*RA'AYI*
'''Na Safiyya.'''*14*
"Son sanar dani had'inka da yaran can da har suna nemi kashemin kai."
"Dad a club muka had'u, kuma cutarmin da Zarah suke sonyi." Yayi shiru kamar mai tunano abinda zai kuma fad'a.
"Uhmm ina saurarenka kuma me tayi masu da har suka d'auki aniyar cutar da ita?"
"Nima bansani ba amma dai sun had'a kai dani akan na yaudarota ta soni sai na kawo masu ita na amince da hakan batare da tunanin komi ba, to ina zuwa gareta naji sonta da k'aunarta sun kamani, kamu mai mugun wuya dan kullum in ban gantaba ko jin muryanta bana iya barcin sukuni, to danaga na fad'a tarkon sonta haka sai nace masu nafasa abinda suka sakani, shine sukayi tamin barazana nima inayi masu irin nawa, kuma Allah Dad bantab'a kawowa zasu iya harbina ba sabida ko da wasa bantab'a ganinsu da mugun makami ba."
"Ya Salam!! Son wani irin rayuwa kajefa kanka ban sani ba?"
"Am sorry dad, natuba bazan sake aikata makamancin haka ba."
"Uhmm to Allah ya amsa, amma inason sanin masha'ar da kake aikatawa batare da sani na ba."
"Dad bana neman mata haka bana homo, amma ina kora barasa kuma abinda yake kaini club kenan shansa har muka had'u dasu suka d'orani a wancan hanyar kuma wallahi dad tunda na had'u da Zarah natsani shan giya tare da mugun halinsu mika, bansan wani irin so nake mataba wanda ya canza ni lokaci d'aya na daina duk wani abu mara kyau, inaga watakil dan ina zaton zamuyi aure ne banson tazo ta sameni a cikin rayuwa mara kyau."
Numfashi Dad nasa yaja "Lallai nagodewa tarayyan nan naka da wannan d'iyar albarka, Allah yabiyata da alkhairi."
"Amin Dad."
"Ina fatan Allah yasa kabari kenan har abada."
"Insha Allahu Dad bazan koma ruwa ba, katayani da addu'a."
"Kada kadamu ina cinkin sa ne, Allah ya lamunce mana"
"Amin, godiya nake Dad, Allah barmana kai."
Murmushi Dad d'in yayi yana shafa sumar kansa cike da k'auna yace "Yanzu ina yake maka ciwo?"
"Babu."
"Masha Allah, mungodewa Allah, Allah ya kuma k'are tsare gaba."
"Amin, thank you my lovely Dad."
Shafo fuskansa yayi cike da kulawa "Anjima da yamma zaka tafi wurin Mum d'inka dan nariga da nagama dukkanin shirye - shiryen, zakabi jirgin 6:00pm, hope it will make u happy?"
Cikin matuk'ar murna yayi hugging Dad d'in "Yes! Dad, I love u so much, Allah yak'ara girma." Ya manna masa kiss a cheek.
"Amin, but inarok'onka dan Allah kada ka koma ruwa tunda katuba to tazamo mai tsantsani daga sake komawa sab'on Allah, sabida uwarka ba mai kula bace kome kayi baza ta tsawatar ba saima dai tace 'yancinka ne kayi abinda kakeso kuma kaga dama bamai takuraka, shi yasa banson zuwarka wurinta."
"Insha Allahu Dad bazan tab'a komawa ba, kuma mum ta canza yanzu tana tsawatarwa tunda lil sis ta kusa mutuwa garin sakacinta."
"Good Allah yayi maka albarka tare da 'yar uwar taka."
"Amin ya Allah."
"Son bazan k'yale wad'an da suka nemi illatamin kai ba, in Allah yaso kafin kadawo annemomin inda suke nasa a hukunta su."
No Dad leave them, na barsu da Allah kuma ina addu'ar Allah ya tsaremin my Zarah daga fad'awa tarkonsu."
"Amin, amma lallai sai nasa anhukuntaminsu duk in nayi idanu biyu dasu."
YOU ARE READING
RA'AYI
Romance"Mitchew!!" taja tsaki "Meke damuna ne ni ZARAH?' Ya Allah ka kawomin dauki alfarmar Annabin farko da k'arshe Amin.