Allah yaraya mana yayi ma rayuwarsu albarka."
"Amin." Ta amsa idanunta lumshe.
Light kiss ya mannawa fatar eyes nata, tayi saurin bud'esu, a tare suka sakarwa juna murmushi mai d'auke da tsantsan farin ciki.
"Ya kikejin jikin naki yanzu?"
"Normal."
"That's good dear."
Zama yayi gefenta ya na d'an latsa cikinta "Anya sweetheart tummy nan babu sauran bayani kuwa?"
Da hanzari ta ture hannunsa tana hararansa "Dan bakai za kayo kashin ba ko?"
Dariya su Zubaida sa, shima dariyan yasoma, ta tura baki ya sunkuyo kamar zai mata kiss tayi saurin yunk'urawa ta zauna tana yamutsa fauska.
"Sorry Sweetheart."
"Yawwa Yaya, baka d'auki yaranba." Ta fad'a cikin shagwaba.
"Oh am sorry dear, kece kika d'aukemin hankali."
D'aya bayan d'aya ya amsa yaran daga hannun Zulfa'a yayi masu addu'a.
Ya ajiyesu samar cinyarta ya tsira masu idanu, hatta yatsunsu irin nasa ne duk da suna kama da juna shi da Zarah amma yaran komi nasane, murmushi ya saki mai sauti, yana kallon cikin idanunta, yayi k'asa da voice ya furta "Alamu ya nuna nafiki hazak'a ta ko ina Sweetie."
"A kan me ba." Itama ta furta cikin rad'a.
"Babies man sun kwashe komi nawa, ko kara basuyi mikiba dan sun san ked'in raguwace ta gaske." Ya k'arasa zancen cikin kashe mata 1 eye.
Kau da fuska tayi gefe cike da kunyar zancensa, ya jiyo da ita ya kai bakinsa samar hancinta ya ciza da k'arfi.
"Ah!!!!." Ta furta tare da kai mishi dukan wasa a k'irji.
Dariya yasa su Zulfa'a na tayashi.
"Jimin shashancin banza dai wurin Ahmadu." Cewar Hajja,shigowarta kenan ta taddasu suna dariya.
"Hajja case, to me yayan yayi daga shigowarki zaki soma k'orafi?"
"Gidanku nace Zeenatu, fitsararriyan banza, bazanyi magana ba alhalin idanuna sun ganemin shashancin da yakeyiwa yarinya ko gama manta zafin haihuwar batayi ba zai soma ta kurata da shirmen banza wai da sunar love, to wallahi ahir d'inka na kuma ganin hannunka samar jikinta, ka daiji bayanina da kyau ko?"
YOU ARE READING
RA'AYI
Romance"Mitchew!!" taja tsaki "Meke damuna ne ni ZARAH?' Ya Allah ka kawomin dauki alfarmar Annabin farko da k'arshe Amin.
